Kwanan su uku a asibiti aka sallamesu, shima kwana ukun nan ba wai dan suna da wani problem ne ba, kawai dan dai haka tsarin asibitin yake, in mace ta haihu sai ta kwana uku an tabbatar da lafiyarta data abinda ta haifa sannan za'a sallameta. Baffan Nura ne yace zai yiwa jariran yanka a can, tunda anan basu da kowa ya zasu yi da abin yankan. Ranar suna da safe Nura ya dauke su  yayi musu huduba, ya saka su a rocker yana jijjiga su Aisha ta fito daga wanka, ya juyo yana kallonta yace "maijego" ta turo baki bata kula shi ba ta fara shafa mai a bronze skin dinta da take kyalli tana daukan idon Nura, Ya taso ya dauki man yana shafa mata a bayanta yace "me kuma nayi?" Tace "naga alamar har yau ranar sunan ma baka da niyyar gaya min sunayen su" ya dauki comb yana taje mata kanta yace "sunan su Muhammad" ta na kallonsa ta mirror tace "wanne ne Muhammad din a ciki?" Yace "duk su biyun. Uwarsu daya ubansu daya, mahaifa daya, placenta daya kuma kamanni daya, so why not suyi sharing suna daya?".

Aisha ta daina abinda take ta saki baki tana kallonsa tace "to yanzu in aka kira Muhammad wanne ne daga ciki zai amsa?" Nura yayi dariyar yadda ta saki baki yace "babu wanda zai amsa tunda bada Muhammad za'ake kiransu ba, sunan yayi girma da yawa, Hassan sunansa Muhammad Ahmad Junaid, Hussain Sunansa Muhammad Ahmad Tijjani" ta juyo taja habarsa tace "you my dear are very dramatic, I like the names" yace "and I like you" yayi mata kiss a lips.

Bayan Aisha ta shirya ne yaran suka fara mutsu mutsu, ya dauki daya itama ta dauki daya suka zauna a bakin gado ita tana breastfeeding daya shi yana bottle feeding daya. She looked at Nura and then the babies and smile, wani irin farin ciki take ji marar misaltuwa a zuciyarta, irin feeling din nan na in komai naka yayi turning out to be alright, but yet, some part of her was missing, one small part, one important part. Her Sister.

Nine Years Later...

Taro ne ake gudanarwa a gidan marayu mai zaman kansa na Abuja. Taro ne wanda gidan ya saba gudanarwa lokaci zuwa lokaci dan bawa mutane damar zuwa suga yaran su kuma bada gudummawar da suke da niyya ba wai dan mai orphanage din ya gaza ba sai dan a bawa mutanen gari dama suma su zama involved gurin harkar marayun. San nan wadanda suke son adopting su zaba tare da cike duk takardun da suka kamata wadanda doka ta tanadar dan tabbatar da komawar hakkin yaran gurin masu daukan nasu. A irin wadannan taron ne kuma ake gabatar da bukatun orphanage din, sannan kuma ana bawa mutane damar su kawo shawarwarin da zasu bunkasa gurin da kuma kyautata rayuwar yaran.

