42

6.4K 868 75
                                    


"Admy kukan nan naki na d'aga mini hankali, ki bar kukan ki fad'a mini laifin da na miki, wallahi zan baki hakuri kuma zan d'auki laifina, Kinji?"
A sannu ta rage sautin kukanta tana jin wani ni'imantaccen sanyi na ratsa duk tsika ta jikinta.
D'ago kanta yayi yana share mata hawayen da suka 6ata mata fuska da yatsun hannunshi yana cewa,
"Ina sauraronki Admy, idan har nike da kaso na canjawarki na miki alk'awarin hukunta kaina har sai kinji tausayina kin dakatar da ni. Har cikin zuciyata nake kuka da kukanki, nake farin ciki da taki farin cikin. Ki tausayawa Anwar ki bashi damar ruguje rayuwar da kuka yi a baya ku d'ora sabuwa mai yalwar farin ciki da nishad'i. Ina sonki Admy ina matuk'ar k'aunarki. Babu macen da take da kaso mafi yawa na soyayyata da k'aunata sama dake. Ki yarda dani Ina sonki har yanzu ke din jinina ce. Please give me another chance."
Komawa tayi kan k'irjinshi cike da jindad'in kalamansa, sosai zuciyarta ta wanku da dottin bak'in cikin da ta kwasa shekara da shekaru, jin kanta take tamkar sabuwar halittar da aka gabatar a yanzu. Me kuma take nema? Meyasa zata tuno da abunda zai k'ara jawo kace-nace tsakaninsu? Meyasa zata fad'a mishi maganar da zata sa yayi feeling guilty bayan d'umbin k'aunar da ya fallasa a gareta? Duk da cewa a baya yaci fuskarta gaban abokinshi, bai kamata ta rik'eshi a ranta har tsawon shekarun nan tana azabtar da ruhinsu ba. Duk laifin da ya aikata gareta ta shafeshi ta d'ora nannauyan soyayyar da yake mata a gurbinshi. Baza taso a koma baya ba, domin ita kad'ai tasan yanda rayuwarta ta kasance cikinta.
Ganin ta dulmiya kogin tunani yasa ya matsa yatsunta har sai da ta yi k'ara.
"Washhh hannuna." Ta yi saurin matsawa daga jikinshi tana yarfe hannu.
Da sauri ya jawota yana duba hannun, yana cewa,
"Kiyi hakuri, wallahi a hankali na miki fa, bansan zaki ji zafi ba, i'm sorry."
Janye hannunta tayi tana murmusawa kada'an tana share sauran hawayen fuskarta, ya d'ago fuskarshi da ke nuna damuwa yana kallonta,
"Baki ji zafi ba?"
"Ban ji ba."
K'ara rungumeta yayi yana jin kamar wannan ne karo na farko da yayi hakan a gareta, yana kuma jin kamar za'a rabashi da ita. Bai k'i a ce sun dauwama a jikin juna kamar haka ba, ya so a ce ita kad'ai gareshi ya nuna mata soyayyar da ta rasa a shekarun baya.
"Kinyi shiru, baki ce mini komai ba." Yace da ita yayin da suke zama kan d'aya daga cikin kujerun da ke falon k'asa.
Kallonshi ta yi ido cikin ido tana jin soyayyarshi na hauhawa yana ninkuwa a zuciyarta.
"In nemi wata alfarma a gunka?"
"Koma menene ki tambaya, nd i promise you muddin bai kauce addini ba zan miki Matata." Ya fad'a yana rik'o tausasan hannayenta cikin nashi cike da tabbacin aikata duk abunda ta buk'ata.
"Kar ka tambayeni abunda ya riga ya wuce, kar ka tuna abunda na aikata gareka marasa dad'i, kayi hakuri da yanda ka sameni, sannan kar ka min gorin abunda ban iya ba. Kaji?" Ta fad'a hawaye na taruwa a idonta suna gangarowa kan kumatunta da suka gaji da bak'uncinsu.
Rungumeta yayi cike da tausayi yana jin takaicin abubuwan da ya sha mata for all these years don ya saka mata kishi a ranta.
Shin yana sonta kamar yanda yake ik'irari kuwa? Anya bai cuceta da yawa ba? Alhakinta zai barshi kuwa?
