50

11.1K 689 129
                                    

{50}

"Yau zan je Sokoto, zan dawo da Nazifa." Ya fad'a a takaice, yana 6oye musu ainihin gaskiyar dalilin dawowarta, don kare mata nata hakkin da mutuncin.

Tun ba yau ba suke rok'an ya dawo da ita, amma baya ko saurarensu. Yanzu da Baba ya mishi magana ya gane cewa shima da laifinshi a rashin hankalin Nazifa, kuma yana son ya gyara wannan kuskuren.

Kamar yanda ya zata hakan ya faru. Sun yi murna kowacce in da suka ce zasu tsaya a share mata part d'in nata.
Sa'adatu ce ta fita ta basu guri domin girkin Adama ne. Tana fita yaje ya kashe treadmill din yana cewa,
  "Muje In nuna miki wani abu a d'aki. 

A ranar da dare, Adama ce ke had'a kayan da Anwar zai yi tafiya dasu, Set din jumfa d'aya ta cire mishi da singlet hade da boxer, sai brush, body spray da turare.
A d'an k'aramin trolley ta jera masa kana ta rufe ta kai motan da zai tafi da ita. Duk abunda take yi Anwar na kwance kan gado yayi ruf da ciki yana kallon duk wani motsinta.
Sanye take cikin Fitted gown na Atamfa da ya bi zubin jikinta, ko'ina a jikinta kamshi ke tashi kamar an yi 6arin turare, d'aurin d'ankwalinta ture-kaga-tsiya ya fitar da dara-daran idanunta, ta shafa nude lip gloss da ya fitar da ainihin kalan la66anta, wanda ke sa Anwar tunanin in ya samesu bazai sake da wuri ba.
Yana cikin tunaninshi har ta je ta dawo ta tsaya kanshi tana masa magana. Bai saurareta ba don yasan maganar d'aya ce,
"Ka tashi kayi wanka kar kayi bacci a haka." Tana jawo hannunshi yana mak'ewa.
Jawota yayi ta fad'o jikinshi yayi saurin matseta yanda baza ta gudu ba, ya ce,
"Kinsan jiya nasha Kunun Aya, kuma da gaske fa marana yana ciwo sosai." Ya fad'a a shagwa6ance yana lalumar lips d'inta.
Murmushi ta yi ta biye mishi don ta dasa tunaninta a ranshi har yaje ya dawo yana kewarta.

Washegari Anwar bai samu Kansa ba sai K'arfe d'aya na rana dalilin aiki daya rik'eshi. Yana idar da sallah azahar ya kama hanyar sokoto shi da Abdallah. Cikin dare suka isa, hakan ya saka suka kama d'aki a Hotel zuwa safiya.
Tun asuba da ya tashi bai koma bacci ba, yana tunanin had'uwarshi da Nazifa. Shin zata gwada halinta ko kuma yanzu ta yi hankali ta canja d'abiu?
Gari na haske ya tashi yayi wanka ya shirya cikin fararen kaya, yayi kyau kamar bak'in balarabe. Sai da ya tattara komai nasa ya fito ya kwankwasa d'akin Abdallah yana jira ya bud'e.
Ganin Abdallah yayi a hargitse da alama yanzu ma ya tashi daga bacci, ran Anwar ya 6aci.
"Ban fad'a maka cewa da safe zamu fita ba don mu kama hanya da wuri?" Ya tambayi Abdallah dake sosa k'eya don yasan yayi laifi.
In-ina ya fara, Anwar ya bashi kud'i yace
"Ka hau Taxi ka sameni a gidan. Minti goma na baka ka sameni a can." Da haka ya fita ya biya Restaurant d'in da ke Hotel d'in yasha Coffee ya kama hanyar gidansu Nazifa.

