77&78

581 51 0
                                    

👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
         *GIMBIYA HAKIMA*
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻

*🌎MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️

     *M. W. A*

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻'''
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
________________________________

  _STORY AND WRITING_ _BY_

    _Jameelah jameey 🖋_

    *(Yar mutan kankia👸🏻)* 

  


*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*

_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._

'''NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR
BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍'''

77&78

Tun daga farkon masarautar Zaria ake yin busa anayi ma Hakima lalai da zuwa masarauta mai albarka, itadai Hakima kanta yana cikin alkarba bata ganinsu sai dai jinsu, shashenta aka kaita da addu'oi ta shigo gidan masarautar haka ma da addu'oi ta shiga shashenta da addu'oi ta shiga room din da aka saka ta, bayan tayi addu'oi ta zauna bisa gadon da yake mallakinta, ita dai Hakima abun mamaki yake ba wai yau itace a gidan miji, mijinma ba wani bane face Hakim makiyinta.

Bayan sun huta aka kawo masu abincin saukar Amarya sannan fa aka shiryama Gimbiya Hakima dan zataje gaida mutanan gida, kwaliya akayi mata mai kyau sannan aka fito da ita shima Hakim ya shirya ya fito tuni ita suke jira dan haka su kuma al'adarsu take idan aka kawo amarya zata je gaida iyaye ita da ango bisa doki, Hakim da kanshi ya ɗauketa ya ɗaura ta bisa doki sannan shima ya hau, direct shashen Gimbiya Zulaha suka dosa daga ita sai shi sai dogarawa masu lura da dokin da suke sama, suna isa ya sauko ya sauko da ita da, sanan yaje saitin kunnanta yace mata sai ta kula sosai kuma komai Gimbiya Zulaha zata ce mata karta ce mata komai iyaka kawai ta gaisheta sai da Hakima taji tsoro dan batasan lokacin da tayi addu'oi ba, hakan da tayi ya burge Hakim sosai riƙe mata hannu yayi sannan yace "kwantar da hankalinki ba abunda zai faru, kedai kawai kiyi abunda nace maki."

Ɗaga mashi kai kawai tayi sanna suka shiga cikin parlourn daman ayi ma iso tuni, sallama sukayi baki ɗayansu tunda suka shigo Hamad yake kallon hannun Hakim da ya riƙe Hakima dashi ji yake kamar ya tashi yaje ya sare ma Hakim kai dan wani bakin kishine ya turniƙe shi zuciyarshi tafasa kawai yake daga zaune, duk abunda yake Hakim yana sane dashi dan yasan yana son Hakima da kunnanshi yaje na gayama Gimbiya Zulaha, bayan sun samu waje sun zauna nan Hakim ya fara gaida Gimbiya, "Gimbiya ina wuni mun samaiku lafiya."?

Kallon sama da ƙasa tayi mashi sannan tace, "da ban wuni ba da kangan ni, ko kuma da ba lafiya ai da asibiti zaka samaini kwance a gadon asibi ɗ'anso."

Hanjin cikin Hakima suka fara kaɗawa daga zuwanta har ta fara ganin masifa, hannunta Hakim ya riƙe gam dan ya lura Hakima ta kusa zundumawa da gudu daga zaunan dasuke.

"Ina wuni."

Hakima tace cikin ɗari-ɗari dan ta tsorata da lamarin gidan su Hakim amman ta ɗaukarma kanta bata shiga harkar kowa zata dage da neman tsarin Allah kamar yanda kowa ke cemata.

"Lafiya, amarya bata laifi ko kin kashe dan masu gida, ai kin bude mana fuskar mu gani ko."?

Hakim da kanshi ya bude ma Gimbiya Zulaha fuskar Hakima ta gani, ba Gimbiya Zulaha ba harda Hamad dake kwance yana kallonsu sai da ya zauna yana kallon sahibarshi Hakima dan wata wutar sonta ke ƙara ruruwa cikin ƙahon zuciyarshi, shi dai Hakim dariya yake a zuciyarshi dan bakin ciki ƙarara yake gani kwance a bisa fuskar Gimbiya Zulaha, itama Hakima duk da kanta na duge sai da ta ɗago kanta ta kallesu dan ji tayi shirun yayi yawa, dakal Gimbiya Zulaha ta bude baki tace, "ba laifi, ashe tsohon naka ya iya zaɓi."?

"Uhmmm, gashi nan dai kin gani, Abba ya zaɓin ma son kowa son wanda ya rasa.", yace yana miƙewa tsaye zasu tafi, zinari da lu'unlu'un ta ba Gimbiya Hakima na barka da zuwa masarautar zaria tayi godiya suka fito suka wuce shashen Gimbiya Kilishi.

Tunda su Hakim suka fita Gimbiya Zulaha ta fara magana tana cewa, "Hamad banga laifinka ba dan kace kana son Hakima ba, ashe haka take da kyau."?

"Hmmm, Gimbiya kiyi wani abu tun kafin ni nayi da kaina dan wallahi ina iya sace Hakima mu bar ƙasar baki ɗaya muje muyi soyayyarmu baki sake ganina har abada."