"Adama ki gafarceni kan abubuwan da na miki, ki yafe min ko zan samu sauk'i a zuciyata, ina jin tsoron kar cutar da ke da nayi ya Allah ya kamani. I'm sorry, i'm so sorry ki yafemin Adama."
"Ya isa haka, na yafe maka kaima ka yafemin."
"Baki ta6a mini musu ba, baki ta6a fad'a min magana mara dad'i ba, baki ta6a tsallake umarnina ba. To me zan yafe miki akai? Babu abunda kika min, ko da akwai ban sani ba, ni Anwar na yafe miki." Ya fad'a yana k'ara matseta a jikinshi.
Ta jima kwance a jikinshi tana zubar da hawaye wanda tamkar tafiya suke da duk bak'in cikinta, har sai da hawayen suka daina zuba dalilin bata da abunda zata kokawa a yanzu.
Tashi ta yi tana kallon fuskarshi da kumburarren idonta da yayi d'an jaa tsabar kuka. tace,
"Ya, me ya sami idonka?" Ganin shima kamar hawayen yake yi.
"Ni ba yayanki bane." Yace yana k'okarin kauda zancen.
"Idonka yayi ja, abu ne ya fad'a ciki?"
"Inaga k'asa ne ya fad'a, hure min."
Da hanzarinta ta mik'e daga jikinsa ta zauna ta talla6o fuskarsa zata hure mishi idon.
Bata yi aune ba sai jin bakinshi tayi cikin nata yana gigitar da tunaninta. Mutsu-mutsu ta fara tana neman kwace jikinta don bai kamata ta k'ara barin hancinshi ya shak'i tsamin da yake kuka a kanshi ba. Da kyar ta samu 'yancin lips d'inta ta mik'e tana mishi gwaliyo ta haura sama da gudu.
Murmushi yayi ya tashi ya kulle k'ofar shiga falon ya d'auki waya ya kira Sa'adatu.
"Ki kula min da yarana, Mamansu zata kwana a part d'ina." Yace da ita bayan ta d'auki wayan.
"To Habibi. Good night." Tace dashi tana dariya.
"Good night Dear."
Da haka ya kashe wayar ya haura sama don tarar da Uwargidanshi Farin cikinshi.
Motsin da yaji a toilet shi ya tabbatar mishi da wanka take yi. Zuwa yayi da niyyar bud'ewa ya ji k'ofar a kulle, murmushi yayi ya fita daga d'akin zuwa wani d'aki da ke gefenshi wanda a da yake mallakin Nazifa, anan yayi wanka ya fito.
D'akin ya koma ya tarar har lokacin bata fito ba, zuwa yayi bakin toilet d'in ya fara kwankwasawa.
"Hayateeh baza ki fito bane? To ki bud'emin in tayaki wankan." Ya fad'a yana murd'a handle d'in k'ofar duk da yasan ba bud'uwa zai yi ba.
Gyaran murya ta yi alamar ta jishi amma baza ta bud'e ba.
"Ina nan ina jiranki ai." Ya fad'a yana dariya ya bar bakin toilet d'in.
Admy dake cikin band'aki wanke kanta ta yi tsaff dama a tsefe yake baya samun wanki balle kitso, hango shaving stick d'inshi tayi ta d'auka tayi amfani dashi, wankanta hud'u tana yi tana gurje jikinta saboda ta cire tsamin da Anwar ya d'au shekaru yana shak'a.
Anwar feshe jikinshi yayi da turare ya sa kayan baccinshi ya hau gado jiran Admynshi. Tun yana kiranta har yayi shiru, can bacci ya d'aukeshi ba tare da ya sani ba. Bai jima da bacci ba Admy ta fito tana tsane kanta da towel da wani a jikinta, ganinshi a kwance yasa ta lalla6a zata watsa masa ruwan kanta sai taga yana bacci. A hankali ta sunkuya tana kallonshi kafin ta koma gaban mirrow tana busar da kanta.
Minti goma da haka ta gama abunda zata yi, sosai take jin dad'in jikinta, iska sai busata yake yi kamar wacce tayi wanka a Kogin Maliya.
Rigarta ta d'auka da niyyar sawa taji yana tsami tayi saurin ajiyewa. Wardrobe d'inshi ta bud'e ta d'auko wata pink long sleeve d'inshi ta saka, sannan ta koma bakin mirrow ta fesa turare ta haura gado bayan ta kashe bedside lamp da ya haskaka d'akin.
