02

9.2K 619 21
                                    


Washe gari da yake saturday ne har taran safe Nazifa bata fito tayi karyawa ba, wanda haka halinta yake, muddin tayi fad'a da miji bata girki saboda tasan bata da 'ya'ya a gidan balle yini da yunwa.

Adama ne zaune a d'akinta tana aikin tunani, yaranta suka banko k'ofa suka shigo jikinsu duk zarnin fitsari suna ta watsa hamma.
Babbar cikinsu mai shekaru 7 mai suna Nanah tace,
"Mama muna jin yunwa, kuma Aunty bata girka ba, da na buga mata k'ofa tace zataci ubana".           Kallonsu takeyi d'aya bayan d'aya kana ta kalli Nanah tace
"Kun wanke fuskarku ne? (Bata ambaci alwala ba balle sallah don har yau tunaninta bai bata cewa ya kamata 'yayanta suna sallah ba).
Mai bin Nanah, Laila'yar 6yrs tace
"Mukam munyi, Imam ne baiyi ba".
kallon Imam d'in tayi yaro d'an kyakkyawa amma rashin kula ya maida shi soko-soko, he's 4yrs old tace
"Kaje ka wanke bakinka kafin nan na gama muku abinci".
Mak'e kafad'a yayi alamar a'a yana tura baki, Adama tace
"Kai ka sani d'an kaniya k'azami kawai, duk sai zarnin fitsari kukeyi".
Nanah ce ta fara fita don jajjaga tarugu da albasa a dafa musu taliya.

A gurguje Adama ta gama dafa taliyar don irin ihun da Imam ke mata wai yunwa yake ji. Ta Baza musu a tray kana ta d'auko marfin tukunya tana fifita musu dashi don yayi sanyi. Lokaci-lokaci tana zaro sili d'aya tana bawa Yusuf wanda ke kan cinyarta, hancinshi dumu-dumu da majina kuma har lokacin bata cire masa pampers d'in daya kwana dashi ba. (ALLAH sarki yaro).
Tun kafin ta musu magana suka hau ci hannu baka hannu kwarya ba ko Bismillah.
A haka Anwar ya fito daga falonshi cikin shirin fita gurin aiki. Shadda ce bugaggiya a jikinshi army green half jumpa. Takalminshi cover kirar Davina black, sai agogonshi Rolex. Babu hula a kanshi hakan yasa gashin kanshi da ya yiwa lowcut shining.
Hannunshi rik'e da jakar laptop d'inshi da phones d'inshi a hannunshi.

Anwar Muhammad Bankudi kenan magidanci d'an shekara 37, saidai yanayin jikinshi zai sa ka bashi 30. Yanada rufin asiri , don plaza yake dashi mai hawa uku, inda ake siyar da komai da komai na rayuwa. Kama daga kayan abinci, furniture, tufafi na all gender, kitchen utensils harda building materials duk cikin *A.M Bankudi Plaza* kuma anan office d'inshi yake inda yake k'addamar da duk harkokinshi harda kwangilar da yake yawan samu daga baffansa Umar Bankudi Deputy Governor.
Wankan tarwad'a ne mai kyau ma'abocin kwarjini da kamala. Yanada faran-faran ga jama'a amma baya son raini ko kad'an.

Iyayenshi Mutanen jos ne inda zama ya dawo dasu bauchi a nasarawa jahun. Babanshi retired lecturer ne a ATBU ta fannin islamic studies. Dattijo ne mai mutunci da ilimi. Matansa biyu Hajia Hauwa da Hajia Amina. Hajia Hauwa uwargidansa tanada 'yaya hudu Nafisa ce babba wacce take aure anan bauchi da 'yayanta 6, sai Saifullah yana aiki a jos tareda matarsa da 'yayansu 3. Sai Anwar da yake binsa mai mata biyu da 'ya'ya 4. Sai autansu Nuhu wanda shima anan bauchin yake zaune da matarsa da dansu daya. Hajia Amina yayanta biyu Fareeda da Abdallah shekara shida da suka wuce Allah ya mata rasuwa sakamakon had'arin mota da tayi a hanyarta na zuwa ziyaran iyayenta, wanda suke sokoto. Anan zaman Fareeda da Abdallah ya dawo hannun Hajia Hauwa kuma take rik'e dasu tsakaninta da Allah. A yanzu haka bikin Fareeda ya k'arato don an mata baiko.

Da gudu yaran suka tashi da niyyan rungumeshi ya dakatar dasu ta hanyar musu tsawa
"Ku tsaya!"
Lailah uwar tsoro ta fashe da kuka yayin da Nanah kuma ta kwashe da dariya harda fad'uwa tace
"Maganinku an fad'a muku Abba yana son a ta6ashi ne?"
Adama da take gefe taji haushin abunda uban nasu ya musu bata la'akari da daud'an dake jikin 'yayanta.
Duk da baya son tsawan da yake yiwa yaran nasa amma ba yanda ya iya, uwarsu ce ta jawo musu da take barinsu cikin k'azanta. A hankali tace
"Ina kwana?"
Sama-sama ya amsa yace,
"Akwai abunda ya k'are na amfanin gida ne?"
Kafin ta bashi amsa ya zarewa Laila ido yace
"Keep quit".
Nan da nan ta had'iye kukanta yace
"Bakwa ganin jikinku da dotti ne? Kuna son 6ata mini riga ne? Kalli fa riganki duk manja, and you...."
Ya nuna Imam da ya koma cin abincinsa ya cigaba
"Ka bar lashe-lashen nan, in bai isheka bane a k'ara maka".

MATAR K'ABILA (Completed)Where stories live. Discover now