05

7K 536 31
                                    


Adama ta kalleta galala tace
"Nazifa don za'a miki kishiya sai kice baza kici abinci ba? Anya kin dauki hanyar da zata bullar dake kuwa? Nikam gaskiya bazan d'aukawa kaina wahala irin haka ba. Yanzu watakila tana can tana harkokinta cikin farin ciki ke kuma kin zauna anan kina damuwa kina tayar da hankalinki. Namiji da kike gani in ya tashi yin aurensa baya kallon kowa da gashi, daidaiku ne cikinsu wanda zai zauna yana lallashinki yana lalla6aki. Wasu mazan idan zasu k'ara aure Gani suke matan da suka ajiye ba mata bane sai wacce zasu auro, zai iya take kowa ya zauna lafiya don rawar da kansa ke masa a wannan lokacin. Lokacin da za'a kawo ki wani irin abu ne ban gani ba Nazifa? Da na d'aga hankalina da yanzu an shafe babina. Gaskiya ki canja salo don wannan wahala kawai zaki sha kuma a banza".

Tunda Adama ta fara magana Nazifa ke binta da ido tana auna maganganun a ranta. Tabbas taso tayi shirme!! Don shi Anwar d'in da take k'ok'arin mutuwa a kansa ma bai damu da halin da ta jefa kanta ciki ba dariya na yake mata ya maida ita wata shashasha sakarai mara aikin yi. D'aga ido tayi ya kalli Adama,
"Kuma gaskiyanki Maman Nanah, ni ina ta haukana shi ko gogan da nake fad'i tashi a kan nashi ko a jikinshi, baki San wulakancin da ya mini ba kafin ya fita. Wallahi ji nake zuciyata kamar ta fashe koma in mutu in huta. Wai dama kema haka kika ji da za'a auroni? Tukunna ma me kuka girka ne? Wallahi yunwa nake ji kamar hanjina zasu tsinke".

Abincinsa yake ci cikin nitsuwa don yana son girkin Adama, duk da ma yaci a gidansu bazai bari daddad'an girkinta ya wucesa ba. Waya yake yi da gimbiyar tashi anan yake fad'a mata sak'on Babanshi. Tayi murna kwarai don tana bala'in son Anwar.
Basu jima ba ya katse tare da komawa d'akinshi ya d'auko key d'in mota ya fita, lokacin karfe tara saura mintuna.
A Bauchi Club Suya ya tsaya ya sayi Suya, Anan ya had'a da drinks din da basu dashi ya juyo gida.

D'akin Nazifa ya nufa ya samu ta shiga toilet, da alama taci abinci don ga empty kwano a ajiye a falonta. A kan bedside drawer ya ajiye mata nata kana ya fice yana murmushi a ranshi yace 'WA YA GAYA MIKI BORNO GABAS TAKE?'

