43&44

590 53 5
                                    

👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
         *GIMBIYA HAKIMA*
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻

*🌎MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️

     *M. W. A*

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻'''
________________________________

  _STORY AND WRITING_ _BY_

    _Jameelah jameey 🖋_

   *(Yar mutan kankia👸🏻)*

*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*

_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._

'''NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR
BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍'''

43&44

Tafiya take tana tunanin wannan halin na Hakima, bata san yanda zatayi taga ta koyama Hakima Son Hakim ba..

Dan itadai tana san Hakima ta aure Hakim amman gashi su duka basu da maƙiya kamar junansu, haka dai Maryam ta kama wanann tunanin har ta isa gidan su Hakim..

Bayan tayi parking ta fito nan suka hadu da Aliyu shima shigowarshi kenan gidan wajen aiki yaje..

"Aaaa! Maryam kice a gidan namu."?

"Yaya Aliyu ina wuni? "Lafiya lau Maryam daman kamar kinsan inasan ganinki."

"Sai kuma gani Yaya Aliyu ina jinka."

"Aiko naji dadin ganinki Maryam, ko zamu zagaya lambu muyi maganar dan tanada tsawo gaskiya ba laifi."

"Alright then, let go Yaya Aliyu bakomai,"ok Maryam,  thank you sister."

Haka Maryam da Aliyu suka dauki hanyar Lambu, Maryam tana mamakin wata kalar magana Aliyu zaiyi mata haka wanda bata yuyuwa a bakin mota har sai anje Lambu...

"Have a sit Maryam, "ok thank Yaya Aliyu."

Bayan Maryam ta zauna nan shima Aliyu ya zauna ya fara magana kamar haka..

"Maryam nasan kina mamakin maganar da zanyi dake ko."?

"Gaskiya hakane Yaya Aliyu ina mamaki sosai dan haka bata taɓe kasancewa ba shiyasa nake jin tsoro."

"Ok kwantar da hankalinki Maryam, ba wata magana bace bayan ta ƙawarki Hakima."

"Hakima kuma Yaya Aliyu."? 

"Yes of course Maryam ,Hakima, inasan Hakima ta auri Hakim amman abun yafi ƙarfina na kasa shawo kan Hakim shine na biyo ta wajenki ko zaki shawo mana kan Hakima."?

Sai da Maryam ta numfasa sanann tace, "Yaya Aliyu abunda ke zuciyata shike cikin zuciyarka, amman am late tooo."

"Bangane kin makara ba Maryam wani abu? Dan kinsani a duhu."

"Eh wani abu Yaya Aliyu, saboda da wani abun shiyasa nace am late, nafi kowa farincikin su zama masoya kuma ma'aurata amman su sun tsani junansu."

"Tabbas Maryam sun tsani junansu amman kuma akwai soyayyar junasu cikin idanunsu, kawai dai kiyayar tayi tasari a kansu shiyasa suka kasa gane soyayyar dake tsakaninsu tunin daɗewa."

"As how? Yaya Aliyu taya haka zata kasance kace suna son junansu bayan kasan basu da wanda suka tsana kamar Junansu."

"Eh hakane Maryam amman suna son junansu sosai, dan haka kema kinsan yanda zakiyi fitting wajen ganin sun mallaki junansu ta hanyar aure, nima zanyi iyakar yina."

GIMBIYA HAKIMAWhere stories live. Discover now