22&23 babbar magana kudai ku ci gaba da biyoni my fans

541 18 0
                                    

👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
         *GIMBIYA HAKIMA*
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻

*🌎MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️

     *M. W. A*

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻'''
________________________________

  _STORY AND WRITING_ _BY_

    _Jameelah jameey 🖋_

   *(Yar mutan kankia👸🏻)*

*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*

_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._

'''NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR
BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍'''

*ALHMDULH AM BACK, NAGODE SOSAI DA SOSAI MASOYANA NAGA ADDU'OI DA KUKAYI MAN ALHMDULH JIKI YAYI SAUKI SOSAI, DAN MU CIGABA DA GASHI SUYA SAI RANAR SALLAH💃🏼💃🏼🥰*

23&24

"Ranka yadaɗ'e Gimbiya Zulaha ta kawo maka ziyara, "ziyara yanzun cikin daren nan? "Eh tana bakin kofa ma tana jiran ayi mata iso, "je kice mata ta shigo"...

"Allah ya taimakeki Gimbiya Zulaha, Yarima Hakim yace ki shigo''..

Nan Gimbiya Zulaha ta shigo, Lanto na biye da butun shayi a bayanta..

"Allah ya kara maki lafiya yau kice da kanki wajen ɗa'nki? "Ba dole ba Hakim nayi kusan sati uku ban saka a idona ba, ko gaisuwarma mu bar cin arzikinta"..

"Ba haka bane Gimbiya, aiki ne yayi man yawa, kin san zaman banza ba aikin yi bane sai sakaran namiji shine zai kwanta yace komai sai dai ayi mashi, dan yana ɗan wani she kiga basu komai sai bin matan banza da sheye sheye"...

Gimbiya Zulaha taji haushin maganar da Hakim ya gaya mata, dan tasan da Hamad  Hakim yake, magana ce ya gaya mata a takaice, Amman sai ta nuna bata gane da ita yake ba, ita dai burin ta yasha tea, dan yana sha ya gama aiki..

"Aiko dai Hakim ai kasan babu maraya sai raigo, Allah dai yayi maku albarka baki dayanku kai da kannanka''..

"Amin Gimbiya"...

"Da man Hakim jina nayi ance baka ji dadi ba kwana biyu shiyasa nace bari dai nima nazo duba lafiyar sarki mai jiran gado"..

"Godiya nike Gimbiya, Amman ni lafiya ta lau gaskiya, Wanda suka gaya maki basu fadi maki dai-dai ba"..

"Tabbas, dan gashi na gani da idona, ga shayi nan nayi maka da hannuna dan nasan kana san shayi sosai"..

"Nagode, nan Hakim ya ansa shayi ya aje gefe, ya cigaba da marking din papers dinshi, Gimbiya Zulaha na san tace mashi ya zuba yasha Amman bataga fuskar haka ba sai da tayi ta maza sannan tace..

"Hakim ai ya kamata kasha ka jike makoshinka, da man naga duk ka gaji da alamu"..

"Zansha Gimbiya amman sai zan kwanta bacci, dan bani shan wani Abu in ina aiki''..

"To shikenan na barka lafiya Hakim, "toh Gimbiya nagode sosai sai da safe"..

Haka Gimbiya Zulaha ta fito wajen Hakim ranta bace dan ya bata mata aiki, tunda boka cewa yayi ya sha gabanta sannan maganin zaiyi aiki..

GIMBIYA HAKIMAWhere stories live. Discover now