14

5.9K 440 2
                                    

Maama ta gyara zamanta tace,
  "Wannan haka ne Papa Tujjani, kuma bayan haka su sake dawowa d'aurin aure, ai d'awainiyar zai musu yawa, fatanmu Allah ya basu zaman lafiya ba a kashe kudi a biki sannan aure yaki zama ba."
  "Gaskiyane. Dazu ya kirani yana min bayanin cewa ya gama ginin gidanshi, ya saka mata komai akan ba sai mun wahalar da kanmu ba. Yaron akwai k'okari da zuciyan yi."
  Sallama da akeyi a waje yasa Papa amsawa ya fita cikin gida daga nan kuma bai dawo ba.
  "Aunty Kubrat kinji abun arziki ko?" Cewar Aunty Mansura bayan ta koma kusa da Maama tana murmushin farin ciki.
  Maama itama da murmushi ta amsa mata da cewa,
  "Alhamdulillah sai kici gaba da mata fad'a ta zauna a gidanta lafiya."
  "Muna kan yi Aunty Kubrat, dama kan gyaran jiki da za'a mata nazo muyi magana. Tayi gayyanta duk a wannan satin daga nan bana son ta lek'a ko da k'ofar gida. Zan gyara 'yata ce sosai."
  Daga nan suka cigaba da magana kan bikin har Papa ya shigo aka cigaba dashi.

Sa'adatu na shiga room d'inta ta samu wayarta da ta jona a charge yana ringing, ganin sunan Cherry d'inta yasa ta d'auka had'e da sallama. 
Amsawa yayi yace,
  "Amarsu ina kika shiga? Nayi ta kiranki baki d'auka ba."
  "Sorry dear, naje gidan Aunty Mansura ce, ba dai ka jima kana kira ba? Afwan na sakaka wahala."
  Murmushi mai k'ayatarwa yayi ya shafi k'eyarsa.
  "No baki wahalar dani ba Amarsu, sai dai nayi kewar sweet voice naki."
  "Aww me too Cherry. Ina yarana? Har yanzu ka k'I bani in gaisa dasu."
  "Soon zaku gaisa, yanzu ban koma gida bane."
  "Kullum haka kake fad'a, In dai nazo  zamu had'u dasu. Amma Har yanzu baka koma gida ba? Gaskiya ni dai bazan yadda kana kai har haka a waje ba." Ta fad'a cikin shagwaba.
  Murmushi yayi yace,
  "Idan kinzo sai kiyi k'okarin canjani, zanji dad'in hakan kuwa."
  "Ka shirya kuwa, Sa'adatu zata kasance da kai koyaushe. Zata kuma kasance farin ciki a gareka."

  *BIKI BIDIRI*

Anyi biki lafiya, duk da Anwar ya saka komai kama daga furnitures da kayan kitchen bai hana iyayenta nuna bajintarsu ba suma. Gefen Amarya had'add'en Walima kawai akayi ranar Friday. Saturday kuma aka d'aura aure da safe k'arfe 9, da yake yan Bauchi tun ran Friday suka iso suka sauk'a a hotel.
  Ana d'aura Aure aka d'auki Amarya da tawagarta wanda duka-dukansu mutum 15 ne, a cewar Papa za'a daura musu d'awainiya in mutane sukayi yawa.
Basu isa ba sai bayan isha, gefen Sa'adatu aka bud'e musu suka baje suna huta gajiya suna santin wannan daula da Sa'adatu ta shigo.
  Minti biyar haka aka fara shigo musu da abinci da drinks, wasu suka fara cin abinci wasu kuma suka fara sallah. Amarya dai na can k'uryan d'akinta da k'awayenta uku, idanunta luhu luhu saboda kukan da ta ci.
  Karimatu matar Musa ce ke mata magiya kan taci abinci tayi mata biris.
  "Sa'adatu please kici abinci ko kad'an ne, rabonki da abinci fa tun jiya. So kike ki kashe kanki ne?".
Nan ma dai shirun ta mata, ganin haka yasa Karimatu ta fita palour bata jima ba sai gata da Aunty Mansura. Kallo d'aya tayiwa Sa'adatu ta kar6i plate d'in abincin ta fara d'urawa. Sai da ta cinye Aunty Mansura ta fita tana murmushi.
  Dariya su Karimatu suka saka ana zolayarta.
  "Ashe ma yunwa take ji jorr, duk kukan munafurcine gobe Iwar haka ta manta da su Maama." Cewar Maryam tana cire sark'a da d'an kunnenta.
   Saddik'a ta kar6e,
  "To wai meye amfanin kukan tunda gidan masoyinka aka kawo ka kuma da yardarka, nifa bazan yi kuka ba in aurena yazo."
Harara Sa'adatu ta mata tace,
  "Ai ke kam Saddik'a babu wanda zai kai ki kuka, Ghana fa zaki zauna, you are leaving the country self."
  "So what? In dai gurin Amadou za'a kaini ki bar guzurin hanky, saboda idanuna ko ruwa baza su tara ba."
  Karimatu zata fara magana wayarta ta fara ringing, ta d'auka bayan ta saisaita muryanta.
  "Darling..." magana aka fad'a mata ta lumshe ido ta bud'e tace
  "Gani nan fitowa."
A ta bayan part d'in Anwar ta had'u da mijinnata suka rungumi juna.
Gyaran muryan Anwar yayi ta saki Musa tana gyara gyalenta, shi kuma gogan nata ko a jikinshi. Hararan wasa ta aika mishi sannan ya ankara yace,
  "I miss you ne."
  "Whatever." Cewar Anwar bayan ya matso kusa da su.
  "Ina Amaryata?" Ya tambayi Karimatu.
  "Tana can tana kuka, da kyar ma taci abinci sai da Aunty Mansura ta tsaya a kanta tukun."
  "Har yanzu tana kukan?" Ya k'ara tambayanta fuskarsa cike da damuwa.
  "A'a tayi shiru yanzu kam. Sai kuma na gobe." Ta bashi amsa cikin zolaya.
  "Baza tayi ba, ki snapping min ita a picture ki turo min please."
  "Kai baza ka wahalar min da mata haka siddan ba. Baby muje gida ki huta."
  "Please Karimatu."
Anwar ya rok'eta ba tare da ya kula Musa ba. Dariya tayi tace,
  "To Angon Sa'adatu."

  Ta kalli Musa bayan Anwar ya basu guri tace,
  "Honey yau fa a gida zaka kwana tunda tafiyan nan da kai muka yi, ni kuma anan zan kwana cikin tawagar Amarya."
  Bai yarda ba sai da ta masa lissafi ya gane cewa yau a d'akin uwargidansa yake. Haka suka rabu zuciyarsa bata so ba.
  Tana shiga kuwa ta d'auki Sa'adatu a hoto kamar yanda ta yiwa Anwar alk'awari.
  Yana can palourn shi da musa yaji k'arar shigowan abu a wayarsa ya bud'e.

MATAR K'ABILA (Completed)Where stories live. Discover now