20&21 Hmm bani da abun cewa

622 54 0
                                    

👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
         *GIMBIYA HAKIMA*
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻

*🌎MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️

     *M. W. A*

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻'''
________________________________

  _STORY AND WRITING_ _BY_

    _Jameelah jameey 🖋_

   *(Yar mutan kankia👸🏻)*

*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*

_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._

'''NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR
BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍'''



21&22



"Hakim mai yasa mai kayan haka?".

"Hmmm! Aliyu kai dai kawai ni ban ma san ya zance maka ba, amman wallahi Aliyu na tsaneta"..

"Ka tsaneta? Wacece mai kuma ya hadaku? Kai da baka damu da mutane ba"..

"Ban qaunarta I hate her wallahi, Hmmm Ammn, "gaya man wai wacece Hakim?".

"Hakima wai ita sunan ta, bani san ta wallahi Aliyu, ko ganinta bani san yi"..

Nan dai Hakim ya gaya ma Aliyu yanda sukayi da Hakima..

"Bala'i ko wacece wannan bata san ko kai waye ba shiya take yi maka haka, dan haka ka nuna mata kawace ajinta ta ko ina"...

"Kyaleta Aliyu zanyi maganinta ai tace duk wanda yaci tuwo da ita miya ya sha, to zata gane kurenta bani rigar nan nasa"..

Nan Hakim ya sa rigar da Aliyu ya kawo mashi sannan suka wuce gida...

"Sannu da zuwa Maryam yau dai gaki temporary house ɗin  Hakima"..

"Gaskiya ko gani gidan Hakima, amman ita Hakima ko maganar zuwa namu gidan bata yi"..

"Karki damu kisa a ranki Hakima tazo gidanku har angama, "to Allah yasa ita Hakima da gaske take, "da ma gaske take"..

"Lantana! "Allah ya taimakeki gani gabanki ina jiran umirninki, "sai nace kuke wo ma bakuwata abin sha da abinci?".

"Muna neman sausaucin uwargijiyarmu , "mtsss! Wai ku dan Allah wasu kalar jahilai ne mararsa gwalkwalwa baki daya har yanzun baku da lissafi, komai sai kunsa mutun magana"..

"Allah ya huci zuciyarki Gimbiya Hakima yar'sarkin kano jikar sarkin yola, muna neman sausaucin Gimbiya Hakima uwar adalci, uwar marayun kano baki dayan ta"..

"Inba kuna banzaye ba... "Ya isa haka Hakima dan Allah, Maryam ta fada ta mai daga ma Hakima hannu ranta a bace dan taji haushin abunda Hakima tayi masu Lantana gasu sun fara manyanta.

"Mama tashi ki dauko mana abinci ki kawo mana cikin daki, "to godiya nike ranki yadaɗ'e"..

"Hakima mu shiga ciki mana, "maiyasa kika yi man haka a gaban bayi na? ''.

"Shi ne nace mu shiga daga ciki magana zamuyi, "Uhmmm"..

Nan su Lantana suka kawo ma Gimbiya Hakima abinci..

GIMBIYA HAKIMAWhere stories live. Discover now