"Rufaman asiri Hamad saura shekara ɗaya Hakim ya mutu Hakima ta zama taka halak malak karka damu."

"To shikenan, nidai ina nan ina jiran lokacin yayi."

_🙄Kai su Hamad sai kace ku ke da lokacin🤔, naga alama kuna mantawa da Allah fa😰_

______________

Bayan sun iso shashen Gimbiya Kilishi aka yi masu iso suka shiga, Humad yana zaune yana kallo kusa da Kilishi ya tashi ya gaidasu Hakim yayi mashi Allah yasa alkhari sannan ya tashi yace ma Kilishi shi ya barta lafiya zaima tafi massallaci, bayan Humad ya tafi, Gimbiya Kilishi ta tashi ta rungumi Hakima tana yi mata lale da zuwa  masarautar kano, hakan yayi ma Hakima dadi Hakim ya lura da haka yana mamakin yanda Kilishi ta iya duniyanci kala-kala sai kace wata tsohuwar karuwa.

Bayan sun zauna suka gaisheta ta taya su murna sosai sannan itama taba Gimbiya Hakima zinari da lu'ulu'u kamar yanda Gimbiya Zulaha ta basu sanna suka fito suna fitowa suka wuce shashen maimartaba shima sun gaidashi ya ba Hakima kyauta, sanann suka wuce shashen Gimbiya Fulano Kubrah Hakima taga gata wajen Fulani Kubrah dan har abun ya fara bata kunya ma, sosai Fulani Kubrah taja Hakima jiki dan kafin su koma shashen su sai da shekuwa ta shiga tsakaninsu kuma ta ƙara gaya mata yanda masarautar take dakuma waye Hakim, Hakima taji dadi sosai sai dare sanan suka koma shashen su bayan kyautukan da Gimbiya Fulani Kubrah ta cika ta dasu, koda suka koma shashen su abun mamaki bata kowa ba dan duk wanda suka rakota sun koma gida an barta ita ɗaya kamar maiya, suna shiga parlourn ta fisge hannunta daga rikon da Hakim yayi mata ta samu kujera ta zauna ta fara aikin kuka dan taji haushi da suka tafi suka barta, su Lantana ma bata gansu ba sun tafi shashen bayi, Hakim bai nuna ya damu da kukan da take ba duk da kukan yana jinshi har cikin zuciyarshi amman sai ya shigewarshi bedroom ɗinshi ya faɗa wanka, da Hakima taga kukan yana ma sanata ciwon kai ita ma ta tashiga ta shiga wanka a bedroom ɗinta, bayan ta fito daga wanka ita dai tasan room ɗin ita ɗaya ke dashi tunda taga Hakim ba shi ya shiga ba kuma kofar a kulleta take wannan dalilin yasa tana fitowa daga wankan ta saɓile towel ɗin baki ɗaya daga jikinta ta tsaya babu komai a jikinta sai da ta goge jikinta sosai sanann ta wuto wajen mirror domin shiryawa tayi bacci,  dump light taje ta kunna sannan ta zauna bisa dreesing mirror ta fara shafa mai, ɗaga kanta da zata yi taga mutun tsaya bisa bayanta yana zara ido kamar mai tsorata tayi tayi wata uwar ƙara ta duge ƙasa tana ƙare ƙirjinta da hannuwanta, tana kuka, tsaki Hakim yayi sanann yace "idan kin gama kukan isakancin naki ga abinci nan sai kice, mai zangani da kike boyewa mtsss."ya wucewarshi yana balbalin bala'i.

*Niko nace da ba abunda zaka kalla mai zaisa ka tsaya kallonta tun fitowarta wanka malam Hakim😛*

Tunda ta duke take kuka, bata tashi ba sai ta taji ta fita sannan ta tashi ta fara cewa, "Allah ya isa ban yafe ba, kawai ka kalli banza kawai."

Haka Hakima ta kama guguni tana shiryawa har ta samu ta gama abunda take saboda da fushin da tayi ko abincin ma bata ci ba kawai addu'a tayi ta kunna suratul baƙara ta kwanta baccinta.

Tunda Hakim ya samu ya baro ɗakin Hakim direct room ɗinshi ya dawo duk da wanka da yayi amman sai yaji yana da bukatar sake wani sabon wanka bayan ya fito daga wanka sallahr nafila yayi sannan yayi addu'a shima ya kwanta, tunda ya kwanta bai samu bacci ba dan daya kulle ido sai ya ga Hakima tana tuɓe towel ɗin da ta fito wanka tun yana ɗaukar abun wasa har yazo da ya girmi tunaninshi da wata kalllar shi'awace ta adabi Hakim ya rasa ya zaiyi da rayuwarshi dan tunda yake bai taɓa jin kallar wannan station ɗin ba sai yau, bai da damar kulle idonshi sai yaga Hakima tana yi mashi gizo ba kaya a jikinta da yaga abun ba sauki ya tashi ya nufi ɗakin Hakima cikin bukatuwar kasancewa da ita dan yayi ma kanshi alkwarin zan sar hakinshi ko ta wani hali ne.


_By Jameelah Jameey✍🏻_

#Share
#Comment
#Like
#Vote
#Please

GIMBIYA HAKIMAWhere stories live. Discover now