5&6 HISTORY

983 62 0
                                    

👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
         *GIMBIYA HAKIMA*
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻

*🌎MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️

     *M. W. A*

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻'''
________________________________

  _STORY AND WRITING_ _BY_
    _Jameelah jameey 🖋_



*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*

_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._

'''NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR
BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍'''



05&06

Wacece Gimbiya Hakima!!

Masarautar kano, Babbar masarautace wanda tana daya daga cikin masarautar da take babba a Nigeria..

Sarki Abdulsamad  Abdulrazak shine mahaifin Sarki Abdulhadi Abdulsamad, sarki Abdulhadi Abdulsamad shine mahaifin Gimbiya Hakima Abdulhadi Abdulsamad...

Sarki Abdulhadi Abdulsamad adalin sarkine, yana mulki cikin Ilimi da adalci baya san yaga tallakawanshi cikin hukubar yunwa ko wani abu na wahalar rayuwa..

Wannan kyaukywan hali  na sarki Abdulhadi Abdulsamad ya gajeshine a wajen mahaifin shi Sarki Abdulsamad Abdulrazak..

Mahaifin Abdulhadi su biyu ya haifa shida da kaninshi Yarima Annas,  sun taso cikin kulawa ta sarauta, mahaifinsu ya koya masu yanda ake mulkin adalci ya tusa masu soyayyar tallakawa a cikin zuciyoyinsu..

Sunan Mahaifarsu Hakimatu, gimbiya Hakimatu ta ba yaranta da Allah ya bata guda biyu tarbiya iyakar bakin kokarinta, ta koya masu gwamawarar rayuwa ta bada gudun muwa wajen gani soyayya ta shiga tsakanin su da tallakawa domin ita macece mai tausayin na kasa da ita..

Abdulhadi yayi karatun addini dana boko, shida kanin shi Annas..

Annas yana final year yayi accident ya rasu, haka su Sarki Abdulhadi suka yi kukan rashin dan uwa da sukayi suka barma Allah lamarinshi..

Mahaifiyarsu diyar sarkin katsina ce Gimbiya Hakimatu tana da faranfaran da mutane, ta zauna da sirikarta lafiya har mai rabawa tazo ta raba su..

Bayan Abdulhadi ya gama karatu ya auro yar'sarkin suleja Gimbiya Yakumbo, Gimbiya Yakumbo Allah ya albarkace su da d'a daya Yarima Annas daga shi Allah bai sake ba Gimbiya Yakumbo haihuwa ba..

Bayan Sarki Abdulsamad yayi murabus ya maida mulki a hannun Yarima Abdulhadi da shekara hudu, sarki Abdulhadi ya auri yar'sarkin Adamawa Gimbiya Aisha ana kiranta da Gimbiya Fulani...

Gimbiya Fulani ita ta haifi  Gimbiya Hakima Abdulhadi Abdulsamad..

Gimbiya Hakima ta taso cikin gata da kulawa a wajen Yakumbo, dan Gimbiya Hakima bata san Fulani ce mahaifiyarta ba sai da ta girma sanann ta san ita ce mahaifiyarta.

Fulani da Gimbiya Hakima ba wani shiri suke yi sosai ba, duk da mahaifiyarta ce, amman Fulani tace mundun bata chanza halinta ba, to basu taba zama inuwa daya. 

Gimbiya Hakima ta tashi da wani kallar hali wanda ya girgiza iyayenta, domin Gimbiya Hakima bata san tallakawa ko kadan, tun tana yarinya indan su Inna Lantana suka dauke ta, to suna ajiyeta sai anyi mata wanka inba haka ba bata iya bacci a ranar..

GIMBIYA HAKIMAWhere stories live. Discover now