***************

Yana kan hanyar zuwa asibiti ne wayar shi tayi ringing.

Mukhtar ne!

Tunda ya dawo jiya Mukhtar din yake ta kiran shi a waya amma ya qi amsawa saboda haushin shi da ya ji a dalilin tura Zara da yayi ta je ta dauko shi daga airport.

Yanzu haka he had no choice but to pick the call domin kuwa Mukhtar ya wuce aboki a wurin Farouq, aminan juna ne sossai, babu secrets din junan su da basu sani ba.

“Muky kayi mun laifi, you should have informed me cewa bazaka zo ba, da na shiga cab ai”

“Haba dan uwa, me yayi zafi? Duk yawan motocin da ke gida a rasa wadda za’a dauko ka da ita sai ka shigo cab? Please kayi haquri”

Cikin tsokana ya cigaba da fadin “Na dai san fushin nan ba don komai ake yin shi ba sai don personal trouble dinka da ta je instead of me”

Farouq ya girgiza kai yace “da gangan ka qi zuwa kenan??”

Mukhtar ya fashe da dariya yace “ko kadan abokina, wallahi aiki ne yayi mun yawa”

“yeah I know abokina, its not easy being an executive”

“haka dai kace Doc”

Farouq yana dariya yace “I am on my way to the hospital yanzu, insha Allah anjima I will check on you”

"Okay abokina"

♤♤♤♤♤♤♤♤♤♤♤♤♤

MUKHTAR ABUBAKAR MANSION
MAITAMA ABUJA

Zaune suke a falon Mukhtar suna buga game kamar kullum.

Mukhtar ne yace “abokina ka gaya mun gaskiya are you really happy with Ruqayya?”

Farouq ya harare shi yace “me ka gani?”

“I can tell idan you are excited about something, akan Ruqayya na kula you are always cold”

Farouq ya saki ajiyar zuciya sannan ya ajiye control pad din dake hannun shi ya kalli abokin shi yace “the honest truth abokina shine ban san me nake ji game da Ruqayya ba, ina ta qoqarin in so ta kamar yadda yakamata amma na kasa. I have realised cewa BA SONTA NAKE BA”

Mukhtar yayi murmushi yace “ita din dai kake so kenan”

Cikin rashin fahimta Farouq yace “wa kenan?”

“Zara”

Runtse idanuwan shi yayi ya bude tare da murtuke fuska ya ja tsaki yace “what the hell abokina, sau nawa zamuyi maganan nan??”

“yeah yeah, ka damu da ita amma baka so ta raina ka blah blah blah, abokina na san ka tun muna yara, ba sai ka gaya mun abinda na riga na sani ba. anyways, whenever you need someone to talk to You can always count on me..”

Wayar Farouq ce tayi qara alamar an aiko mishi message. Ko da ya duba hotunan Zara ne ta aiko mishi kamar kullum.

Murmushi yayi wanda bai ma san yayi ba a dalilin wani funny face da tayi making in one of the photos 

“its her... isn’t it?”

Hararar shi yayi yace “bari in tafi gida tunda yau takura mun zaka yi”

“yi haquri abokina, na bar maganar”

♤♤♤♤♤♤♤♤♤♤♤♤♤

CALEDONIAN SUITES
MAITAMA ABUJA

Ruqayya ce kwance a kan gadon daya daga cikin dakunan Hotel din yayinda take kallon shi.

Fitowan shi kenan daga wanka.

BA SON TA NAKE BA | ✔Where stories live. Discover now