27

6.9K 449 12
                                    


Tana tsaye a in da take kamar gunki har ya bud'e Fridge d'in ya ciro abunda ta ajiye. Bud'ewa yayi ya gani babu abunda ta ta6a, ajiyewa yayi a kasan carpet da ke tsakiyar falon ya dubeta.
"Zo ki zauna kici." Ya umurceta fuska ba yabo ba fallasa.
"Na k'oshi ne." Ta fad'a tana share hawayen fuskarta.
"Kinsan bana son musu. Oya zauna ki ci tun kafin ranki ya 6aci." Ya zauna a kan kujera yana fuskantarta.
Kallonshi tayi, ya nuna mata k'asa inda ledan yake.
"Ki zauna ki ci."
Dolenta ta zauna ta fara ci, amma sam bata jin dad'inshi a bakinta dalilin yunwan da ta bari ya zama abokin rayuwarta.
Sai da ya ga tana k'ok'arin amai sannan ya barta ta tafi bayan ta kwashe gurin.
Room d'inshi ya koma ya kwanta cike tunanin yanda wannan aure nasu zai kasance.
Tana komawa d'aki ta rufe k'ofar ta shige toilet ta watsa ruwa ta fito, kayan bacci ta d'auko cikin akwatin kayan aurenta ta saka kana ta bi lafiyar gado. Bata ko jima ba bacci 6arawo yayi awon gaba da ita.
    Tun Asuba ta tashi ta yi sallah, tana zaune har gari ya fara haske. Tashi tayi ta shiga kitchen ta had'a musu breakfast, ta dafa Tea mai citta da kanunfari. Akan Centre Table ta ajiye masa nasa, ta jera duk abunda zai buk'ata a gurin ta shiga da nata d'aki ta ajiye. Fitowa tayi ta share gidan duk da babu wani dottin kirki sannan ta shiga wanka ta fito, shiryawa ta yi cikin Atampa riga da zani. Bata yi wani kwalliya ba kasancewar ita ba gwanar kwalliyan bace.
Tana cin abincinta ya shigo da sallamarsa, ajiye spoon d'in hannunta tayi ta amsa sallamar fuskarta a k'asa ta gaisheshi.
Ya amsa da sanyin murya. Ya tambayeta,
"Ya kwanan bak'unta?
"Lafiya." Ta bashi amsa kana yasa kai ya fita.
Sai da yaci breakfast sannan ya tafi gurin aikinshi. Bai dawo ba sai dare k'arfe 9. A inda ta ajiye masa breakfast ta ajiye masa lunch har da dinner d'inshi.
Sai da ya watsa ruwa ya lek'a d'akinta har tayi bacci ya tasheta.
"Ki daina yin lunch da ni, don bazan samu daman dawowa da rana ba." Yana fad'a ya fice ta bishi da kallo, cike da tausayin kanta.
Yinin ranar cikin kewar Iyayenta da kannenta tayi, dad'in abun ma wata mak'ociyarta ta shigo ta tayata hira.
Ta rasa gane wani irin zama za'ayi tsakaninta da yayanta. Watakila ma ba shi yace yana sonta ba Iyayensu suka had'asu aure, saboda gashi an yi auren amma babu wani hali da ya nuna wanda zata ce sonta yake yi. Anya kuwa ba auren dole aka musu ba?
Tagumi kawai ta rafka tana aikin tunani don hawayen ma babu sun k'are.

Haka rayuwar da cigaba da kasance musu har sati uku, basu cika had'uwa ba don tana gama aikace-aikacenta zata shige room d'inta. Shima ya daina zuwa d'akin nata don da ya ganta yake rasa nitsuwarsa ya ji yana buk'atar matarsa.
Ranar da suka cika 3weeks Musa da Surayya suka kawo musu ziyara da dare. Musa na lura da yanayinsu, daga Anwar har Adama sun kasa sakewa ayi hira. Basu jima ba Musa ya ja Anwar waje.
"Me kake yiwa yarinyar nan ne take tsoronka haka? Kaji tsoron Allah Anwar, matarka Amana ce a gunka. Bazan maka dogon bayani ba amma abu d'aya zan fad'a maka, ita ba k'anwarka bace yanzu, ta zama abokiyar rayuwarka, mahad'in jindadi da walwalarka. Kar kayi wasa da damanka."
Yana fad'a ya kira Surayya a waya ta fito tana cewa.
"Zan aiko miki atamfofin ki gani, ko baza ki saya ba ki nuna wa makwabtanki watakila su saya. Ai suna da kyau ga karfi."
"To shikenan." Adama ta fad'a a sanyaye.
Musa girgiza kai yayi. Anwar kuwa ya nuna kamar bai jisu ba.
Wanka yayi ya feshe jikinshi da turare ya nufi d'akin Admy don a yau ya d'au alwashin daidaita zaman aurensu.
K'ofar room d'inta ya bud'e a hankali kamar 6arawo ya kutsa kai ciki. Ko'ina duhu da alama ta dad'e da kwanciya. Wutan d'akin ya kunna wanda ya fallasa surar Adama kwance tana sharar bacci.
Night gown ne dogo mai santsi kalar blue a jikinta. Tsayawa yayi yana k'arewa halittarta kallo zuciyarsa na ingizashi ga kai k'ok'on bararsa gareta.
Firgigit ta farka dalilin hasken da ya dameta, don ita bata son haske a kanta sam in tana bacci.
Tsaye ta ganshi a bakin k'ofa sanye da Singlet da Three Quarter Brown ya zuba mata ido. Sosai ta firgita, kattin idanunta suka yi zuru-zuru kamar wacce tayi k'arya a gaban sarki.
"Yaya wallahi ban san me na maka ba. Kayi hakuri." Tace dashi bakinta har rawa yake yi tsabar tsoro.
"Shhhh." Ya d'aura yatsansa kan lips d'insa.
"Babu abunda kika min. Kuma na hanaki yawan rantsuwa ko."
"Na daina to."
"Tashi kiyi alwala, ki sameni a falo."
Zata yi magana yace,
"Nace bana son musu."

MATAR K'ABILA (Completed)Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang