01 Mafarin Rikicin...

24.2K 1K 44
                                    

Mik'ewa tayi tsaye da sauri kamar wacce aka tsikara tana nanata kalmar 'AURE' a ranta. K'irjinta ne yake dukan uku-uku yayin da take jin zuciyarta kamar ana soya mata shi.
Ta dafe Inda yake mata zafi tace
"Inaa!! Sam ba zai yiwu ba! Au.. au... aure zaka k'ara ANWAR? Meyasa? No ba zai ma yiwu ba, dalilin uwar me zai sa ka kara aure?"
Kallonta yake yi cikin nitsuwa yace
"Saboda raya sunnar ma'aiki."
Ta kalli uwargidanta ADAMA wacce tunda aka fad'a musu wannan mummunan sak'on bata d'ago kai ba, bare tayi magana. Cikin takaici Nazifa ta mai da dubanta kan mijin nasu tace
"Duk mu biyu bamu isheka ba? Yanzu fisabilillahi Anwar mu d'in ba raya sunnar kayi damu ba? Ko dadiranka ne mu? Kai wasa ma kake yi, baka da dalilin Kara aure balle har ka ce zaka yi".
Bai ce mata k'ala ba. Cikin tsawa tace
"Ka mini magana mana!"
Nan take hawayen da take dannewa suka fara wanke mata fuska kamar an bude famfo.
Fuskarsa a tsuke yace,
"Ki zauna NAZIFA, kin tsaya a kaina kamar wani dan cikinki, and you know bana son raini Sam."
Harara ta watsa masa, kamar idanunta zasu fito waje kuma a hakan tana hawaye tace
"Bazan zauna ba. Nace bazan zauna ba. In banda rashin godiyar Allah mata biyu basu isheka ba sai ka k'ara kwaso wata jaka.....".
"Enough Nazifa!!!".
Tsawan daya daka mata ne yasa dolenta zama ba shiri, zuciyarta kuma ta tsananta bugu.
Adama da ke gefenta ma sai da ta tsorita don yanda taji tsawar bazata. Yana huci ya nunata da yatsa yace
"Kul!! Kar ki kuskura ki bata min rai".
Kuka ne ya subuce mata, ta tashi da gudu ta fita daga falon maigidan nasu.
Ajiyar zuciya ya sake yana kallon Adama uwargidansa da take kallon bakin k'ofa fuskarta cike da damuwa had'e da tsoro yace
"Zaki iya tafiya".
Sum-sum ta tashi ta fice itama tayi d'akinta.
Hular dake kanshi ya hankade ta cillu gefe guda. Tsaki yaja ya tashi ya shige bedroom d'inshi bayan ya kwashi wayoyinsa.

    Nazifa a d'akinta ta dinga rabzar kuka kamar wacce uwarta ta rasu. Bata tab'a zaton akwai ranar da Anwar zai juya mata baya ba, ada tasan itace 'yar lelenshi amma cikin shekara d'aya daya wuce komai ya tarwatse dalilin matsalar da ta samu kanta ciki.
Bayan kukanta ya lafa ta tashi Jikinta a sanyaye kamar wacce a yiwa duka, ga kanta yana wani irin sarawa kamar zai tsage. A haka ta isa falonta wanda komai yake neat kamar sabuwar amarya. Komai nata a wadace babu dauda.
  K'ofar falonta ta bud'e ta lek'a cikin gidan. As usual ko'ina kaca-kaca da tsummukara, shara, kwanuka da tarkacen kayan amfanin gida, k'ofar kitchen d'insu ta gani a bud'e wanda tasan muddin ya kwana a bude babu mamaki Bera ya shiga ya musu barna. Ko a kwalarta taja k'ofar dakinta Giriffff ta rufe harda saka lock. Tana sane da cewa yau itace tayi girki, ita keda Miji amma kuma bata mance da cewa ko taje d'akinsa bata da amfani a gurinsa ba, sai ma dukansu su kwana da bakin ciki. To me amfanin zuwan?

