43

6.8K 534 18
                                    


   Side d'in Adama suka je, amma basu tarar da yaran a nan ba,
  "Ina ga suna can d'akinta." Anwar ya fad'a yana dosan side d'in Sa'adatu, Adama na binshi a baya.
  Kwankwasa suka yi Nana ta bud'e musu da uniform a jikinta, tana bud'ewa ta ruga zata tafi Admy ta kirata tace,
  "Baki iya gaisuwa bane?"
  Daburcewa Nana ta yi don bata gane me Maman nata ke nufi ba. Hakan yasa Admy jin wani irin, tana jin nauyin kasa bawa 'yayanta tarbiyya mai kyau da tayi duk da cewa abunda ya faru bai shafesu ba, asalima basa duniyar.
  "Baki gaishemu ba." Tace da ita tana dafa kafad'unta da murmushi a fuskarta. Sai da ya fara gaishe da Adaman sannan ta dubi babanta tace
  "Abba ina kwana?"
  "Lafiya Angel, kin tashi lafiya?"
  "Abba nine Angel?..." Ta fara tsallen murna.
  "...Abba dama Daddyn Khairat K'awata shima da Angel yake kiranta, kuma nima inason ka dinga kirana da Angel din. Zaka dinga kirana dashi kullum nima sai in fad'awa k'awayena?" Ta karishe maganan tana kamo hannunshi wanda a da bata isa ta yi ba muddin bata yi wanka ba.
  Wannan karon daga Uban har Uwar jikinsu yayi sanyi matuk'a. Admy da take jin hawaye na kokarin taruwa a idonta tayi saurin shiga falon da sallama a bakinta.
  Fitowar Laila da Imam daga d'akin Sa'adatu shi ya bawa Anwar kaucewa Nana ya shigo falon shima, sai dai da ka ganshi kasan he's someone who's guilty.
  Sa'adatu ne ta fito a bayansu tana rike da socks d'in Laila a hannunta. Har k'asa ta durk'usa ta gaishe da Anwar ya amsa yana murmushi. Yace,
  "Ni da nazo shiryasu sai gashi har kin gama."
  Murmushi kawai ta yi ta d'agawa Admy gaisuwa, ta amsa tare da mata godiya ta cewa yaran su gode mata. Daga nan ta jasu suka fita zuwa side d'inta domin suci abinci kafin Abdallah yazo d'aukarsu.
  Suna cin abinci Anwar ya shigo yana rik'e da key d'in mota.
  "Ku gama cin abinci yau ni zan kaiku makaranta." Ya fad'a yana yiwa yaran nasa kallon k'auna.
  Dad'in da suka ji shi ya hanasu cin abincin da kyau, nan da nan suka tashi suka d'auki Bags dinsu da Lunchbox suna ihu yau Abba ne zai kai su skul. Nana har da shafa powder a fuska don yau zata kece raini gaban k'awayenta.
  Admy dad'i ne ya lullu6eta ganin Uba da 'Yayan suma suna k'ok'arin gyarawa alak'ar dake tsakaninsu. Kiran Abdallah yayi yace kar yazo, sannan ya d'aukesu ya kaisu Makaranta.
Kafin ya dawo Adama ta gyara part d'inshi ta share ko'ina, sannan ta dawo nata d'akin ta shiga wanka tana tunanin ya zata fara gyara part d'in nata don wani gurin har wankewa yake buk'ata gefe d'aya kuma tana mamakin yanda zuciyarta a yanzu take son tsafta da gyara daga jiya zuwa yau, sai kace wanda aka switching wani button. Tana wanka Anwar ya dawo, bayan ta fito ta shirya cikin wani Material lace mai kyau d'inkin Fitted gown da yabi jikinta ya mata kyau, tun kwanaki Jamila ta d'inko ta kawo mata amma Adama tana sawa ta cire wai ya matseta bata so. Yau gashi ta saka tana yaba kyawun da ya mata.
