0&04 ADEQUATE

840 29 4
                                    

👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
         *GIMBIYA HAKIMA*
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻

*🌎MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️

     *M. W. A*

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻'''
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
________________________________

  _STORY AND WRITING_ _BY_
    _Jameelah jameey 🖋_



*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*

_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._

'''NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR
BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍'''



03&04


Tunda Asuba su Bilkisu suke tsaye jiran Gimbiya Hakima, hankalinsu duk a tashe yake baki dayan su suna tsoron hukuncin da zata zartar a kansu..

"Wai Ba'ba Bilkisu mai mukayi ma Gimbiya Hakima?"..

"Wallahi A'bu nima bansan mai mukayi ma Gimbiya Hakima ba, amman karki so kiga yanda jiya ranta ya baci, ko nima nan dakal nasha dan harda mari sai da na sha cikin daren nan''..

"Yanzun Ba'ba Bilkisu ke din Gimbiya Hakima ta mara?"..

"Yo sau nawa ankayi Murja ai sai dai kar'asake indai marine munsha shi wurin Gimbiya Hakima nida Lantana yunzun kinga Lantana tana gidan hukunci dan ma Allah yaso ta yau za'a fiddo ta, da sati biyu ta yanke mata"..

"Wai dan Allah maiyasa Gimbiya Hakima bata biyo halin iyayenta ba?  baki daya Gimbiya Hakima bata da tausayi balle imani, da tana da tausayi da bata mari kamar su Ba'ba Bilkisu ba"..

"Hakane gaskiya Ladi, shiyasa na godema Allah da nike wajen dahuwa kawai, shiyasa kullun nike kiyaye wulakancin Gimbiya Hakima, domin bata gani girman kowa cikin masarautar nan"..

"Aiko Larai, kinga yanzun har karfe goma na safiya yayi amman har yanzun bata yi lokacin mu, itada tace tun shiddan safe take san ganinmu, amman shiru kuke jinta"..

"To ya zamuyi Ba'ba Bilkisu, ai hakuri zamuyi tunda haka Allah ya kaddari rayuwarmu, "aiko dai ai hakuri ya zama dole Larai..

Su Ba'ba Bilkisu suna can tsaye tun asuba, amman Gimbiya ta gyalesu kuma sarai ta san da tsayuwarsu a bakin shashenta saboda tun takwas din safe take ido biyu tanata chatting dinta sai da goma tayi sannan ta shiga wanka, bayan ta fito wanka ta shirya cikin wata purple din doguwar riga sannan ta fito tana tafiya cikin isa da mulki irin na sarauta..

"Sai yanzun kuka gadamar zuwa kenan?".

"Muna neman afuwar Gimbiya, uwar Marayu, tun dazun muke nan muna jiran isowarki"..

"To maiyasa bakuje kuka yi man magana ba?".. 

"Allah ya huci zuciyarki, ai bamu da ikon zuwa turakarki batare da wani dalili ba, kuma ai kina bacci shiyasa"..

"Matsalarku ce wannan, kuna jina?"..

"Eh muna ji uwargijiyarmu, muna jiran umirni daga gareki"..

Mtssss"wai ku wasu kallar jahilai ne dabobi wanda basu da gwakwalwa basu da lisafi da basu san inda yake yi masu ciwo ba? "...

"Allah ya huci zuciyarki, suka fada kansu a duge suna tsugune a kasa suna sauraren cin fuska da wulakancin da Gimbiya Hakima take yi masu..

GIMBIYA HAKIMAWhere stories live. Discover now