22

5.4K 434 0
                                    


Sosai taji kunya ya rufeta, ta kawar da kanta gefe kanta a k'asa, yayinda zuciyarta ke bugawa da sauri tana maimaita sunan 'Admy Nah' a ranta.
"Zaki yi latti fa, naga alama bakya son rabuwa dani ne ko?"
Da sauri ta fice daga motar ta rufe ta waigo a hankali tana kallonsa don ji tayi in bata kalli kyakkyawar fuskarsa ba baza ta iya tafiya ba, wai shin lafiyanta kuwa? Me yake k'okarin faruwa da ita ne?
"Nagode." Tace dashi cikin wata sassanyar muryar da bata san tana dashi ba.
"Ina jiranki har a tashi." Ya fad'a yana shafa kwantaccen gashin kanshi mai santsi.
Tafiya ta fara yi har ta isa bakin k'ofar gidan. Tsayawa tayi cakk! cikin kwad'ayin k'ara tozali dashi.
Anwar da ke mota ya zubo narkakkun idanunshi a kanta, ya gyara zama a ranshi yana fatan ko sau d'aya ta juyo ya k'ara ganinta.
Wani irin yanayi suka shiga dukansu wanda suka kasa fassarawa especially Adama da take bak'uwa a wannan fanni.
Juyowa tayi tana murmushi suka had'a ido, wawan ajiyar zuciya suka sauk'e a tare kana tayi saurin shiga har tana karo da gate.
Murmushi yayi, ya d'an kishingid'a a jikin sit zuciyarsa cike da matsanancin so da tunanin Admy.

Tana shiga ta samu ana yiwa Amarya Hudah kwalliya, ga wata mata na mitan cewa Mallam yazo su ake jira fa. Basu k'ara minti biyu ba suka gama.
"Adama ki yafa min gyalena irin naki, ya mini kyau." Inji Amarya Hudda. Adama ta yafa mata gyalen after dress d'in da sauri suka fita gurin waliman wanda za'ayi a haraban gidan.
Anyi Walima lafiya, Mallam yayi wa'azi mai shiga jiki na zaman aure, Amarya tun daga lokacin ta fara kuka, Adama mai zuciyar tausayi itama ta fara matsar kwalla cike da tausayin k'awartata.
Bayan an tashi Anwar ya zuba ido yana jiran fitowan Adama ganin mata na ta fita tun d'azu. Shiru-shiru babu alamarta, fita yayi daga motar ya jingina ya zubawa gate d'in ido.
Hannu ya yiwa wata budurwa da ta fita daga gidan tun d'azu ta tsaya wani shago nan kusa dashi. Nufan gurinshi tayi tana wani kwarkwasa, kawar da kai yayi don haushi ma ta bashi.
"Sannuka Mallam."
"Sannunki, nace ko kinsan wata Adama Umar? K'awar Amarya ce."
"Adama? Na santa, tare muka gama makaranta ai. Ni sunana Hajara Isma'eel ko ka kirani Cute Hajar Emm... kai yayanta ne?"
"Ehh, don Allah kira min ita." Yana fad'an hakan ya shige mota ba tare da ya k'ara kallonta ba. Ita kuwa gaba d'aya ya tafi ta imaninta, gaskiya ajinsa ya burgeta.
Da sauri ta koma ciki ta samu su Adama har yanzu suna faman kuka. Tsaki taja don bata ga amfanin kukan ba, to gwanda ma Amaryan, Adama kuma kukan me take yi? Dama tun a skul ba wani shiri suke yi da Adama ba dalilin Haajar ta cika rawar kai.
Sak'on Anwar Haajar ta fad'awa Adama tana wani bubbuga bayanta alamar rarrashi, hakan ya bawa k'awayensu mamaki matuk'a suka bisu da ido. Sallama Adama ta yi musu da alk'awarin gobe zata dawo a kai Amarya tare da ita.
Tare suka fito da Hajar tana wani rirrik'eta don dai kawai ta samu shiga a gurin Yayanta.
"Kaga K'anwarmu na taya Amarya kuka ko?" Ta fad'a a shagwa6ance bayan ta bud'ewa Adama mota ta shiga.
"K'anwarki? Waye k'anwarki?" Adama ta tambayeta cikin rashin fahimta.
Dariya Hajar tayi ta langa6ar da kanta jikin window motar tace,
"Ki tambayi Yayanki."
Ba Anwar kad'ai ba hatta Adama ta yi mamakin jin furucinta, sai da tayi dogon tunani na kusan 10secs sannan ta gane in da maganar Hajar ta dosa.
Wani haushi ne ya murtuk'eta ta galla mata harara kana taja marfin motar da k'arfi saura kad'an ta had'a da yatsan Hajar.
Murmushi Anwar yayi ya kunna motar suka tafi Hajar na d'aga musu hannu, a zuciyarta tana tabbatarwa kanta ta samu mijin aure ko da Adama bata so. (K'arfin hali, adashen manga).
A hanya Anwar ya lura da yanda Adama ta murtuk'e fuska yayi shiru bai ce mata uffan ba. Ita kuma ta d'ora 6acin ranta akan cewa don bata shiri da Hajar ne gashi da alama Anwar ya mata maganar so. Wani tsaki taja wanda ba shiri Anwar ya juyo yana kallonta. Jin alamar ita yake kallo yasa ta juyar da kanta gefen window ta k'ara had'e fuska. Shima kawar da kanshi yayi ya cigaba da tuk'inshi har suka iso gida.
Ba godiya ta fara k'okarin 6alle marfin k'ofar cike da haushin Yayanta ya kula School Rival d'inta.
"Kee." Yace da ita da kakkausan murya ganin tana k'okarin rainashi.
A tsorice ta juyo suka koma Tom anda Jerry ba Love Birds d'in d'azu ba.
"Na'am Yaya."
"Uban me aka miki da kike ta kumburi haka? Ke kububuwa ce? Kuma don tsabar kin fara rainani sai ki fita babu godiya. Tukunna ma nace na gama da ke ne?" Ya k'arisa maganan kamar ya maketa.
Hakuri ta fara bashi tana dana-sanin sake fuskarta gareshi har tana tunanin maganar Umma ne ya fara zama gaskiya.

MATAR K'ABILA (Completed)Where stories live. Discover now