Part d'in Anwar ta tafi bayan ta saka zumbulelen hijab, a stairs ta hangoshi yana sauk'owa shima ya shirya cikin k'ananan kayan da suke 6oye yawan shekarunshi.
  Sansanyar murmushi suka aikawa juna kafin ya fara mata kallon tuhuma yana hararanta.
  Ko ba'a fad'a ba tasan me yake nufi, a hankali ta cire hijab d'in jikinta ta ajiye ta nufi dinning table yana binta a baya yana cewa,
   "60, 70, 80, 90." A kowanne juyin hips d'inta.
Sosai kayan ya burgeshi yana godewa Allah da ya bashi mace mai k'irar Admynshi. Ita dai dariya kawai take mishi, a ranta kuma tana jindad'i ganin da gasken daga ita har shi suna k'ok'arin gyara rayuwarsu ba tare da sun kalli baya ba.
  Bayan sun gama cin abinci ta ke cewa,
  "Don Allah inaso kamin izini inje gidanmu anjima. Tun tafiyan Yusuf yaye sau d'aya naje na ganshi."
  Mik'ewa yayi yana d'aura agogo yayi kamar bai ji ta ba, matsoshi tayi ta saka mishi tana Allah-Allah kar ya hanata zuwa.
  Sai da ta gama saka mishi ya fuskanceta ya fara magana cikin sanyin murya,
  "Amma kinsan ina buk'atarki ko? Jiya haka kika jima a toilet har nayi bacci, yau kuma kika kama aiki tun asuba, kuma kina sane yau Sa'adatu zata kar6i girki. Shin har yanzu bana burgeki ne bakya sha'awata? Bakya son kasancewa dani?"
Kafa mata idanunshi yayi yana nazarinta zuciyarsa na masa ba dad'i, gefe guda kuwa wani abu ke fisgarsa har mamakin hakan yake yi sai kace bai ta6a kad'aicewa da mace ba. Dama yayi planning zuwa Plaza ya d'an dubasu ne, sai ya dawo gida ya kwashi gara.
  "Kinyi shiru, har yanzu akwai sauran neman yafiya a gabana kenan. Kiyi hakuri karki zautani." Yace da ita yana jawota jikinshi.
  "Ba haka bane fa. kawai dai..." Ta k'ara yin shiru tana kallon cikin idonshi.
  "To menene? Shikenan ba komai sai kin dawo." Ya saki jikinta yana k'ara yin gaba.
  "Kwana nake son yi fa." Ta fad'a cike da tsokana.
  Anwar da ya k'ulu yace,
  "Kije kiyi sati in kina so." Yana fad'an haka ya juya zai tafi ta rungumeshi ta baya, tsayawa yayi yana murmushi ko ba komai yanzu ta san 6acin ransa har tasan ta rarrasheshi.
  Juyowa tayi gabanshi suna fuskantar juna ta d'an mik'e tsaye ta fad'a mishi abu a kunnenshi da ya sakashi sakin fara'a lokaci guda,  yace,
  "Ina so mana. Zan bi in d'aukeki." Ya fad'a yana d'aukan jakarshi tare da mata winking. Da haka ya tafi bayan ta bashi zazzafan kiss da zai tuna da ita da whole day. Yana fita ta dafe k'irjinta dake racing tana mamakin boldness d'inta kamar wacce aka yiwa wahayinshi.

