51&52

556 52 7
                                    

👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
         *GIMBIYA HAKIMA*
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻

*🌎MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️

     *M. W. A*

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻'''
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
________________________________

  _STORY AND WRITING_ _BY_

    _Jameelah jameey 🖋_

    *(Yar mutan kankia👸🏻)* 

  

*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*

_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._

'''NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR
BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍'''


51&52




Washe gari bayan Gimbiya ta tashi daga bacci shiryawa tayi sannan ta fito yin breakfast..

Tafiya take kamar bata san taka kasa dan yau zata kaima bayin masarautar ziyara sannan ta wuce shashen wazari zata gano shi da jiki dan baiji daɗin jikinshi ba kwana biyu..

"Allah ya taimaki Gimbiya Hakima takawarki Lafiya yar'sarki jikar sarki gaba dai gaba dai Uwar Marayun kano baki ɗayanta."

"Lantana maza kije ki kiranta shugaban gidan horo inasan ganinshi yanzun kafin mu tafi ziyarar nan."

"Angama Uwargijiyata, muna neman sausaucin Uwar Marayu, na barki Lafiya."

"Bilkisu yi maza ki ɗauko kan wayata wanda nike waya da ita dan naga alamu baku fito da ita ba ko ni kuka bari na ɗauko maku wayar."?

"Allah ya ja da tsawancin kwana ina neman afuwar Gimbiya Hakima Uwar Marayu wallahi safa'a nayi nasa duka na ɗauko su."

"Ya isa haka Bilkisu ba abunda zanyi maki tashi kije ki ɗauko karki ɓatamana lokaci da wannna shurutun naki, kudai baki ɗayanku kun cika shurutun masifa wallahi haba."

Nan Bilkisu ta tashi ta ɗauko waya tana godema Allah da Gimbiya Hakima tace batayi mata komai dan ba ƙaramin tashi hankalinta yayi ba, dan taji ta aika a kira mata shugaban gidan horo baki ɗaya bama sarkin Bulala ba..

"Allah ya taimakeka, Gimbiya Hakima tace tana san ganinka yanzun -yanzun nan inma da hali mu taho tare ƙafata ƙafarka."

"Lantana Allah yasa ba wani abu kuka yi mata ba."?

"Ba abunda mukayi kawai dai tana san ganinka , amman ba abunda akayi mata."

"To shikenan, mu tafi daman bansan naji ance wata baiwa tayi laifi a shashen Gimbiya Hakima dan bansan naga a na hukunta mata dama maza lafiya lau."

"Aiko dai Allah ya ƙara mana hakurin zama da ita, "Amin ya Allah Lantana."

Nan suka tare da Lantana su tautaunawa yanda lokaci guda Gimbiya Hakima ta chanza halinta baki ɗaya bayan sun isa Lantana tayi mashi iso wajen Gimbiya Hakima sannan suka shigo tare..

"Allah ya taimakeki Allah ya ƙarama Gimbiya Hakima tsawon rai, gani na ansa kiranki cikin gaugawa ina jiran umirninki."

"Mudi kana jina."?

"Eh Uwar Marayu ina sauraranki."

"Duk wanda yake cikin gidan horo a sallameshi ya koma bakin aikinshi, na yafema kowa koda bani yayi ma laifi ba balle nasan duk wanda yake cikin gidan nace sillar Shigarshi ciki."

"Godiya suke Uwar Marayu yanzun nan zai zartar da umirninki, na barki Lafiya."

Nan Mudi ya tafi fiddo bayin dake kulle gidan horo, ita kuma Gimbiya Hakima ta tafi ziyara gidan bayi ba ƙaramin kyauta tayi ma bayi ba daga nan ta wuce gidan waziri ta duba jikinshi sannan ta wuto shashen ta..

Masauratar kano a ranar ba ƙaramin murna sukayi ba dan har sai da bayi suka haɗama Gimbiya Hakima walima gobe za'ayi ta..

"Uwar Marayu gobe insha Allah baki ɗaya bayin gidan nan suna gaiyatarki walima bakin ruwa, zamu nuna maki godiya da jindaɗin abunda kikayi a jiya."

"Bilkisu Allah ya kaimu goben, yanzun bacci zanyi sannan kuma ku fara shiryawa jibi zamu koma makaranta."

Washe gari bayan Gimbiya Hakima ta gama shiryawa direct shashen Gimbiya Yakumbo ta wuce kafin dare yayi taje walimar da bayi suka shirya mata..

"Momy kin tashi lafiya."?

"Lafiya lau Hakima ya koƙari?, "Alhmdulillah Momy, Momy gobe zan koma school fa."

"Ai ya dace a koma tunda ankusa gamawa insha Allah."

"Aiko dai Momy sauran Shekara ɗaya insha Allah, "Allah ya kaimu Hakima, "Amin Momy Yaya Annas shima da mukayi yawa yace next year ɗin nan zai dawo ya gama shima baki ɗaya."

"Eh kinga tare zaku gama keda shi, "Aa Momy shi harda masters yayi fa nikuma degree kinga ai da banbanci sosai."

"To Allah ya baku Nasara baki ɗayanku, "Amin ya Allah ni barki lafiya Momy zan biya na gaise da Fulani."

"To Daugter Allah yayi maki al'barka, "Amin Momy."

Bayan ta wuce shashen Gimbiya Fulani suka gaisa sosai, "Fulani zanyi missing ɗinki gobe ne zan koma school."

"Nima zanyi missing ɗinki Hakima, dan Allah ki kula da mutuncin kanki kiyi abunda ya kaiki wannan gari."

"Insha Allah zan kiyaya, "idan mu iyayenki bamu ganinki to Allahn da ya halliceki yana kallonki kuma duniya duk abunda ka suka shi zaka girba dan haka kiji tsoran Allah sannan ki guji abunda zai ɓatama iyayenki rai har ya sasu hawaye."

"Insha Allah Fulani, bayan Fulani ta gama yi ma Hakima wa'azi sanann ta fito ta wuce shashen ta, shiryawa tayu sannan suka wuce walima.

Ba ƙaramin dadi Gimbiya Hakima tayi dan bayi sunyi koƙari sosai wajen ganin sun faranta ma Gimbiya Hakima rai, kuma Alhmdulillah suma sunji dadi dan a fuskar kawai zasu gane Gimbiya Hakima taji dadin abunda suka yi mata dan sai murmurshi take, bayan anci ansha sanann kowa ya tafi makwancinshi..

Wanka kawai Gimbiya Hakima tayi sannan ta kwanta bacci, washe gari karfe biyun rana suka ɗauki hanyar Zaria..

*Oooooooo🥺wallahi nagaji sosai typing is no essay guy kuyi manage da wanannna pls inayinku ovver and over💃🏼❤️🖤💯*

*ANJIMA ZANYI MAKU WANI UPDATE INSHA ALLAH*

_By Jameelah Jameey✍🏻_

*Share*
*COMMENT*
*Vote*
*Like*
*Please*

GIMBIYA HAKIMAWhere stories live. Discover now