Ta kwashe sakwanni kafin hankalinta ya dawo dai-dai, tana waswasin abunda idonta ke gane mata. Shin Anwar ne ko kuma mafarki take yi kamar yanda ta saba?
Fitowan Ma'u yasa ta tashi daga bakin murhun ta shige gida da sauri. A zauren gidan ta tsaya tana numfarfashi kamar wacce ta yi tsere, har yanzu bata yarda cewa Anwar ne tsaye a k'ofar gidansu ba. Shin me ya kawoshi? Ko yazo ya k'ara mata wasu sakin ne kan wanda ya mata? Tasan tsakaninsu yanzu sai ikon Allah, don lokaci yayi da ta tabbatarwa kanta sani cewa Anwar yafi k'arfin mace irinta. Me zai yi da mace mara ilimi mara hankali da tunani? Macen da bata damu da ibadarta ba balle har ayi tunanin zata koyawa 'yayanta? Macen da bata amsa sunanta mace ba tunda ta lalata gabanta. Macen da maganar k'awayenta yafi maganar mijinta?
Duk abunda ya mata ta cancanci fiye da haka ma. Idanunta ne suka ciko da kwalla ta yi saurin shanyewa ta shige gida, zuciyarta na son lek'a waje amma ta haramtawa kanta kallon mutumin da ta cuta a rayuwar aurensu.
D'aki ta shige can ciki, ta samu katifarta dake jingine da bango ta shimfid'a a k'asa ta zauna akai tana aikin tunanin da ya zame mata d'abia.
Sunanta da ake kira a tsakar gida ya sakata mik'ewa da sauri tana zare ido, zuciyarta ta ci gaba da bugawa. Hijabinta ta mayar jikinta ta lek'o tsakar gidan in da Mamarta ke shimfid'a tabarma, Anwar da Abdallah na k'okarin kar6a.
A bakin k'ofa ta tsaya ta zubawa Anwar ido da a ganinta kamar ya k'ara kyau da haske, yanzu wannan kyakkyawar halittan mijinta ne a da? Ina hankalinta yake da har ta bari rud'in duniya yasa ta masa laifi ya saketa? Ina ma ina ma! Ina ma koma baya! Ina ma ace yau ne ranar da yazo d'aurin aurensu yazo tafiya da ita zuwa duniyarsa! Da hakan zai faru da ta fi kowanne Bil'adama murna a duniya. Ina ma!
"Nazifa kina jina kuwa?" Ta jiyo muryar Mamarta cike da bacin rai.
"Ina jinki, ina wannan ne." Ta samu kanta da fad'i bayan ta sunkuyar da kanta, ganin irin kallon da Anwar da Abdallah suke aiko mata. Kunyace ta rufeta ta koma cikin falon ta zauna.
"Nace ki kawo musu ruwa da kunun gyad'a, sai ki d'ebo musu k'osai a waje in kun fara tuyar."
Jiki a sanyaye ta fito ta gaishe da Anwar ya amsa a takaice, sannan ta shiga kitchen d'ebo musu kunun. Tana ji Anwar na cewa shi a k'oshe yake, yayin da Abdallah yace shi zai ci.
A gabansu ta ajiye jug da kofuna biyu sannan ta d'auki kula ta fita d'auko musu Kosai. Bata jima ba ta dawo ta ajiye musu ta koma falo tana tunanin me ya kawo Anwar.
Tana zaune Abdallah ya shigo falon ya samu guri ya zauna a k'asa, bud'e kosan yayi ya fara ci yana korawa da kunu ko ya kulata. A can waje kuma Anwar ne ke magana da Mamanta wanda duk yanda ta yi ta kasa gane mai suke cewa.
"Abdallah me kuka zo yi?" Ta katse shirun dake tsakaninta da Abdallah.
"Sai yanzu kika ga daman yi mini magana?" Shima ya tambayeta yana k'urban kunu.
"Kayi hakuri nasan ban kyauta ba da naki d'aukan wayoyinku, bansan me zance muku ba bayan duk abunda ya faru, kawai bansan me zan yi bane. Kuyi hakuri." Tace dashi cikin nadama, don tun da ta dawo gida suke kiranta a waya shi da Farida amma bata d'auka. Bata son ace sun d'auki Yayansu a ransu alhali duk laifi nata ne ba nashi ba.
Abdallah kwarewa yayi da kunun da yake sha don bai ta6a jin Nazifa ta bawa wani hak'uri ba. Dariya yayi a ransa yace 'shege wuya'. A fili kuma yace,
"Ba komai, ya wuce."
"To me kuka zo yi?" Ta k'ara tambayanshi cike da fargaba.
"Nima wallahi ban sani ba. Haka kawai ya kirani jiya yace zamu yi tafiya. Ban ma san ina zamu zo ba sai da muka kama hanya. Amma ina zaton komawa zaki yi."
Gwalalo ido Nazifa ta yi don bata ta6a kawo hakan a ranta ba, cikinta ne ya murd'a ya bada k'ara kamar had'uwar gajimare. Abdallah da ke d'an nesa da ita ya tsaya kallonta ganin rud'ewan da ta yi.
"Lafiyanki kuwa?" Ya tambayeta yana ajiye kosan hannunsa don ta razanashi shima.
"Ba komai. Cikina ne ya fara ciwo." Da haka ta tashi ta shige can k'uryan d'akin ta barshi a falo. Zama ta yi gefen katifarta tana dafe da zuciyarta dake bugawa kamar zai tsago ta k'irjinta. Shin tana da wata k'imar da zai sa Anwar ya dawo da ita gidanshi ne? Kai bazai ma yiwu ba, dama Abdallahn ma cewa yayi 'zato' yake yi.
Kira Mamanta ta k'ara kwala mata a tsakar gida a karo na biyu, wanda hakan k'ara firgitata yayi ba kad'an ba. A sanyaye ta fita ta samu guri kan tabarma can nesa da Anwar ta zauna. Ta ce.
"Gani Mama."

MATAR K'ABILA (Completed)Where stories live. Discover now