Turkashi!!! Nan fa akeyinta sisters ki garzayo domin ki ji abunda ke cikin..

830 59 0
                                    

👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
*GIMBIYA HAKIMA*
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻

*🌎MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️

*M. W. A*

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻'''
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
________________________________

_STORY AND WRITING_ _BY_

_Jameelah jameey 🖋_

*(Yar mutan kankia👸🏻)*




*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*

_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._

'''NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR
BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍'''

09&10

Nan Gimbiya Hakima ta shirya ta dauki hanyar shashen Maimartaba ita da kuyanganta...

Bayan sun iso Jakkaddiya tayi mata iso har gaban sarki..

"Ranka yadade Allah ya ja da tsawancin kwana, na barku lafiya, "Uhmmm, abunda yayi mata kenan Jakkaddiya ta kama gabanta, ta koma bakin aikinta..

"Baffah ina kwana, "lafiya Lau Mamana,"Baffah da man nazo ne akan maganar makaranta, "to inajinki Mamana, mai kike so ayi maki?"..

"Da man ina neman Sausaci wajen Sarki mai adalci akan hukuncin da ya yanke man na yin karatu nan kasar Nigeria"..

"Kin gama Hakima, sai da gaban Gimbiya Hakima ya tashi da taji yau Maimartaba ya kira sunanta ba tare da yace Mamana ba..

"Eh Baffah na gama!"..

"To daga yau karna sake jin kin zoman da maganar baki san karatu nan kasar, ya zamai maki dole kiyi karatu a kasar Zaria, can nike bukatar kiyi karatu, ko kuma na maidoki nan Kano kiyi karatun"..

"Allah ya huci zuciyarka, Amman, "ya isa haka Hakima kinsan bani magana biyu, dan haka ki shirya nan da kwana biyu zaki wuce makaranta dan na gaji da zamanki gidan masarautarnan kina shiga hakin bayin Allah"..

"Godiya nike Baffah, Amman ina neman alfarma ta biyu, "Uhmmm ina jinki, "da man nace ayi man adalci, adalin sarki, kar a barni na zauna hostel""..

"Da man ba hostel zaki zauna ba, na sa ankama maki gida, dan ba zaki zauna gidan Sarkin Zaria ba, ki zunda man mutunci kina wulakanta masu bayi""...

"Dan haka ina mai maimaita maki Hakima nan da kwana biyu zaki tafi makaranta, kije kiyi karatu nasan tarbiyar da muka baki, tashi ki tafi Allah yayi maki albarka"..

"Amin, godiya nike Baffah, ni na wuce"..

Haka Gimbiya Hakima ta fito turakar Maimartaba ranta bace tana mamakin yanda Fulani da Maimartaba basu ansar uzurinta a rayuwa su dai sunfi san bayin gidan nan akanta...

Tana cikin tafiya wata baiwa daga shashen bayi tafito bata bata lura da Gimbiya Hakima ba ta shafen mata gefen alkelba..

Tas! Tas!! Tas!!! "Ke wata kalar kidahuma ce da zaki taho kamar wani doki kike san bankadeni?"..

"Inalillahi! Ranki yadade kiman rai, wallahi banga tahowarku ba uwar marayu"..

"Ke Azima, "Naam Allah ya taimakike, "maza kije ki kira man Sarkin bulala, "ke kuma in samaiki bakin shashena, "to Allah ya taimaki Gimbiya Hakima"..

GIMBIYA HAKIMAWhere stories live. Discover now