Ana tsakiya ta taron ne wata katuwar mota ta shigo gurin, shugabar masu kula da gurin ce ta mike da sauri ta fita, sauran ma'aikatan gurin ma duk suka mike suka mara mata baya. Yaran da suke zazzaune kuma suka fara murna wadansu daga cikinsu suna tafa hannayensu dan nuna jin dadin su. Motar tana packing mai tuka ta ya fito da sauri ya bude kofar baya sannan ya durkusa yana gyarawa mai fitowa daga motar takalminta. Saurin da yayi gurin fitowa zai saka mutum ya dauka driver ne, amma kallo daya zakayi masa kasan cewa ba driver bane ba, shekarunsa ba zasu wuce ashirin ba ko ashirin da daya, kyau, jin dadi tarbiyya da kuma kamar da yake da wadda ta fito din zai sa ka tabbatar da cewa dan ta ne. Ta fito tana kare hasken rana da tafin hannunta, kyakykyawar gaske ce wadda shekarunta basu rage ko kadan daga kyanta ba, murmushin da baya barin fuskarta yana nan, ta saka hannu ta hargitsa kwantaccen gashin wanda ya bude mata kofar shi kuma ya bata rai alamar shagwaba sannan ya zagaya ya bude daya barin. Wata mata ce ta sake fitowa daga kofar. Baka ce, wadda jin dadi da kwanciyar hankali ya kara fito da boyayyen kyanta. Fuskarta dauke da sun glasses wanda ya kara kawata kyakykyawar fuskar tata, ta saka dan yatsan da yasha adon zoben gwal ta lakuci kumatun wanda ya bude mata kofar, ya sake bata rai har yana buga kafa a kasa ita kuma tana yi masa dariya. A tare matan suka taka suka nufi inda 'yan taryan nasu suke tahowa. Shi kuma dan saurayin ya juya zai koma seat dinsa inda ya bar kofa a bude saboda sauri sai yaji anyi masa magana daga seat din kusa da driver "psst, aren't you forgetting something Bassam?" Ya jefa mata harara tare da tsaki yace "ki shiga hankalinki Basma. In kika bari na zagayo na shiga motar nan ba tare da kin fito ba sai jikinki ya gaya miki wallahi" bata fito ba har ya zagayo din sannan ta bude kofar da gudu ta fita ta bar masa kofar a bude ta juyo tayi masa gwalo shi kuma yayi mata sign din I will kill you.

A cikin gurin taron bayan kowa ya koma ya zauna, mai gabatarwa ta gabatar da Dr Maimoon Muhammad Dikko tare da aminiyarta kuma ta hannun damanta Dr Aisha Zayyan. Daga nan kuma sai Dr Maimoon ta karbi mick ta yi jawabin godiya ga duk wadanda suka samu halartar taron sannan kuma ta bayar da hakuri a bisa makarar da tayi ta kuma bada hakurin rashin samun zuwan maigidanta "abubuwa sunyi masa yawa sosai yanzu, tunda yanzu kusan shi yake gabatar da duk al'amuran masarautar mu saboda rashin lafiyar maimartaba sarki. Dan haka from today ni zan cigaba da gudanar da duk abinda ya shafi wannan orphanage din" daga nan kuma aka fara gabatar da bukatun orphanage din, kusan basu da wata bukata tunda yawanci kafin a bukaci abu har Dr da maigidanta sun aiwatar, abinda kawai suka nema a wannan taron shine gyaran wadansu fanfuna da electric appliances da suka lalace, wanda a take Dr Aisha tace ta dauki nauyin wannan. Daga nan kuma sai aka bada dama ga wadanda suka yi applying for adoption dasu zagaya su ga yaran su kuma zabi wadanda suke so suyi adopting.

An jera yaran ne according to their ages, ma'ana jarirai ne a farko wadanda aka shirya cikin shiga mai kyau rike a hannun nannies, daga nan sai 1-3 year, bayan su kuma 3-6 years a haka har 12 year wadanda da wahala yaro a wannan orphanage din ya wuce 12 ba'a yi adopting dinsa ba saboda irin kulawa da tarbiyyar da suke samu. Aisha tana daga zaune a high table take bin yaran da kallo tana murmushin yadda suke ta doki suna so a zaba dasu suma su samu family, duk wanda aka zaba kuma sai murna. Kowa a cikinsu yana murmushi kuma daga anzo kusa dashi sai ya durkusa yayi gaisuwa dan ya nuna tarbiyyarsa dan ya samu a zabe shi.

Aisha taji tausayinsu a ranta, duk da dai ba abinda suka nema suka rasa amma kuma inside them they are yearning for a family, Family. Ta jima tana son tayi adopting amma maigidanta yana hana ta, shi gani yake kamar rashin 'ya'yan da basu dasu da yawa ne yasa take son adopting ita kuma ba haka bane, dan twins dinta kadai sun ishe ta duniya da lahira, abinda take so shine taimako, taimakon maraya.

