71&72

579 45 0
                                    

👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
         *GIMBIYA HAKIMA*
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻

*🌎MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️

     *M. W. A*

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻'''
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
________________________________

  _STORY AND WRITING_ _BY_

    _Jameelah jameey 🖋_

    *(Yar mutan kankia👸🏻)* 

  


*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*

_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._

'''NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR
BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍'''



71&72

Tunda Hakima ta tafi shashen Gimbiya Yakumbo nan suka zauna suka fara magana.

"Daughter kinga Hakim ko."?

"Eh naganshi Momy kuma yayi Allah dai ya albarkaci Aurenmu."

"Amin ya Allah, daman nasan kuna ganin juna zaka amince da juna saboda ba ƙaramin dacewa kukayi da juna ba."

"Gaskiya ne Momy, yana da hankali ga dukan alamu dan jiya kawai muka fara ganin juna amman naga hankali a taitare da shi."

*{kunji Hakima da wata sharaton wai jiya suka fara ganin juna 🤣🤣}*

"Ai haka yake kuma gado yayi waje biyu daga uban har uwar, nidai Daughter dan Allah karki bamu kunya ku zauna lafiya keda wannan baiwan Allahn, Allah yayi maku albarka."

"Amin Momy, insha Allah ba zan baku kunya ba, "haka nike san ji ai ga wannan ya kawo da kudi dubu ɗari biyar."

"Wooow! Momy gaskiya nagode, amman ban ansar kudin nan sunyi man yawa ina da kudi sosai."

"Kinga a haka akayi ma kowace mace indai gidan sarauta ta fito sai uwar miji ta bada tukuncinta na fara zuwa neman aure kuma kw zakiyi amfani da komai da aka kawo wanan ne zaki nuna kin gode."

"To Momy nagode, na zan wuce na fara jin bacci, "to Daughter Allah ya kaimu, "Amin ya Allah."

Azima ta anshi kayan hannun Gimbiya Hakima sanann ta wuce dasu su kuma su Bilkisu suka take mata baya zuwa shashen ta, tunda Azima ta anshi kaya sai da ta kaisu kowane shashen dake cikin masarautar baki ɗaya sanann ta dawo wajen Gimbiya Hakima.

"Allah ya taimakeki, gaskiya Yarima Hakim yayi koƙari dan tunda nike ban taɓa ganin irin wanan kyautar ta ganin farko ba sai gunku."

"Uhmmm! Azima ku riba kuɗin ga duk wani bawa dake shashena sai kuyi hakuri ba yawa, sai ku fara shirin bikin kafin na baku abunda zaku bukata su kuma wanann super aura da wanann laces ɗin akai ma ɗikin fatan kinjini."?

"Allah ya taimakeki yanzun zani cika Umirninki, muna godiya Gimbiya Hakima Allah ya ƙara tsawancin kwana ya raba ki daga shirin maƙiya."

"Amin, ku wuce ku ban waje ina bukatar na huta, "to mun barki lafiya."

Haka suka tafi suna murna, ranar bayin shashen Gimbiya Hakima sunyi murna daman basu wuce su bakwai ba aiko sunsha kudi, Gimbiya Hakima ko tasha addu'oi kala-kala.

Bayan tafiyar su Lantana,  Hakima online ta hau direct *JAMEEY NOVEL FAN* ta shiga nan suka fara comment da shirhi na novels ɗin Jameey dan suna gani koƙarinta wajen yanda take baje basira take Nishad'antar da masoyan ta, bayan sun gama sannan ta sauka online ta kwanta bacci.

        *SOME DAYS LATTER*

Tunda Hakim yazo bai ƙara waiwayar Hakima ba itama bata damuba dan daman ita ba jiran wayarshi take ba balle zuwanshi, hidimar gabanta take balle biki yanzun saura sati ɗaya dilkar da halawar da ake yi mata sun ma isheta dan jike kamar ta kurma ihu da gyaran jikin da ake yi mata.

Gimbiya Yakumbo yanzun bata da lokacin zama dan gyara Hakima take ciki da waje, dan tace idan kana da kyau to ka ƙara da wanka shiyasa ta ko ina gyara Hakima take dan yanzun Hakima ta dawo shashenta da zama baki ɗaya.

Daga can bangaren kuma Gimbiya Yakumbo tsaye take tana ba Hakima maganin kariya daga shirin shidanu sannan kuma tana ƙara janjamata ta riƙe Allah dan shine gatan ko wani bawa.

