Har a wannan lokacin kuwa Zara tana nan riqe da hannun shi yayinda ta ji yace “you look beautiful though”

Da sauri tace "what??" tare da dawowa gaban shi ta tsaya tana kallon shi wanda hakan ya sa shima ya tsaya yana kallonta..

"what?? did I say anything worth this reaction??"

“Ya Farouq??” ta fada cike da mamaki

“what??” ya qara fadi shima looking a bit confused this time..

Bai ankara ba ya ji ta shige jikinshi tayi hugging dinshi tana fadin “Ya Farouq this is actually the first time da kace mun nayi kyau, Your compliment means so much to me.. thank you very much”

Gani nayi ya girgiza kai har yana murmushi.. who will take a compliment like that as a big deal idan ba Zara ba...

Tuni na hango ana ta daukar su hotuna yayinda ake ta maganar how cute they look together... infact alot of people a cikin hall din thought Mata da miji ne because sunyi masifar dacewa.

Mukhtar da Hafsat dai kallon juna suka yi suna ta dariya yayinda Mamy da ke zaune tare da su Mom ta dafe kai tace “yau na shiga uku da yaran nan”

Mom tana dariya tace “ai wadannan aure kawai yakamata ku hada su”

MC ne ya matso kusa da su yace “barka da zuwa Farouq da Zara yara a gidan CBN Governor Alhaji Al-Hussain Umar Jimeta”

Da sauri na ga Zara tayi breaking hug din ta ja baya kadan tana kallon fuskar Farouq..

She expected to see an angry Farouq who might even attempt to slap her a dalilin abinda tayi mishi amma to her suprise sai ta ga yana kallonta with a very little smile on his face.

"Ya Farouq don Allah kayi haquri.."

"Ya zanyi da ke tunda ba kya jin magana.. laifi na ne da nace kinyi kyau" ya fada yayinda ya cigaba da tafiya abinshi.

Ita kuwa bin shi da kallo tayi tana murmushi...

The first time da Farouq ya zama so nice to her!!

MC dai anan suka bar shi yana ta aikin shi na magana...

*******************

Haka dai aka cigaba da shagalin biki... Taro yayi taro yayinda aka ci aka sha.

Zara wadda take bala’in son rawa haka ta zage ta dinga rawa a cikin mutane.

Farouq wanda ya hango ta kuwa gaba daya sai ta bashi haushi... how can she be dancing in front of people like this??

He turned his face away from her without looking again... babu shakka ta bashi haushi!

Wayar shi ce tayi ringing ya duba..

Ruqayya ce! 

Miqewa yayi ya koma can wani corner kusa da exit inda babu hayaniya sossai sannan yayi answering.

“Honey wai me kake yi da yarinyar nan? Yanzu na ga wani post a instagram tayi hugging dinka” ta fada cikin masifa.

“hey relax, it’s nothing. I will explain when I get home” ya fada calmly don kuwa ya sani cewa she has every right to be angry.

Cikin muryar kuka tace “amma Honey…”

“Wifey not now.. we will talk when I get back, sai na dawo, take care”

Bai tsaya jiranta ba ya kashe wayar.

Yana shirin tashi ne ya ji ance “Ya Farouq ina wuni”

Dago kai yayi ya ga qanwar Anty wato Saima.

BA SON TA NAKE BA | ✔Where stories live. Discover now