44: Sabuwar Rayuwa

7.6K 558 137
                                    


Note: Akwai wasu pictures a k'asa da ba nawa bane. Idan mamallakiyarsu ta nuna rashin amincewa da sakasu da nayi zan cire nan take. Thank you.

Adama cire hijabinta ta yi, ta isa gaban mirrow dake cike da kayan kwalliya kamar na hauka. Wani abun bata ma san amfaninshi ba ko da ta d'auka ta karanta. Man gashi da d'auka tana shafawa kanta Jamila ta shigo d'auke da tray da drinks a kai, kan table din tsakiyar d'akin mai kewaye da kujeru uku ta ajiye kana ta zo bayan Adama tana kallon gashin kanta.
"Yaa Allah! Adda ya aka yi kanki ya zube Haka?"
Jamila ta tambaya tana tattaba gashin.
Kallonta Adama ta yi ta murmusa,
"Jiyan nan kuma na wankeshi, ni kaina da ina drying naga zubewarshi."
"Ke ce ai baki son amfani da mai mai kyau. Da zaki yarda da na kaiki iLubiee spa and saloon. Baki ga yadda suka kware wurin gyaran gashi ba. Gyaran jiki kam ba a cewa komai Allah."
Kallonta Adama ta yi tana murmusawa, kamar ta san abunda ke k'unshe a zuciyarta kenan, illa kunyar tambaya take, dan bata san Jamilan ta d'agota ta tsokaneta.
"Kai haba dan Allah?" Ta fad'a tana k'ara kallonta.
"Allah ba wasa nake ba, idan kin shirya ki tashi muje kafin in canja mind dina."
"Kefa kinji matsalarki, tashi muje da Allah."
Da sauri Adama ta zura Hijabinta ta tsaya kallon Jamila da ke kwashe-kwashe a wani jaka k'arami.
"Baki fad'a min kwana ake yi a gurin ba."
Murmushi kawai Jamila ta yi, ta k'arisa jidan abunda zata buk'ata suka fito. Sallama suka yiwa Umma da ke kitchen tana had'a abincin Daddy.
"Ina zaku je da uwar jaka haka?" Ta tambayesu tana kallon jakar hannun Jamila.
"Umma sai mun dawo zaki gani." Adama ta fad'a da sauri kar Jamila ta kopsa mata.
Sallama suka mata sannan suka fita, Umma kwalawa Jamila kira tayi ta dawo.
"Ki d'auki Credit card d'ina a jaka. Make sure kin saya mata duk abunda ya kamata. Komai Jamila." Umman ta fad'a, jikinta har rawa yake tsabar dad'i.
Da gudu Jamila ta koma ciki ta d'auko har da key na motar Umma, ai ita yau babu wanda ya kaita murna. Sai ta canja rayuwar 'yar uwarta.
A parking space mai d'auke da motoci kala kala ake daru tsakanin Adama da Jamila, Adama tace baza ta shiga driving d'in Jamila ba sai dai driver ya kaisu. Da kyar ta yarda ta shiga bayan Jamila ta kira Daddy ya tabbatarwa Adama cewa ta iya. Can iLubiee Spa suka yi zango.
Yanayin saloon d'in kadai, ya sanya nishadi a zuciyar Adama, ganin yadda ma'aikatan ke aiyukansu cikin kwarewa, shima ya kara jin dadi a zuciyarta.
Da wankin kai aka fara, tana zaune cikin dryer, 'yan mata biyu na tsaye gefe da gefenta, d'aya na yi mata pedicure d'ayar tana manicure. Suna gamawa aka k'arisa gyaran gashin sai shek'i yake yi ya zubo kafad'unta, nan ma a hakan ya zube ba kad'an ba. Tufke gashin aka yi a tsakiyar kanta suka wuce gurin spa.
Tun ba a fara mata dilka da helwa ba, ta fara samun wani wadataccen iska a cikin kanta da kafafunta, dalilin yadda aka gyara akaifunta na hannu, sosai ya birge ta, har tana tunanin ashe dama haka yatsunta ke da masifar kyau?
6angaren spa suka k'arasa, a nan Adama ta sake baki tana kallon ikon Allah. Da charcoal face mask aka fara shafe fuskarta da, kafun aka ci gaba da dilka a sauran sassa na jikinta.
A kalla sai da suka dauki awanni ukku A wurin, sosai Adama ta canja, ta koma wata sabuwar halitta ta daban, fuskarta sai wani sheki take da haske na ban mamaki. Lalle bak'i aka zana mata a hannunta da k'afarta, sai da ya bushe aka wanke suka turata band'aki ta sillo wanka ta fito.
"Tubarkallah mashaa Allah. Adda dama haka kike? Kin ga yadda fatarki ke glowing kuwa. Make up kawai ya miki saura." Cewar jamila tana bude make up kit d'inta, wanda bata rabuwa da shi tun fil azal.
"Kafin nan, ga wad'annan kayan ki saka." Ta mik'o mata kayan Adama na mata kallon tuhuma. Bata yi musu ba ta kar6i kayan, aka nuna mata wani d'aki ta shiga ta saka kayan ta fito.
"Jamila lokacin sallah yayi fa." Cewar Adama. Nan aka bata sallaya ta yi sallarta sannan aka fara make up.
Kusan awa guda kwalliyar ta d'aukesu, sai da aka gama tsab, Jamila ta kafa mata d'auri da d'ankwali mahad'in kayan, sannan ta kama hannunta, ta isar da ita gaban wadataccen madubin da ke wurin.
"Innalillahi wa inna ilaihir rajiun." Shine abunda Adama ta fad'a da sauri tana ja da baya. Dariya jamila da mutanen wurin suka saka, ganin yadda mamaki ya wanzu a fuskar Adama.
"Ba ni ba ce wannan." Ta k'ara fad'a tana tattaba fuskarta.
"Wallahi ke ce fa Adda." Cewar jamila tana tattara kayanta.
Har Jamila ta biya kud'in suka bar wurin, Adama ba ta daina mamaki ba. Gani take yi tabbas canjin fuska da jiki aka mata.
Jamila bata gaya mata inda suka dosa ba, straight dark Prince Studio suka tsaya.
"Ban gane ba? Jamila ina ne nan?"
"Biyo ni ki sha labari ke dai, a zatonki wannna gayun zai tashi a banza ne?"
Bata jira amsarta ba ta fita daga motan ta zarce ciki, Adama fitowa ta yi ta tsaya tana wara ido, Jamila ta fito ta kama hannun ta suka karasa ciki.
Sai a lokacin ta fahimci abunda ya zo da su wurin, hotuna aka fara kashe mata ba adadi, cikin sa'a ta bada had'in kai kuma, domin gaba daya pictures din babu na banza.

MATAR K'ABILA (Completed)Where stories live. Discover now