Shiri suke ba kama hannun yaro, cikin lokaci ƙalilan Hakima ta koma kamar balarabiya dan baka gane ta sai tayi magana, maganar ma idan tayi sai ka kyaleta sosai zaka gane Gimbiya Hakima ce  saboda ta chanza baki ɗayan ta.

_____________________________

*×ZARIA×*

Itama Gimbiya Fulani Kubrah ba abarta a baya ba dan ta zage tayi ma Gimbiya Hakima lefe nagani da buɗe, duk da Maimartaba Sarki Abdulmatalak ya bada kuɗi amman itama ta ƙara da kuɗinta banda kuɗin da Hakim shima ya bada, dubai taje itadasu Maryama suka haɗo ma Gimbiya Hakima Lefa set 42 akayi mata banda gana most go guda shidda ba abunda ke cikinta sai bags da dai sauransu.

Bata damu da fidda hannu da su Gimbiya Zulaha suka yi ba, daman tasan haka zai faru shiyasa taita hidimar gabanta badamu da abunda suke ba, ta ba banzaye ajiyarsu.

Su kuma su Gimbiya Kilishi bakin ciki kamar ya kashesu, ba kamar yanda sukaga iyayen lafe su duk a tunaninsu Maimartaba Sarki Abdulmatalak shi ya bada kuɗin duka akayi wanann lafe ga kuma sunga dubai akaje aka haɗo su hakan ya ƙara tun zuramasu zuciya.

Gimbiya Kilishi abun ya isheta kasa zaune tayi hakan yasa ta ɗauki hanyar shashen Gimbiya Zulaha hankali tashe dan batada wata kwanciyar hankali gani take dukiyar Maimartaba ce duka Gimbiya Fulani ta ansa taje tayi ma Hakim wanann ƙarya injisu ba.

"Gimbiya wai kina ganin abunda ke faruwa cikin masarautar nan."?

Hmmm! "Ina gani Kilishi, daman tuni nasan Abdulmatalak yana nuna mana banbanci tsakaninmu da Kubrah, yafi sonta a kanmu kuma asirine kawai tayi mashi shiyasa baya saurarar kowa sai ita."

"Ina wallahi bazai saɓuba budunga a ruwa, ya zama dole muma idan su Hamad suka tashi aure ayi masu fin abunda akayi ma wance gawar, suna wahalar banza basu san saura shekara ɗaya ya mutu ba."


"Ai ni harda haka yasa na kwantar da hankali na su gama wahalar banza saura shekara ɗaya ya mutu kinga komai suka saya Hamad za'aba shi duka harda ita matar dasuke rawar ƙafa a kanta."

"Aiko dai hakane kawai mu samasu ido suka gama haukansu wawaye kawai dasu, ai gobe ne zamu kai lefe ko."? 

"Eh gobe ne, "ok muna jiran goben tayi zamu kai lefe yanda take bukata mudai musan karshen lefen namu ne."

"Ehmana, kedai bari Kilishi ni kawai sama Kubrah ido nayi tagama bikinta da dariyarta nan da shekara ɗaya kuka zatayi sannan tanaji tana gani za'a ɗaura Hamad mulki na maida ta baiwa ta bikin ciki zaiyi ajalinta."

Uhmmmm! Abunsa Kilishi tace kenan ta tafiyarta dan ita kaɗai tasan abunda zatayi ma Gimbiya Zulaha, nan da shekara ɗaya itama zatayi kuka karshe bikin ciki zaiyi ajalinta itama, dan gaban idonta za'a ɗaura Humad mulki, haka tai ta tunaninta daga karshe ta kama dariya dan gani take komai ya kusa zuwan mata karshe tana haka bacci ya kwasheta ba tare da tayi addu'a ba, to ina ma zatayi addu'a matar da ko sallah batayi.

*{yan uwa muslmai wallahi muji tsoran Allah ita wannan duniyar ba matabbata bace, duka nawa duniyar take da zakiyi ma Yar'uwarki hassada da bakin ciki bayan kunsan cewa hassada ga mai rabo takice🤔😰, to maiye abun yi ma mutun hassada bayan Allahn da baya mutun shi zai baki idan kina da rabo wanda kike ma hassada karki manta bashi ya ba kanshi ba, Allah ya bashi dan haka nidai shawarace tawa sisters murage yi ma junanmu hassada kaima kayi addu'a Allah yabaka abunda zai zamaka Alkhari ka nema Alkharin Allah, Allah yasa mudace Amin}*





_By Jameelah Jameey✍🏻_




#JameelarhSadiq@wattpad
#Share
#Comment
#Vote
#Like
#Please

GIMBIYA HAKIMAWhere stories live. Discover now