A lokacin ne idonta yakai kan wata yarinya a can karshen baya. Daga farko ta dauka ita ma a cikin bakin tazo, sai daga baya ta lura da tag din wuyan yarinyar irin na sauran yaran ne, amma bata cikin kowanne layi saboda ta girmi kowa a gurin dan kallo daya in kayi mata zaka iya kiranta da cikakkiyar budurwa, sai dai kuma in ka kare mata kallo zaka gane cewa girman burodi ne dan ba zata wuce 15 ba, highest 16 years.

Dogon hijab ne a jikinta wanda ya kai har gwuiwar ta amma duk da haka bai boye cikar kirjinta ba, ta kankame jikinta da hannayenta tana ta rarraba idanu kamar wacce take jiran abu kadan ta fita a guje. Tsabar tsoro ne a rubuce baro baro a fuskarta. Aisha ta lura da cewa da yawa daga cikin mutanen basa ma karasawa kusa da ita suke juyawa, idan kuma an samu wasu sun karasa gurin nata sai ta kara takure kanta a jikin bango ba tare da ko gaishe su tayi ba. Dagabaya sai Aisha ta lura cewa mutane da yawa a gurin suna kallon yarinyar suna maganganu kasa kasa.

A haka har taro ya kare, kusan duk wanda yazo adoption ya samu abinda yake so, daga yaran har sababbin iyayensu suna ta murna. Bayan kowa ya watse ne sai suka tafi office din director din orphanage din, nan suka zauna aka kawo musu abubuwan motsa baki sannan director din ta gabatarwa da Dr Maimoon takardun da suke bukatar saka hannunta, daga nan kuma suka maganganunsu akan gurin wanda Aisha ba gane wa take yi ba dan haka ta juya gurin Basma suke hirar su.

Ana cikin haka ne taji director din tace "Dr saura kuma zancen yarinyar nan, kinga last adoptive parents dinta sun dawo da ita suma, gashi yau ma naga babu wanda yako yi attempting daukanta" Mami tayi ajjiyar zuciya tace "to yanzu menene shawara? Ya kike ganin zamuyi da ita?" Director tace "we just have to let her go. Ai Allah ya gani munyi iyakacin kokarin mu. Tayi girma da yawa ina gudun gurbacewar tarbiyyar sauran yaran mu" Da sauri Mami tace "let her go? Let her go where? Yarinya budurwa kamar wannan zamu bude wa gate muce mata go? Bayan munsan bata da kowa a duniya?"

Director tayi shiru dan ta fahimci shawarar tata ta bata ran Mami, Aisha ta matso tana tambayar wacce yarinya ce, Mami bata bata amsa ba tace da director din ta kira yarinyar, sai da ta fita sannan Mami tace da Aisha "yarinya ce kinga, ta jima a sabon orphanage dinmu na lagos duk wanda ya dauke ta saiya dawo da ita, sai suka turo ta Kano shima nan bata chanza zani ba, yanzu shekarar ta biyu anan gurin mu kuma an kaita sama da gida biyar kenan amma wani gidan ko sati bata yi suke dawo mana da ita" Aisha ta tabbatar yarinyar data gani dazu ce. Suna cikin maganar sai gata ta shigo a bayan director, ta samu gefe daya ta rakube kamar zata shige bango. Mami tana kallonta tace "babu gaisuwa HUMAIRAH" ?

Ta dago dara daran idanuwanta wadanda suka rine kalar ja saboda kukan ta tun safe take yi, ta sauke su akan Mami, sannan cikin ranar murya tace "Mami sannu da zuwa" take kuma hawayen da take rikewa tun da ta shigo gurin suka sauko akan kuncinta.

What do you think?

Aisha_HumairahUnde poveștirile trăiesc. Descoperă acum