Adama tana shiga falonta ta tarar da yaranta uku suna cin tuwon dare, ko'ina na falon kaca-kaca, ga warin yajin daddawa da yaran suke k'arawa a miyan ya cika falon bussss.
Ko kallonsu bata yi ba ta shige kuryan d'akinta had'e da saka lock. A hankali ta k'arisa bakin gado wanda bedsheet d'in yaci ubansa da dotti had'e da map din fitsari.
D'anta k'arami d'an wata sha uku ne kwance yana sharar bacci, suntur yake duwawunsa ko pant babu balle Diaper.
Zamanta keda wuya ya farka ya rarrafo gurinta yana cewa "nanna" wato 'nono'.
Jawoshi tayi ta fara bashi nono. Anan idanunta suka ciko da hawaye tayi saurin sharewa, amma ko seconds biyu bata yi da sharewan ba wasu suka zubo, a hankali take kukanta wanda ita kad'ai ta san yanda zuciyarta ke mata zogi hade da k'una.
Tafi minti talatin cikin wannan yanayin na zafin zuciya, ganin yaron yayi bacci yasa ta kwantar dashi. Wardrobe d'inta ta bud'e ta d'auko pampers tazo zata saka masa, sai dai tun kafin ta iso ya tsula mata fitsari a inda yake kwance, jawoshi tayi gefe d'aya tareda lik'a masa pampers d'in ta zura masa y'ar riga.
Ta fita zuwa falonta ta samu yaranta sun gama cin abincin har sun tafi d'akinsu, sai dai anan suka bar mata kwanukan hatta ledan yajin daddawan anan suka bari.
Tsaki tayi ta tattara kwanukan ta fita dasu bakin k'ofar d'akinta ta ajiyesu anan. Kitchen d'insu ta hanga a bud'e, ta fita ta rufe, ta dawo d'akinta shima ta rufe ba tare da ta lek'a yaran nata ba kamar yanda ta saba. Agogon falon take kallo wanda ya nuna 09:47pm.
Zama tayi a d'aya daga cikin kujerun falon wanda colour d'insu brown ne amma don tsabar dotti da fitsarin yara ya koma coffee. Tana zama taji danshi-danshi, wanda ta tabbatarwa kanta fitsari ne, sai dai tana dubawa taga ledan pure water ne da yaran suka sha suka bari ya jik'a kan kujeran. A hankali take k'arewa falon nata kallo.

  Saman ceiling din falonta duk cike yake cobwebs da ya masa mummunan ado ba kyan gani. Jikin gini kuwa zanen pensir da biro ne na sunan 'yayanta har da nata wai 'Adamalle vs Anwar' aikin d'iyarta ta fari.
Duk da oily paint ne bai hana jikin ginin dotti na miya da majina ba. Kayan kallonta duk sunyi k'ura, an watsa wayoyinsu ta ko'ina, kan carpet d'inta shima da yake brown bak'i ya zama ba ma coffee ba.
Lek'a bayan kujeranta tayi ta saka hannu ta dauko wani cup din tea wanda a k'alla yayi sati a gurin bata sani ba. Gefenshi kuma wani gayan tuwo ne daya fara 6aci, kiyashi sun yanyameshi suna d'iban rabon su. Tsaki ta ja tana ayyanawa a ranta gobe zata fitar dashi waje.
  Hakikanin gaskiya Adama ta ciri tuta wajen k'azanta da halin ko in kula. D'akinta ta koma in da shi d'in ma kamar falon yake ko worst. K'ofofin wardrobe d'inta sun fiffita ko'ina ka duba kayane a watse, can kan gadon a gefe kuma kayan sakawanta ne wanda aka wanke, amma sunfi kwana hud'u a gurin an kasa matsar dasu. Ledan su biscuit, chocolates, books d'in yaranta duk a barbaje a k'asa. Ta bakin toilet d'inta kuma poo ne wanda babu mamaki kashi ne a ciki. Touchlight ta haska can k'uryan gadonta ta jawo wani zanin super wax ta shinfid'a a kan fitsarin da yaron ta yayi d'azu ta kwanta. Sheshshekar kuka ta fara a hankali har bacci b'arawo ya saceta bayan ta jima a haka.

K'arfe 11:00 Anwar ya fito daga d'akinsa zuwa tsakar gidan sa, in da sabo ya saba da ganin daud'ar gidansa, amma a kowanne lokaci ya gani zuciyarsa na k'una yana bak'in cikin rashin samun mata masu tsabta.
Ya lek'a ko'ina yana tattara abubuwan da bai kamata su kwana a waje ba yana mayar dasu in da ya kamata a ajiyesu. Bayan ya gama ne ya shiga d'akin yaranshi wanda ke tashin zarnin fitsari,  a hakan ya gyara musu kwanciyarsu tare da rufe musu k'ofa.
Kamar zaiyi kuka tsabar b'acin rai  ya wuce d'akinsa ya zauna akan gado, yana tunanin rayuwar iyalinsa wanda yake ganin kwata-kwata bai yi sa'ar mata ba, samm!
Dukannin su babu na rufin asiri, kowacce da gagarumar matsalarta. Matar da zai aura ne ta fad'o masa a rai, Ajiyar zuciya yayi yana mai fatan shima yayi sa'ar za'be kamar abokinshi kuma makwabcin sa Alhaji Musa.
A hankali ya furta
"Matar K'abila."

MATAR K'ABILA (Completed)Where stories live. Discover now