19&20. Muje zuwa kawai MY FANS

647 76 6
                                    

👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻
         *GIMBIYA HAKIMA*
👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻👸🏻

*🌎MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION* 📚🖊️

     *M. W. A*

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu. Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta ta kuma Nishad'antar da masoyan ta. 🤙🏻'''
________________________________

  _STORY AND WRITING_ _BY_

    _Jameelah jameey 🖋_

   *(Yar mutan kankia👸🏻)*

*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*

_Wannan labarin kagaggen ne, duk wanda yazo daidai da rayuwarshi a kasi ne._

'''NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA FATIMA ABUBAKAR
BELLO, ALLAH YA BAR KAUNA YAR UWA RABIN JIKI😍😍'''

19&20

Washe gari bayan Lantana ta gama shiryawama Hakima littafan ta, saboda karatun da Gimbiyar ta fara na dare dan cikin week din nan zasu fara tests din su dan haka shiyasa ta fara karatun ta..


"Lantana! "Allah ya taimakeki gani gabanki ina jiran umirninki"..

"Maza kije kice ma Bala, ya fiddo mota yanzun dan ayi fixing din lecture yanzun nan, dan haka yayi maza ya fiddo mota, gani nan fitowa"...

"Allah ya kara maki jaraja angama, "Amin, nan Lantana ta tafi wajen Bala...

"Malam Bala, ka tashi lafiya? "Lafiya lau Lantana, ya aiki? ''Aiki da godiya, "To Allah ya bamu ladar, "amin"..

"Sako daga Gimbiya Hakima, "mai kuma nayi Lantana?". 

"Kwantar da hankalinka, ba abunda kayi, "Alhmdulh, kin san wallahi Lantana ban san abunda zai hadani da Gimbiya Hakima da girmanka da mutuncinka, amman Gimbiya Hakima sai ta taci maka mutunci cikin mutane"..

"Hakane gaskiya, Allah ya kara tsaremu daga cin mutuncin ta, "Amin Lantana, mai ita Gimbiya Hakima tace maki?". 

"Cewa tayi ka fiddo mota yanzun dan an maido masu da koyarwa yanzun da safen nan, shine tace ki fiddo mota ga tanan fitowa"..

"To shikenan, ai yanzun kuwa zan fiddo ta, "ni na wuce Bala na barma lafiya"..

Nan Lantana taje ta gayama Gimbiya Hakima an fiddo mota..

"To ni zan wuce Bilkisu yau ki san kuyi man dambun masara, ku samu zagole kusa a cikin dan yau da bakuwa zamu dawo kuma tana san dambu"...

"Angama uwargijiyarmu, Allah yabada sa'a, "Uhmmm, sannan ta gama gaban tana saurin dan yanzun seven thirty tayi gashi lecture din eight yayi fixed dinta, bayan basu da wata lecture sai two amman dan mugunta ya maidota eight...

"Bala kayi sauri, ban san na makara ka sani, dan haka kasan yanda zakayi kafin eight na ganin acikin lecture hall"..

"To Gimbiya uwar marayu, Gimbiya diyar sarki uwar sarki insha Allah"..

Nan Bala ya kama bankama mota wuta, Gimbiya Hakima sai da taji tsoron kalar gudun da Bala yake da ita cikin mota, to amman bata da choice ɗin hana shi, dan idan sukayi wasa kan titin to zatayi lating ne, kuma bata san wani abu yake hadata da Yarima Hakim, shiyasa tayi hakuri tana ganin rayuwarta a iska..

(Lol sun Gimbiya Hakima ashe dai ana tsoro, kike iskanci🙃)

Cikin ikon Allah, karfe eight dai-dai tayi ma Gimbiya Hakima cikin makaranta tana hango Yarima Hakim shima lokacin ya fito office din shi, dan haka tayi sauri ta shige warta ta zauna nan Maryam itama lokacin ta shigo ta zauna kusa da kawarta...

GIMBIYA HAKIMAWhere stories live. Discover now