  Kwanukan da suka ci abinci ta wanke da sauri don bata son abunda zai 6ata mata lokaci. K'arfe 9 dai-dai ta fita daga gidan bayan ta yiwa Sa'adatu sallama, Napep ta tara ta wuce gidansu.

   Tana isa gida ta kwankwasa gate, d'aya daga cikin sojojin da ke gadin gidan ya lek'a kafin ya bud'e mata, tana shigowa suka gaisheta cike da girmamawa kana ta kutsa kai cikin gidan nasu. Sai yanzu take ganin tsari da kyau na ginin gidan wato Gidan Deputy Governor na Bauchi State. Masu aikin da suke kai kawo suka fara kwasar gaisuwa tana amsawa har ta wuce side d'in tar6an baki ta tasamma ainihin part d'in Mahaifiyarta.
  Kamar kullum sai da ta samu wasu mata guda biyu masu kawo kokensu a falon Ummanta, suna ganinta suka d'aga mata gaisuwa ta amsa fuska a sake, da yake ta sansu tun tana budurwa a can unguwar da suka tashi.
  "Umma fa?" Ta tambayesu yayin da take zama kan kujera.
  "Yanzu ta shiga ciki." D'aya daga cikinsu ta bata amsa.
  Umma ce ta fito daga d'akinta Jamila na binta a baya tana danna waya. Ganin Adama zaune a falon yasa Jamila doka tsalle ta je ta ruk'unk'umeta.
  "Ke lafiyarki kuwa? Zaki karyata ne?"
  "Umma ni da Yayata kuma sai a ce kar na rungumeta." Ta fad'a cike da shagwa6a tana kallon Adama da ke murmusawa duk lokacin nan.
  "Kun fi kusa." Cewar Umma tana mik'awa Matan wani babban leda suka yi godiya suka fita.
Anan ta maida hankalinta kansu. Adama ta gaisheta tana lek'a in da zata hango yusuf.
  "Yana can gurin Daddynku, koyaushe a can yake yini a side d'inshi." Cewar Umma sanin me Adaman take tunani.
  "Umma ban ma tambayeshi ba fa." Ta fad'a tana dariya.
  "Nima ban ce kin tambaya ba ai."
  "Adda yau kam kinsa kayan kenan?" Cewar Jamila tana d'aga hijabin Adama.
  Make hannunta Adaman tayi tace,
"Ina wasa dake ne?" Ta saci kallon Ummansu dake murmushi amma wani gefen na zuciyarta na nuna mata canji tattare da 'yarta yau. Komanta neat, ga kayanta da hijabin a wanke a goge, ga takalmi da jaka da ta had'a to match. Rok'an Allah tayi a zuciyarta yasa Adamanta ta dawo hayyacinta ne.
  "Umma, Daddy lafiyanshi kuwa? Naji kince koyaushe Yusuf na gurinshi, baya fita aiki ne?"
  "Lafiyanshi kalau, hutu ya d'auka na 2weeks. Kije ki gaisheshi, ni zan shiga d'aki. Sannan kafin ki tafi akwai maganan da zamu yi."
  Falon Daddy suka nufa, na iyalinshi kad'ai. Sallama suka yi aka amsa musu sannan suka shiga. Yusuf suka hango zaune kan k'afan Daddy suna shan kankana a wani bowl, kowa da fork d'inshi a hannu. Shigowan Adama da Jamila yasashi d'ago kai ya zura musu ido yana kallon Mamanshi, murmushi kawai ya mata yaci gaba da shan kankananshi yana kad'a kai.
  "Adda, Yusuf ya manta dake wallahi." Jamila ta fad'a tana dariya yayinda suke zama kusa da mahaifin nasu da ya zuba musu ido cike da k'auna.
  "Dady ina kwana." Adama ta gaisheshi tana mik'awa Yusuf hannu shi kuma yana k'ara shigewa jikin Kakanshi.
  "Lafiya kalau. Kece da safen nan? Ina sauran yaran?"
  "Suna Skul duka. Wannan sojan nazo d'auka mu tafi gida." Ta fad'a cikin son jin me zai ce.
  "Wannan kam ya zama abokina, anan gidan zaka zauna ko Abokina?"
  Yusuf da bai san me ake yi ba, ya d'aga kai yana kallon Jamila da ta caki kankana da fork d'in Daddy ta kai bakinta. Kwaye fuska yayi, ai kuwa yana ganin kankanan ya shiga bakinta ya fashe da kuka, da sauri Daddy ya kwace fork d'in ya ajiye a gefenshi yana kallon Jamila.
  "Wa yace kisha mishi abunshi?"
  "Na daina." Ta yi sauri fad'a kar ta jawowa kanta lik'i, Waya take son a canja mata tun ba yau ba amma Daddy yak'i yace sai ta gama zana SSCE nata.
  Adama kam sai kallon kyawun da yusuf yayi take yi, kayan da ya saka masu kyau, shadda ce green riga da wando, ga gare har da hula sun yi Anko da Daddy. Yaro kyakkyawa dashi amma sam bata ganin hakan a da can baya.

  "Wa ya d'inka maka kaya mai gare Baby na?" Duk salon tasa ya ganeta yazo gurinta

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.

  "Wa ya d'inka maka kaya mai gare Baby na?" Duk salon tasa ya ganeta yazo gurinta.
  Ko kallonta bai yi ba haka ta gama bidirinta Daddy da Jamila na mata dariya wai ya za6i kakanni kan Mamanshi.
  Basu jima ba suka baro gurin Daddy, suka dawo side na Ummansu, D'akin Jamila ta shiga don making move d'inta na farko.

Mum Fateey👌

MATAR K'ABILA (Completed)Where stories live. Discover now