37

5.6K 541 47
                                    


"Honey, nace da ka bari naje gurinta, zai fi kyautuwa." Cewar Sa'adatu.
"Duk d'ayane tunda abu guda zaki fad'a." Ya bata amsa.
Da haka ta yi shiru tana tunanin lalle hakan bai dace ba, sai dai babu yanda ta iya, bata isa ta yi musu dashi ba.
Minti biyar bayan haka Adama ta yi sallama ta shigo. Da ka ganta kasan bata da lafiya, hijabi ta saka amma bazai hana ganin k'irjinta da ya cika yayi fam kamar ballon ba. A hankali ta tako ta samu guri kan kujera ta zauna d'an nesa dasu.
"Ina wuni?" Tace da Anwar tana satan kallonshi.
"Me ya sameki Adama? Baki da lafiya ne? Ya watso mata tambaya ba tare da ya amsa gaisuwarta ba.
Shiru ta yi ta kawar da kanta gefe tana wasa da yatsunta.
"Baki ji bane ina miki magana." Ya fad'a wannan karon ranshi a d'an 6ace.
"Zazza6i ne kawai, kuma nasha magani naji sauk'i." Ta bashi amsa.
Yana son tambayanta dalilin cikowar k'irjinta amma yaji ba zai iya ba, kawai ya share yace,
"Dama Sa'adatu ce zata miki godiya kan girki da kike yi damu. Dear, ga Maman Lailah." Ya karishe maganan yana duban Sa'adatu da tun shigowan Adama ta kafeta da ido, tana mamakin kyanta da kuma birkitaccen dressing d'inta. Sai take ganin tun zuwanta bata mata kyakkyawan kallo irin na yanzu ba.
Ta Gaisheta, Adama ta amsa fuska ba yabo ba fallasa don tana tuna maganan Anwar ne, kenan ya kirata ne don kawai Amaryarshi ta mata godiya ko dai akwai wani abun?
"Nagode sosai da hidima, Allah ya saka da Alkhairi ya bar zumunci." Sa'adatu ta fad'a.
"Ameen." Adama ta amsa.
Daga nan suka yi shiru dukaninsu na kusan minti d'aya, ita Adama tana jiran ta ji dalilin kiranta da aka yi, shi kuma Anwar tunaninshi me ya zaunar da ita tunda an yi abunda ya kirata dominshi?
"Shikenan zaki iya tafiya." Ya fad'a a takaice.
Mik'ewa ta yi amma ta kasa d'aga kafanta tana tsaye a gurin.Tunani take yi meyasa ya kirata?
"Ban gane ba, ka kirani baka ce komai ba." Ta ce dashi don ta kasa gaskata abunda kunnenta ya jiyo mata.
D'an kallonta yayi ya basar yace,
"Adama kenan. Nace Sa'adatu ce take son miki godiya shine na kiraki ta miki godiyan. Kin gane yanzu?"
"Akan ita tafi k'arfin zuwa gurin da nake ne?" Ta ji kalmomin sun ku6uce a bakinta hawaye na silalowa kan kuncinta.
Jikinshi ne yayi sanyi haka ma Sa'adatu don tun farko ta nuna mishi hakan bai dace ba amma yaki sauraranta.
"Duk wulakancin da Nazifa take min bai isa ba sai itama ka d'orata kan turban hakan? Shiru-shiru ne laifina? Ko kuma dai don ni k'azama ce?" Ta k'arishe maganan tana jan numfashi sama-sama hawaye na gudu a fuskarta.
Kafin yace wani abu ta fita a falon da sauri tana rik'e da gefen zuciyarta, kai tsaye dakinta ta shiga ta kwanta kan gado.
Kuka take son yi amma ta kasa, so take ta yi kukan da dukkan k'arfinta ko zata ji sanyi a zuciyarta da yake mata zafi yana bugawa tamkar zai tsago ta cikin kirjinta.
"Ya Salam." Ta furta a hankali tana yamutsa hijabin jikinta ta gefen zuciyarta.
Anan komai ya dawo mata sabo fil, tun daga zaginta da kusheta da yayi gaban abokinshi Musa, da aurenshi da Nazifa, har cin mutuncin da Nazifan tasha mata tamkar ita ta haifeta, sannan ga wani na yanzu, duk shi yake nuna musu hanyar wulakantata, shi yake basu lasisin tozartata su rainata. Shine dalilin canjawarta kuma shine kan gaba wajen aibata halin da ta tsinci kanta a ciki.
Shin meyasa ya kasa mata uzuri tun farko? Me yasa ya kasa tuna cewa a da ba haka halinta yake ba?.
Sai a lokacin kuka mai k'arfi ya kwace mata.
"Menene laifina? Me na maka Anwar? Me na maka kake cusa min bakin ciki? Why? Why me? Ka fad'a min." Haka ta yi ta sambatu tana kuka tamkar ranta zai fita.

"You hurt her." Sa'adatu ta fad'a bayan Adama ta fita, fuskarta d'auke da damuwa.
"You hurt her feelings Habi...." Bata karisa ba ya katseta.
"Ya isa haka." Yana fadan hakan ya tashi ya haura upstairs d'akinshi.
A gaban mirrow ya zauna ya dafe kanshi da hannayenshi yana jin zafi a ranshi. Yau Adama ce ta yi magana? Menene laifi a ciki don ya ce ta zo?
Mik'ewa yayi ya fara safa da marwa a d'akin, ya ma rasa meke mishi dad'i. Shigowar Sa'adatu yasashi zama akan gado ya sunkuyar da kanshi.
Kusa dashi ta zauna jikinta na gugan nashi, hannunta d'aya a k'eyarshi tana shafawa a hankali zuwa saman kanshi.
"To me laifina?"
"Shhhh." Ta katseshi tare da manna bakinta kan nashi.
Da haka ta mantar dashi damuwarshi suka luluk'a duniyar Ma'aurata.

Nazifa tunda ta tashi karfe hudu na rana ta k'i fita ko'ina, tana nan ciki tana tunanin yaya zata fita gurinsu Hamdy ba tare da Anwar ya kamata ba? Hak'uri ta bawa kanta cewa ta bari sai komai ya lafa sai ta nemi izinin fita unguwa, ta nan sai ta je gurin nasu.

Adama ta dad'e tana kuka kafin baccin wahala ya saceta anan in da take. Bata jima da baccin ba ta farka dalilin zazza6i da ciwon kai da suka dirar mata lokaci guda. A haka ta rarrafa neman magani a dakinta amma haka ta gama nema bata samu ba. Da kyar take bud'e idonta dalilin nauyi da kanta ya mata, ga kirjinta da ya ciko yana mata zafi dalilin yaye Yusuf da tayi. Ta Kwanta tana karatun Al'qurani a hankali har bacci ya k'ara d'aukanta.

Maman Fateey👌🏽

MATAR K'ABILA (Completed)Where stories live. Discover now