Ajiyar zuciya ya saki sannan ya dan bata rai yace “wai haka zaki shiga?”

Ta kalli jikinta tace “eh Yaaya... ban yi kyau bane?”

Aikuwa nan da nan ta nemi ta fara kuka....

Da sauri yace "Hey dont cry... you shouldn't ruin your make up"

Hannunta ya kamo ya riqe sannan yace “On the contrary, kinyi kyau sossai... what I am trying to say is, shi dinkin haka aka yi shi? aren’t you suppose to cover yourself up with a veil or something?”

Zara wadda ta turo baki tace "Haka yake Yaaya..."

Shiru na ga ta dan yi sannan tace "wait... are you jealous?” yayinda ta kashe mishi ido dqya.

"Nope" ya fada while trying to look unbothered amma ya kasa.

it's written all over him that he is jealous!

Side hug ta bashi tace "Please dont be..."

******************

Qawayen amarya da abokanen ango ne suka jagoranci shigowa hall din.

Bayan sun shigo ne Ango da Amarya ma suka shigo riqe da hannuwan juna.

Sunyi masifar kyau... Sai hotuna ake daukar su yayinda MC yake ta yaba kyan da suka yi tare da wasa su....

"Ya Farouq please ka rage sauri mana"

"wa yace ki sa dogon takalmi? kin cika rigima I swear"

Fashewa tayi da dariya tace “toh Ya Farouq kai ne ai you are tall, idan ban sa takalmi mai tsawo ba za’a yi mun kallon dwarf”

Fashewa yayi dariya shima tare da rage sauri....

Gani nayi ya janyo ta jikinshi tare da bata support... Hakan ya sa ta maqale a jikinshi kamar wata mage yayinda suka cigaba da hira not minding the number of eyes that are on them.

Daddy ya kalli Abba wadanda suke zaune tare da abokanen su yace “ka gan su ko? Kamar ba su bane suke ta bata rai don mun ce zamu hada su”

Abba yana dariya yace “ai wadannan yaran ka qyale su kawai”

Zara dai yau all white ta sa na wani shegen dinki mai masifar kyau da Galiafahad yayi mata, tayi masifar kyau.

Biki dai yayi biki, ana ta shagali. An ci an sha sannan anyi rawa.

A lokacin da MC ya kira Zara ta fito tayi rawa tare da qawayen ta ne Farouq ya hana.

Abu dai kamar wasa MC ya dage akan lallai sai Farouq ya bari ta fito amma ya qi.

Haka kuwa aka dinga yi musu dariya.

“gaskiya idan ba qwaqwarar dalili zaka bamu ba bazamu yarda ba sai amarya ta fito...”

Farouq wanda ran shi ya fara baci da insistence din MC din ne yace “qafarta na ciwo”

Gaba daya hall din aka fashe da dariya yayinda MC ya kalli Zara yace “Amarya wai dagaske qafar ki na ciwo?”

Zara ce na ga ta kalli Farouq looking Sad tace “Ya Farouq please ka bari inyi kadan... ka ga na kamu da na fara shima janye ni kayi..”

BA SON TA NAKE BA | ✔Where stories live. Discover now