Side d'inshi ya shiga yaga babu Adama, kai tsaye ya shiga room d'inta ya sameta har ta kwanta ita da yusuf suna bacci.
Tashinta yayi yace
"Ban gane ba kinzo kin kwanta anan".
"To me zanyi?"
Ta tambayeshi kanta na k'asa. Shiru yayi kana yace
"Kizo ki sameni sai ki gani".
Yana fad'an haka ya fita don yasan dole ta biyo shi.
Zamanshi da minti d'aya kuwa sai gata ta shigo, ta zauna can nesa dashi. Yayi kamar bai ji ta shigo ba ya jawo ledan naman ya fara ci.
Shiru-shiru ganin bata da niyyan zuwa yace
"Kizo mana"
"Na k'oshi"
Ta bashi amsa.
Zuwa yayi inda take ya kamo hannuta suka zauna a k'asa, ya d'auko tsoka d'aya yace
"Ko kici ko in miki d'ure, kuma ko baki ci ba sai kin biyani ladan wahalan siyowa".
Ya k'arishe maganan da murmushi a fuskarsa.
Itama bata san sanda ta murmusa ba can kuma ta tsuke fuska, ganin haka yasa ya d'aura mata naman a la66anta dolenta ta bude bakinta ta kar6a suna ci. Labarin gurin aikinsa yake kawo mata don ya mantar da ita fushin da take ciki ta kuma sake dashi.
Yasan ba hiran soyayya take so ba balle ya mata. A da in ya fara mata kalaman love sai dai kawai ta bishi da "uhmm, hmmm ko 'to me kake so ince? Wani lokaci kuma cewa take yi 'nifa abubuwan nan basa burgeni yanzu' Lalla6ata yake yi don yanzu ita kad'ai ce mai kore mishi k'ishinshi.
Bayan sun gama ne ya jata zuwa aza room, sai dai kamar kullum yau ma tana d'an tashi tashin tsami wanda ya hade da body spray da ta fesa ya bada wani scent mai wuyar fassara, kawai dai yana saka tashin zuciya da hamami.
Tsayawa yayi da abunda yake yi, a kasalance ya dubeta zuciyarsa na k'una,
"Adama wannan wani irin abu ne don Allah? Ke har yanzu baza kiyi wanka mai hankali ba. Haba don Allah!! Sau nawa zan miki magana kan cewa ki dinga bin lungu lungu na jikinki kina wanke wa? Kina abu sai kace ba mace ba, wanka wannan sai an koya miki yanda zakiyi da tarin iliminki da wayewarki? Ki zo muje bathroom, yau ma abunda muka saba shi za'ayi, kuma kar ki kuskura ki bud'e mini baki kice zaki yi kuka".
   Jawota yayi ya cire mata kayanta tsaf kana ya kaita band'aki, hawaye kawai takeyi a zuciyarta kuma ta tsine mishi yafi sau dubu.
Sai da ya wanketa tass yanda yake so kana ya fito da ita zuwa d'aki. Man shafawansa ya shafa mata bayan ya gama tsantsane jikinta da towel. Ya fesa mata body spray duk tana tsaye tana aikin hawaye zuciyarta cunkushe da bak'in ciki, gani take yi duk duniya babu wani nau'in wulakanci da ya kai wannan girma a gurinta.
Kan gadon ya mayar da ita ya cigaba da aikinshi. Bai barta ta huta ba sai da yaji ya biya buk'atarsa. Mirginawa yayi gefe yana maida numfashi kamar wanda yayi tsere.
Adama ta gyara kwanciyarta tana zun6ure-zun6ure, tayi kicin kicin fuskar nan tata a had'e kamar wacce aka aikowa mummunan sak'o.
Hannunshi ya mik'ar da niyyan k'ara jawota ta fashe mishi da kuka, da sauri ya tashi zaune yace
"Menene?"
"Yusuf ya tashi".
Tsaki yaja ya shige toilet.
Tana ganin ya shige ta d'auki zaninta tasa kana ta kwashi sauran kayanta ta fice tana Allah ya saka mata wulakancin da yake mata.
Koda taje d'akinta ma yusuf yana baccinsa da alama ko motsawa ma baiyi ba. Wanka ta shiga don duk lalacin Adama bata ta6a kwana da janaba a kanta, ko kuma ta shayar da yaro ba tare da tayi wankan ba. (Mata da yawa suna yin wannan kuskuren, zama da janaba sam ba abune mai kyau ba don saboda k'azanta ce. Kuma muddin akwai halin gusar da ita, a gusar d'in yafi tsafta, musamman iyaye mata masu shayarwa, ba'a so ki taba koda yatsan yaronki a yayin da kike janaba, idan kuma tilas ne sai kin bashi mama, ko kuma babu ruwan da zaki yi amfani dashi ne, to ana so ki wanke bakin nonon kafin ki bashi ya sha. Wallahu Aalam).

MATAR K'ABILA (Completed)Where stories live. Discover now