Wuraren qarfe goma sha daya Mamy ta qwanqwaso qofar dakin ta shigo. Murmushi tayi ta nufi gadon ta zauna tare da zare pillow din da Zara ta rufe fuskarta da shi.

Motsi tayi ba tare da ta bude idanuwan ta ba tace “Mamy please”

“I thought kin ce zaki je gidan su Hafsat yau”

Da sauri Zara ta bude idanuwanta ta miqe tana fadin “oh my God, whats the time? Yau Hafsy zata ci qaniya na”

Mamy tana murmushi tace “its just past 11, maza je kiyi wanka ki sauko kiyi breakfast”

Zara ta sauka daga kan gadonta sannan ta duqo tayi ma Mamy kiss a kumatu tace “okay Mamy.. thanks for waking me up” ta nufi dressing room dinta don shirin wanka yayinda Mamy tayi murmushi ta miqe ta fita.

Zaune take a cikin qaton Jacuzzi din kewayen ta, qamshi kawai ke tashi kamar anyi barin turarruka, wasa take da ruwan kamar kullum. Idanuwan ta a lumshe suke yayin da take jin dadin ruwan da take ciki. Tayi kusan minti talatin a cikin Jacuzzi din sannan ta dauraye jikinta ta fito.

Tana zaune a gaban Vanity mirror tana ta shafe shafen mai da turaruka. Wayar ta ce tayi ringing, ta miqe ta nufi bed side drawer inda wayar take ta dauka.

Ganin sunan Hafsat ne yasa tayi murmushi ta amsa tare da fadin “Babes how far” a dayan bangaren Hafsat tace “wallahi if it were possible for me to change a friend I would have done so tuntuni Zara”

“toh ko zaki gwada ne?”

Hafsat ta ja tsaki tace “are you daring me?”

Zara ta fashe da dariya tare da hawa kan gadonta tace “sorry bestie, I love you”

“and I hate you, where have you been ina ta kiran ki tun dazu? Hala kina ta baccin nan naki na mamaki?”

“sorry babes gani har nayi wanka ma, as soon as I eat my breakfast zan qaraso”

Bayan sunyi sallama ne ta nufi closet dinta don daukan rigar da zata sa.

Tsayawa tayi tana bin kayan ta kamar kullum, wata farar long top ta hango can qasan jerin kayan ta. Murmushi tayi tace “its definitely you baby”

Dakinta ta koma ta latsa intercom, a dayan bangaren Larai ce ta amsa cikin girmamawa.

“please come”

Cikin mintuna biyu kacal Larai ta turo qofar dakin Zara cikin ladabi ta duqa har qasa tace “ina kwana Anty”

“lafiya Larai ba sai kin duqa ba kafin ki gaishe ni, zo ki cire mun wannan kayan”

Larai ta miqe ta bi Zara har closet dinta sannan ta nuna mata kayan da zata ciro mata ta juya ta koma dakin.

Zara ta sani sarai idan da kanta zata zaro kayan gaba daya sai ta birkita closet din shiyasa ta sa Larai ta dauko mata.

Tana nan zaune Larai ta fitar mata da kayanta sannan ta fita.

Bayan ta shirya ne ta dauki wayar ta tare da makullin motarta ta fita.

Ko da ta sauko straight dinning ta wuce ta zauna, kayan abinci ne aka jera kala kala kamar kullum.

Murmushi tayi ta sa hannu zata bude warmer din da ke gaban ta sai ga asabe ta shigo da sauri tace “Anty bari in zuba miki”

Cikin ladabi ta duqa har qasa tace “ina kwana”

Zara wadda ta fara gajiya da extra ladabin da masu aikin suke yi mata ce ta girgiza kai tace “tashi asabe, lafiya lau”

Plantain ta nuna mata tace “I will take this only”

Nan da nan Asabe tayi serving dinta sannan ta koma kicin.

BA SON TA NAKE BA | ✔Where stories live. Discover now