97&98

710 47 1
                                    

👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
         *GIMBIYA HAKIMA*
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻

*🌎MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️

     *M. W. A*

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻'''
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
________________________________

  _STORY AND WRITING_ _BY_

    _Jameelah jameey 🖋_

    *(Yar mutan kankia👸🏻)* 

  


*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*

_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._

'''NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR
BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍'''

97&98


Tunda safe Hakima ta tashi ta fara hidimar gabanta tunda ba ita zatayi break ba Hikimatu ce tunda room ɗinta Hakim ya kwana, daman ita ba komai take ci ba yanzun duk da cikin nata ya kai wata biyar yanzun bata da girman ciki shiyasa har yanzun ba wanda ya gane tana da ciki kuma bata shiga sabgar kowa, duk da fitinar da Hikimatu take janta, amman bata da lokacinta kuma komai Hikimatu zatayi mata bata taɓai gaya ma Hakim ba, amman ita Hikimatu komai Hakima tayi mata sai ta gaya ma Hakim, Hakim har mamaki yake dan baki ɗaya halin Hikimatu da Hakima ba ɗaya bane.

Bayan Hakim ya tashi daga bisa abin sallah azkar yayi dan yau tunda ya dawo sallahr asuba yaji bai iya komawa bacci ya cigaba da azkar ɗinshi yana gamawa yayi wanka ya shirya ya fita ya bar Hikimatu tana baccin asara, bacci take bata damu da ta tashi tayi masu break ba, daman shi tunda yake da Hikimatu bai taɓa shan koda ruwan hannun Hikimatu ba dan shi harga Allah ƙyamarta yake, bayan ya gama shiryawa ya tafi yaga ya sanyin idanuyanshi ta tashi ita da Babynshi, yana zuwa room ɗin Hakima suka cin karo da juna, ja da baya tayi sannan tayi hug ɗinshi tana cewa, "ina kwana mijina."?

Ƙara rungume ta yayi sannan yace, "lafiya lau My Jewel ya kuka kwana keda Babyn na."?..... "Uhmm, abunda jiya Babyn ma hanani bacci yayi, sai dai na tashi nai ta sallah fa.".... Ta ƙarasa maganar cikin yanga da shagwaɓa rungumeta ya ƙarayi sannan yace, "sorry Jewel ban sani ba ai da nazo munyi sallar tare ko."?... "Aa ai inasan kayi bacci ka huta, kuma Hikimatu ba bari zatayi ba, ni yanzun bansan tashin hankali."... "Ai ko da na sani da sai nazo munyi sallahr tare, amman ai yau zamuyi ko."?.... "Eh insha Allah, Angle nifa hankalina tashe yake, bansan taron mai Abba zaiyi ba yau naji Baffah yace zasuzo dan suna hanya ma, Allah yasa ba wata matar zai sake baka ba.".... Lakusar mata hanci yayi sannan yace, "Jewel bai dai tsoron kishiya kike ba."?.... "Aa Angle ban tsoron kishiya amman kasani ina sonka ina kishinka."..... "Nima ina sonki ina kishinki, insha Allah daga Hikimatu ba zan sake aure ba, kuma nasan Abba bai ƙara yi man aure tunda ga su Hamad nan, yanzun mu tafi shashen Fulani muyi breakfast kafin Yakumbo su iso ko."?.... "To shikenan masoyina ilove with all my heart.".... Love you too Jewel mu tafi karda muyi leting.".... "Ok let go."

Haka suka tafi shashen Fulani bayan sun gaidata suka fara yin breakfast.

_____________

"Gimbiya wai taron mai Abba zai yi kinga yanda akeyi ma wajen fada decoration kuwa."?

"Wallahi ko Hamad bansan taron mai zaiyi ba, ni ba wannan ne gabana ba har yanzun banji anfasa ihu ba Hakim ya mutu kuma yau shekara biyar take cika amman shiru nike ji Hamad."

GIMBIYA HAKIMAWhere stories live. Discover now