Tana kwanciya ya juyo ya rungumeta cikin gigin bacci, itama rungumarsa ta yi tana murmushi har bacci ya d'auketa cike da tunanin yanda zatayi k'okarin zama abar kwatance gurin Mijinta kuma Ruhinta.
  Da asuba shi ya fara farkwa da salati a bakinshi, bai ida ba ya dakata jin Admy a jikinshi ta tukuikuyeshi tana baccinta hankali kwance. Ya kunna bedside lamp yana kallonta yana murmushi, kawar da gashinta da ya rufe mata fuska yayi idanunshi suka sauk'a kan lips d'inta da suke matuk'ar kama da nashi hatta kalarsu wato Dirty pink.
Yatsunshi biyu ya saka ya shafi lips d'in yana jin bak'on yanayi tattare dashi. Juyin da tayi shi ya fallasar da abunda ke k'irjinta da suke zaune tamkar bata ta6a shayarwa ba. Gabad'aya ya shagalgalce da kallonta har ta farka itama ta k'ura mishi ido. Karaf idanunsu suka had'u tare da sakarwa junansu kyakkyawan murmushi mai cike da ma'ana daban-daban.
  Shi ya jasu suka yi sallah tare, bayan sun idar ya fara karatu, ganin haka yasa Admy ficewa daga d'akin ta sauka k'asa don had'a karyawa.
Minti 17 da fitarta shima ya sauk'o daga stairs sanye da wando, babu riga. Kitchen d'in ya shiga ya tsaya daga bakin k'ofa yana kallonta. Har lokacin gari da duhu, amma hakan bai hanashi kallon zubin halittarta ba dalilin hasken wutan lantarki da ke kitchen d'in, sanye take da rigarsa da ya mata yawa amma she look damn sexy, fararen cinyoyinta da suke a bayyane su suka fi k'onashi. A hankali ya taka zuwa gurinta tare da rungumota ta baya yana shinshinanta. Hannunshi ya zagaya kan cikinta ya matseta jikinshi yana sauk'ar da numfashi mai d'umi a ilahirin wuyanta. Admy tuni ta d'auke wuta ta fara k'ok'arin fad'uwa, da sauri ya sungumeta ya fice da ita zuwa falo. Anan labarin ya sha bam-bam don birkita juna suka yi sun mance da girki da aka d'ora. K'aurin abu da suka jiyo shi ya dakatar dasu da abunda suke yi, Admy da sauri ta tashi cike da kunya ta tafi kitchen. Shi kuwa Anwar zamanshi yayi a falon yana maida numfashi don haushin da yaji da girkin ya katse masa jindad'i, jiya ma haka bacci ya kwafsa masa bai aikata abunda yake muradi ba.
Sai da ta gama girkin tasa a kula ta wanke kwanukan da ta 6ata kana ta goge kitchen d'in ta fito da kulolin tare da ajiyewa akan dinning table. Tunda haka yace Sa'adatu take yi itama zata yi, ai In bata manta ba itama ta ta6a kwatanta hakan a rayuwarta.
Gurinshi taje ta zauna tana kallon yanda ya tsareta da ido, tace
"Ina kwana Ruheey." Da murmushi a fuskarta.
"Kika ce me?" Ya tambayeta yana tasowa daga kishingid'an da yayi.
Sauk'ar da kanta ta yi k'asa ta nanata abunda ta fad'a tana jin kanta a sabuwar duniya.
"Sunan ya mini dad'i Hayateey. Ina son sunan." Ya fad'a yana lumshe idanunsa.
Mik'ewa tayi tsaye tana kallonshi. Tace,
"Zan je in tashi yara suyi shirin skul."
"Dama haka kike tashi tun asuba baza ki koma bacci ba? Ya fad'a da mamakinsa.
Murmushi tayi tace,
"Saboda ban ta6a kwana a d'akinka ba shiyasa baka sani ba."
"Kince a daina tuna abunda ya wuce."
"Uhmm. Bari inje."
"Ki d'auko min jallabiyata a d'aki, yau ni zan shirya 'ya'yana.

Ya kuka ji wannan page d'in?
Shin Adamy ta shiryu ko dai akwai sauran aiki?

I am telling you, next chapter zai fi kowanne chapter dadi. Shower me with your comments nd votes dearies.😍😄

Mum Fateey.

MATAR K'ABILA (Completed)Hikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin