28

6.3K 419 5
                                    


NAZIFA 'Ya ce ga k'anwar Marigayiya Hajia Amina, Matar Baban Anwar na biyu. Mahaifinta ya rasu tun suna yara, ya bar mata biyu da 'yaya 10. Nazifa ce 'ya ta hud'u a gidan.
Ta taso cikin wata irin rayuwa da babu kwa6a, ba girmama na gaba, sanna ba karatun Boko da Arabi.
Tun rasuwar mahaifinsu Iyayensu mata ke d'awainiya dasu ta hanyar d'aurawa manya talla, su kunu, goro, kayan miya, robobi har da su kayan kwalam da ake kaiwa yara makaranta.
Da safe mahaifiyarta na suyan k'osai a k'ofar gida, ita kuma Nazifa tana dama kunun koko da gyada. Da rana kuma zasu yi shinkafa da mai da yaji da d'anwake har da ruwan lemo. Sai dare kuma k'anwarta Ma'u tayi doya da awara. Suna ciniki sosai, anan suke samun na abincinsu, suturarsu da rashin lafiyarsu.
Nazifa ta tsani rayuwar da take ciki, shiyasa ta d'au alwashin komai rintsi sai ta auri mai kud'I itama ta huta a rayuwarta.
Zainab (Zee) k'awarta ce tun suna yara. Tare suke zuwa talla da Mahifiyarta ke d'aura mata itama. Mahifiyarta babu sana'ar da bata yi har da maganin mata, domin a nan Zee tayi gado. Duk neman kud'insu basa godewa Allah kuma kud'in ba ya ta6a taruwa.
Zee ita ta k'ara koyawa Nazifa son kud'i, wanda har ta kai suna bin d'akin samari a shashshafasu a biyasu. Sai dai Nazifa duk iskancinta a shafe-shafen yake tsayawa saboda tana son duk wanda ya aureta yana ganin darajarta. Ita kuma Zee har kwana da samarin take yi, kuma mahaifiyarta na sane da abunda take aikatawa amma son Naira ya hanata kwa6an 'yarta, a cewarta Barewa baza tayi gudu d'anta yayi rarrafe ba, don har yau Zee bata ma san waye mahaifinta ba.
Mahaifiyar Nazifa da 'yayanta basu yi zumunci da Marigayiya Hajiya Amina sosai ba, dalilin Hajiya Amina tana zagewa ta nuna musu laifinsu na rashin tarbiyya da kuma mugun son kud'i da suka saka a gaba. Lokacin da ta rasu cewa suka yi Allah ne ya kar6i addu'arsu.
Fareeda da Abdallah na son zumunci dasu, dalilin Mahaifiyar Nazifa ita kad'aice wacce take uwa d'aya uba d'aya da Mahaifiyarsu. Suna yawan zuwa sokoto ziyara gurin dangi, su Nazifa tun suna nuna musu bak'in hali har suka hak'ura suka daina, ganin wacce ake yi a kanta ma bata doron k'asa, sannan su Fareeda basa saka musu ido a rayuwarsu.
Akwai wani Business Trip da Anwar zai yi zuwa Sokoto, ya biya gidansu don musu sallama ya tarar su Fareeda na rok'an Baba ya barsu su je hutu. Baba ba wai baya son zuwan nasu bane sai dai yana jimamin gidan da zasu zauna, sanin rashin tarbiyyan yaran gidan. Yana tsoro kar 'yayansa su yi koyi da gur6atattun halayensu.
Shigowan Anwar yasa suka fita bayan sun gaisheshi fuska a kwaye. Anan Anwar ke tambayan Baba dalili, Baba ya fad'a masa Sokoto suke son zuwa amma shi baya son suna yawan zuwa kar su kwaso irin halinsu. Anwar ne ya rok'I alfarmar a bari ya tafi dasu tunda kwana hud'u zai yi sai su dawo tare.
Hakan kuwa aka yi. Bayan isansu ya k'ara jaddada musu cewa su shirya ranar Wednesday zai zo d'aukarsu. Sun ji dad'I sosai duk da cewa basu samu yanda suke so ba.
Suna cire akwatinsu a booth Nazifa ta dawo daga kasuwa.
Rungumarta suka yi itama ta biye musu tana dariya, don tun daga nesa ta hango dalleliyar mota a k'ofar gidansu. Abdallah ne ya nuna Anwar yana cewa.
"Ga Yaya Anwar, shine kad'ai baki sani ba. Don lokacin rasuwar Mamanmu baya k'asar nan, yana Jami'a."
'Jami'a' ta nanata a ranta, Tana kallon motar da suka zo da ita zuciyarta na dukan shida-shida. Tab! Lalle baza ta bari wannan gayen ya ku6uce mata ba ko da mata hud'u gareshi.
Shi kuwa Anwar duk abunda suke yi baya ma jinsu, waya yake yi da mutumin da zasu had'u. Yana gamawa ya juyo yana kallonsu.
Nazifa ta russuna ta gaisheshi tana k'ara yabawa da tsarin halittarsa. Sama-sama ya amsa don ransa ya 6aci da kallon k'urillan da take masa.
Ya kira su Fareeda gefe yana kashe musu warning kar su kuskura su d'auki wani sabon hali wai don sun ga basa gida. Alk'awari suka masa cewa baza su yi ba, sannan ya ciro 5k ya basu.
Ashe maganan da suke yi har Nazifa ta runtuma da gudu ta fad'a 'yan gidan ga su Abdallah da Yayansu sun zo a babbar mota. Nan da nan suka kimtsa da yake gidan baya rabo da shara dalilin sana'ar abinci da suke yi.
Komawanta waje ta tarar har yana k'okarin tayar da mota, su Farida na d'aga mishi hannu. Da sauri ta isa gefenshi ta kwankwasa glass d'in motar. Da mamaki ya bud'e yana kallonta.
"Inna ce tace ka shiga ku gaisa tunda baka ta6a zuwa ba." Ta fad'a tana hura k'aton hancinta alamar tayi gudu.
To, Kawai yace.
Kamar bazai je ba amma ya fito ganin cewa Mamansu ce ta masa iso.
Suna gaba yana binsu a baya har suka shiga gidan. A tabarmar da aka shimfid'a masa ya zauna. Bayan sun gaisa da fara'arsa ya musu sallama ya fita. Sosai tsaftar gidan ta burgeshi. Ko'ina tass, gashi daga uwar har yaran tsaf-tsaf dasu.
Har bakin mota Nazifa ta masa rakiya ya tafi tana d'aga masa hannu.
Tsaki ya ja bayan ya daina ganinta don kwata-kwata yarinyar haushi ta bashi.
Nazifa Irin matan nan ne 'yan firit kamar yara amma fuskar shekarunsu garesu. Bata da tsayi ba k'iba, sai cikar k'irji kaman su ja ta k'asa. Round face gareta mai d'auke da k'ananun ido Sexy, tana da k'aramin baki dai-dai misali, sai dai k'aton hancinta ne ya mata cikas. Tana da tsafta ga son kwalliya da ado, don harkarsu ta sayar da abinci da shiga d'akin samari dole sai da tsafta.
Kamar yanda Anwar ya musu alk'awari ranar Wednesday ya zo d'aukarsu misalin k'arfe tara na safe. Sosai ya kad'u ganin da Nazifa za'ayi tafiyar.
Ita kuwa Nazifa da wayo da dabara ta tambayi su Farida rayuwar Anwar. Kaf tarihinsa suka bata labari har da yanayin zamansa da Adama 'yar Baffansu.
Sai da ta gama jin komai ta samu Zee don yin shawara. Shawarar itace Nazifa zata bisu Bauchi, baza ta dawo ba sai ta samu gurbi a zuciyar Anwar. Ko da ta samu mahaifiyarta da maganan cewa tayi 'in kin gaji da zama zaki dawo, Allah ya baki sa'a.'
A cikin mota tana gaba ita da Anwar su Abdallah na baya. Jin labarin rayuwarsa yasa ta koyi nitsuwar dole, kunya da kuma girmama manya.
A hanya shiru kake ji in banda sautin karatun Al-kur'ani da yake tashi a hankali. Anwar na lura da ita duk da bai nuna alamar hakan ba. Farko yanda tayi dressing gwanin burgewa, lace ne mai saukin kud'I riga da zani a jikinta, sai hijabinta har kusan guiwanta. K'amshin turarenta mai sanyin k'amshi shi yake ta shak'a tun da aka fara tafiyar. Tunawa yayi rabon da yaji k'amshi mai sanyaya zuciya a jikin Adama tun tana Amarya.
Har aka iso magananta bai fi a k'irga ba, nan ma dasu Fareeda take yi.
A gidansu aka fara ajiyesu, Nazifa ta russuna tana masa godiya. Abunka da mai son girma, murmushi yayi yace ba komai, don haushinta da yake ji 70% ya ragu a 'yar tafiyar da suka yi.
Zamanta a gidan su Anwar zama ne na takura a gurin Nazifa, don ba yawace-yawace ba zaryan d'akin samari da 6arin tarbiyya. Aikin gidan kaf ta d'aukewa Mama (mahaifiyar Anwar).
Mama tun tana d'ari-d'ari da ita har ta daina, tana kyautata zaton Nazifa tana da hankali sa6anin yanda suke tunani.
Ana kwananta hudu da zuwa, ran sunday tace wa Fareeda ta tambaya musu Mama zasu je gidan Anwar. Tun daga k'ofar gidan ta rainawa matar Anwar wayo. Suna shiga suka fara cin karo da kwandon shara ya cika mak'il, ga k'udaje na bi suna wak'ok'insu.
A yanda suka sami cikin gidan da d'akinta ba'a magana. Ga yaranta uku sai kiriniya suke yi cikin dotti, da alama ko wanka bata musu ba tun safe.
Kyakkyawan tar6a Adama ta musu tana kallon Nazifa kaman ta ta6a ganinta a wani guri. Fareeda ne ta fad'a mata dangantakar da ke tsakaninsu sannan Adama ta tuna ashe a sokoto ta ganta lokacin rasuwar Hajiya Amina.
Bayan sun ci abincin rana, Nazifa ta tattara in da suka ci abincin ta gyara. Daga nan ta tsiri shara da goge-goge na gidan. Ciki da waje ta bi lungu-da-sak'o ta fitar da shara ta bawa almajiri ya kai bola. Adama kuwa tun tana 'ki bari Nazifa, kar in sakaki d'awainiya' har ta hakura ta barta don taga abun nata bana k'arewa bane.
Adama ta ji d'aci a ranta don ta tabbata Nazifa ta rainawa tsaftarta ce, sai dai bata nuna a fuskarta ba, don ko ba komai ta gyara mata gida.
Bayan la'asar suka yi haraman tafiya Adama tace su bari mana zuwa anjima da yamma su tafi tunda tsakaninsu da gidan ba nisa sosai.
Suna zaune har yamma Anwar ya dawo kamar yanda ya saba. Don tun lokacin da ya fara Kasuwanci yake dawowa gida da wuri, sai dai da yayi wanka zai fice don ya tsani ganin gidan da k'azanta, daga nan kuma ba zai dawo ba sai 9 na dare watarana har goma. Yaci abinci ya bita d'akinta ya kirata in yana da buk'atarta.
Daga k'ofar gida ya fara ganin sauyi, yana shiga gidan sai da yayi mutuwar tsaye, don ya dad'e bai ga gidanshi clean haka ba. Har wani iska ne sassanya yake busowa yana shiga jikinshi. Lumshe ido yayi ya bud'e yana jindad'in sauyin da aka samu. Yana kyautata zaton Admy ne tayi aikin don itama ta gaji da zama cikin dotti.
Da sallama ya isa falo ya d'aga labule ya shiga. Nazifa ya gani tana shafawa 'yayansa man shafawa sai tsalle-tsalle suke yi tana dariya.
Bin falon yayi da kallo yaga shima an gyarashi har an canja tsarinshi.
Amsa sallamarsa Nazifa tayi tana wani sunkuyar da kai ita mai kunya. Har k'asa ta tsuguna ta gaisheshi, ya amsa cikin fara'a kana ya shige d'akinsa yana alawadai da idanunsa da suke kai kansu k'irjin Nazifa. Rigan da ta saka irin mai V-Shape d'innan ne, wanda yayi sanadiyyar bayyana wani shashe na kirjinta.
Tana ganin ya shiga ta sauk'e ajiyar zuciya, don taga da alama ta fara ciyo kanshi.
Bayan Anwar yayi wanka ya fito falo ya tarar su Nazifa na yiwa Adama sallama, tana cewa su bari sai sunci abinci. Sallama suka mishi shima suka tafi.
Sai anan Anwar ya kai dubanshi kan Adama yana ganin wawan dressing d'inta, da sauri ya d'auke kai ya nufi k'ofar fita itama tayi shigewarta kitchen.
Washe gari da ya dawo sai yaga gidan ba kamar jiya ba, gidan babu shara ba kimtsi. Kawai dai an dawo rayuwar baya. Da mamaki ya shiga room d'insa ya fito ya sameta a kitchen.
"Me yasa yau baki share gidan ba?" Ya tambayeta.
"Nayi shara fa, yara ne suke 6atawa." Ta bashi amsa tana 6ata fuska.
"Jiya kuma basu 6ata ba ko?"
Shiru tayi ya matso daf da ita ya kamo kafad'unta idanunshi a kanta.
