95&96

722 51 1
                                    

👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
         *GIMBIYA HAKIMA*
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻

*🌎MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️

     *M. W. A*

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻'''
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
________________________________

  _STORY AND WRITING_ _BY_

    _Jameelah jameey 🖋_

    *(Yar mutan kankia👸🏻)* 

  

*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*

_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._

'''NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR
BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍'''

95&96

Tana zaune tana lazimi gama raka'atul fijir inta kenan tana lazimi Hakim ya shigo, zauna nawa yayi suka shafa tare sannan yace tunda ta tashi shi zai tafi sallah, bayan ta gama sallahr asuba wanka tayi ta shirya cikin wata atamfa yellow mai ratsin green sannan ta fito kichent ta shiga ta fara haɗa masu breakfast na gani ba faɗa, dan zagewa tayi tana tsara masu break mai kyau da dadi, su kuma su Azima daman su ke gyara shashen su uku haka suka fito suna aikinsu, Hakim ya gama azkar ɗin shi sanann ya taho sheshen shi gaisawa yayi dasu Azima dan yana ganin girmansu, balle ma da yake ganin kaunar Jewel ɗin shi a kwayar idanunwansu shiyasa yake basu girma dan duk mai san Hakima yace shi yake so, kuma duk wanda bai san Hakima tabbas bai sonshi shima tunda Hakima itace rayuwarshi, bayan sun gama gaisawa ya shiga cikin parlour kamshin girkin Hakima ya doki hancin Hakim, lunshe idanun shi yayi yana godiya ga Allah da ya bashi Hakima dan yasan ba wayaun shi bane ya bashi ko dibararshi Hakima kyautace Allah ya bashi, kuma ya ansa hannu biyu yana yi mashi godiya.

Ji tayi an ɗagata sama ana juyi da ita,dariya ta fara yi mashi tana cewa, "please Angle ka sauke ni pls mana."...... Ta ƙarasa maganar tana tusa hannunta cikin laulausar sumar kanshi da taji kudi wajen gyara, bai sauke ta ba sai da ya gaji dan kanshi sannan yace, "Good morng Rayuwata, yana yi mata wani hots romatic kiss, "itama cewa tayi, "Morg too bugun numfashi na.".... Dariya sukayi su dukansu yana jan hancinshi cewa yayi, "Jewel mai like dafa mana har haka ya cika gida da kamshi haka."

"Gasarsaiyar gurasa sai kosai, "wow Jewel bari na taya ki ko."? .... "Aa ai na gama Angel ka gani ma."?.... "Eh nagani Jewel sannu da aiki.".... "Yauwa yanzun dai kaje ka shirya sai ku fito kai da Amarya muyi breakfast."..... "To shikenan yanda kakece haka za'ayi uwar gida sarautar mata."

Haka suka fito tare  shi ya shiga room ɗin shi itama ta shiga nata  wanka ta shiga, tunda Hakim ya shigo room ya tarda Hikimatu tana bacci lokaci ya duba yaga 10am, amman ga dukan alamu bata tashi tayi sallah ba balle ta shirya, ranshi ɓace ya tadda, "wai shin bazaki tashi kiyi wanka kiyi sallah ba? Tun ɗazun nike tadaki harna fito wanka amman baki tashi ba? To kinga tafiya dan Jewel nacen tana jiranmu mu fito cin abinci bansan bata mata lokaci."

Wani irin kallo tayi mashi, wai duk abunda Hakim yayi mata amman da maganganun da zai saka mata dasu kenan "wallahi dole na  fidda Hakima a zuciyar Hakim."... Ta faɗa cikin fushi tashi tayi ta haɗa ruwa tayi wanka tana fitowa tayi sallah sannan ta shirya ta fito, zaune ta iskesu bisa dining sun ajiran isowarta, tana zuwa ta samu waje ta zauna sai cin magani take, Hakima tace mata, "ina kwana Amaryarmu fatan kin tashi lafiya."?.... Wani kallo tayi mata sannan tace, "lafiya."?

GIMBIYA HAKIMAWhere stories live. Discover now