101&110

1.4K 49 4
                                    

👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
         *GIMBIYA HAKIMA*
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻

*🌎MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️

     *M. W. A*

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻'''
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
________________________________

  _STORY AND WRITING_ _BY_

    _Jameelah jameey 🖋_

    *(Yar mutan kankia👸🏻)* 

  


*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*

_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._

'''NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR
BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍'''

*ALHMDULILLAH ALLAH NAGODE MAKA DA KABANI LAFIYA HAR NA KAMMALA WANNAN LABARI MAI TAKEN GIMBIYA HAKIMA*

*TO JAMA'A ANCE LAIFIN DADI ƘAREWA TO GASHI TA KASANCE DAMU, YAU NA KAWO MAKU KARSHEN GIMBIYA HAKIMA, WANDA NA ƁATA MA RAI TA SANADIN WANANN LABARIN DAN ALLAH YA YAFEMAN NIMA NA YA FE MAKU 😁*

*NAGA MASOYA SOSAI KUMA INA YI MAKU GODIYA DA WANDA NA SANI DA MA WANDA BAN SANI BA DUK INA GODIYA ALLAH YA BAR KAUNA DAN INAYIN DADIN KASANCEWARKU DANI INA GODIYA SOSAI😁*

*LOKACINE, TABBAS KOMAI LOKACINE GASHI LOKACIN YAYI MUN GAMA GIMBIYA HAKIMA SAI KU TARENI A SABON BOOKS ƊIN NA WANDA ZASU ZO INSHA ALLAH NGD😁*

101&110🔚

Ruɗewa sosai Gimbiya Zulaha tayi, waya ta ɗauko ta kira Hakim ta gaya mashi Gimbiya haihuwa ta zo, Hakim kiran Aliyu yayi suka zo suka ɗauketa sai asibiti, domin ganin anceto rayuwarta ita da abunda ke cikin cikinta.

Bayan sun kai ta asibitin, shidai Hakim kasa tsaye yayi ya kasa zaune dan yana cikin tashin hankali balle da yaga sun kusa aya babu labarin komai tashi yayi kawai yayi alwallah ya shiga massalacin da ke asibitin ya sallah yana rokan Allah ya tada ƙafadun matarshi lafiya, cikin ikon Allah Hakim yana cikin sallah sai ga Hamad yazo yana sanar dashi haihuwar Hakima, duk farincikin da yake cikin sai da ya gama sallah ya ƙara godema Allah sannnan ya tashi ya bi bayan Hamad suna zuwa suka shiga direct wajen Hakima ya wuce bai tsaya tambayar abunda aka haifa ba shidai so yake yaga Jewel ɗinshi wani hali take ciki, yana zuwa ya kama hannunta yana mata sannu, kallonshi tayi sai tayi murmurshi kawai dan har lokacin bata ida jin ta dai dai ba, tsugun nawa yayi yai mata kiss a goshi sannan yace, "Allah yayi maki albarka Jewel, Allah ya saka maki da mafificin alkhari, Allah nagode maka da ka sauki matata lafiya, tabbas yau ranace ta farinciki a gareni Jewel da ba abunda ya samaiki ina godiya ga Allah(SWT)."

Kallonshi take wani sonshi ke fisgarta tabbas tayi dacen miji da kowace mace take da burin samu a duniya, duk wani qualities da ake so namiji yake to Hakim ɗinta yake har ya wuce wajen, riƙe hannunshi tayi tace, "Mijina abun sona ina alfahari dakai Angle, inasonka ina kaunarka, fatana Allah ya raya mana abun da muka haifa."..... Sai da tace haka ya tuna ashe ma baiga mai aka haifa ba cewa yayi, "Jewel fatan dai mace kika haifamana mai kama dake ko."?... Kallonshi tayi tana mamakin tambayar shi sannan tace, "kana nufin bakaga kyautar da Allah ya bamu ba."?

Shafa fuskarta yayi sannan yace, "hankalina baya jikina, yana wajenki lafiyarki itace lafiyata, kece rayuwata idan na rasaki bansan ina zan sa kaina ba Jewel, na safa'a na wutosu parlour na wuto nan domin naga lafiyarki,amman yanzun zan tafi na gano su."

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Jul 22, 2020 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

GIMBIYA HAKIMAWhere stories live. Discover now