"Jiya da na shigo gidan nan baki san farin cikin da na shiga ba, ganin ko'ina fes-fes kamar gidan Amarya. A tunanina Admy ce ta dawo normal kamar yanda take a daa. Bari in tambayeki, don Allah gyaran da kika yi jiya ke kanki baki ji dad'I ba? Kuma baki ga gidan ya miki kyau ba? Sannan ki duba ki gani yara ma basu 6ata ko'ina ba, dalilin sun ga ba tarkace. Don Allah ki dawo da gidanmu kamar na jiya, daga ni har ke da yara rayuwarmu zata fi dad'i." Kallonta yake yi kamar wani abun tausayi.
Kanta a k'asa tace,
"Ba nice nayi ba, Nazifa ce tayi share-sharen." Tana fad'an hakan ta bar mishi kitchen d'in.
Jiki a sa6ule ya kama hanya ya fita daga gidan.
Tun daga ranar ya tabbatarwa kanshi sanin cewa Adama baza ta ta6a canjawa ba sai wani ikon Allah. Nazifa tana yawan ziyartarta, kuma duk lokacin da ta je gidan sai Anwar ya gane dalilin canji da zai samu na gyare-gyare.
Tsaftarta, kunyarta, da hankalinta suna burgeshi, sai dai har lokacin bai ta6a nuna mata ba. Suna had'uwa a gidansu idan ya je, yana yawan ganin tana taya Mama aiki. Yarinyar ta shiga ranshi da yanayinta da kuma tsaftarta.
Watan Nazifa Uku a Bauchi tayi haramar komawa gida, don ta tabbatarwa kanta sani cewa ta shiga zuciyar Anwar.
Sosai kowa yayi kewarta a gida, musamman su Fareeda da suka saba sosai.
Anwar bai san ta tafi ba sai da ya jera kwana biyu yana zuwa baya ganinta, anan yake tambayan Fareeda tace masa ta tafi.
Bayan tafiyanta da sati d'aya Anwar na tare da Musa suna hira, wata Sabuwar Number ta kirashi. Bayan ya d'auka ya ji sallama da wata muryan da ya sani. Amsawa yayi suka gaisa. Anan ya gane ko wacece.
"Dama na kiraka ne mu gaisa Yaya Anwar." Nazifa ta fad'a cike da girmamawa.
"Kin kyauta kuwa. Nagode, ya mutan gidannaku?"
"Lafiya lau, sun gaishe ku."
"Muna amsawa."
Ko bai fada ba tasan ya ganeta. Shi kuwa ya ji dad'in kiranshi da tayi, don har cewa yayi me yasa ta tafi babu sallama? Hak'uri ta bashi, kana ya jaddada mata zai yi saving Numbernta ana gaisawa.
Bayan sun yi hanging ne Musa ya dubeshi da alamar tambaya. Anwar yace,
"Yarinyar nan ne da nake baka labari. Cousin d'insu Abdallah."
"Auu, cewa zaka yi wannan yarinyar da take burgeka da tsaftarta."
"Ban san ko ina sonta ko bana sonta ba. Abunda na sani shine muddin ta shigo gidana Adama zata canja halayenta itama ta koyi tsafta." Cewar Anwar.
"Ka nemi za6in Allah Aboki. Insha Allah zan tayaka da addu'a." Musa ya fad'a yana mai dafa kafad'ar abokin nashi.

Bayan sati biyu da haka, Anwar ya je da maganar Nazifa gurin Baba. Baba yayi na'am da zancen ba tare da tunanin komai ba. Don don a iya zamanta a gida ya lura tana da nitsuwa da hankali. Bayan sati da faruwar haka magabatan Anwar suka tafi nema masa auren Nazifa.
Ana aure saura 1month Nazifa ta fara shaye-shayen maganin mata da gyaran jiki. Duk in da taji ana sayar da wani had'edd'e sai ta siya ta sha. Wannan kenan.

Adama tun lokacin da Anwar yazo mata da labarin k'arin auren da zai yi ta rasa hankalinta da nitsuwarta. Babu abun da yafi bak'anta mata rai sai cewa Nazifa zai aura, wacce take zuwa nan gidanta tana ganin sirrinta kuma ta san komai na rayuwarta. Tasha kuka har ta godewa Allah. Anwar kuwa in taga yanda yake wani zumud'I da rawar kai sai taji kamar ta tunkareshi da neman takardar sakinta. Sai dai tasan ko da wasa baza ta iya ba, don abunda zai biyo baya sai ta gwammaci kid'a da karatu.

MATAR K'ABILA (Completed)Where stories live. Discover now