16

6.1K 442 2
                                    


Washegari tun da asuba masu girki da akayi haya suka zo suka fara aiki. Kafin 7 sun gama breakfast Adama da take kansu bata bar gurin ba sai da ta tabbatar komai ya kammalu sannan ta tafi bayan ai kaiwa 'yan biki.
Takwas saura dangi suka fara isowa biki ya dawo gidan Anwar. Kowacce da ta shigo zata wuce side d'in Adama. Nazifa kuma tun da ta shiga bata bud'e k'ofarta ba har wannan lokaci.
Ko'ina hayaniyar 'yan biki kake ji ana shirin bud'an kai wanda za'ayi k'arfe 10 na safe.
Jamila k'anwar Adama ta yiwa yara wanka tana shiryasu ta dubi yayartata da d'an mamaki a fuskarta,
"Aunty Adama nikam ina Nazifa ce? Tun zuwan mu banji d'uriyarta ba. Koda muka je gaishe da kwanan bak'I ban ganta cikin zuganmu ba".
"Hala bata gama shiryawa bane". Adama ta bata amsa don bata son maganan yayi tsayi.
Aunty Nafisa yayar Anwar babba da take gefe kan gado tana magana da k'anwar mamansu ta juyo tana kallon Adama ta tambaya a fuskarta.
"Adama dama tun d'azu Nazifa bata fito ba? Kina nufin duk aikin nan ke kika tsaya a kai?".
"Adda Nafisa don Allah a bar maganan, zata fito ai". Cewar Adama da damuwa a fuskarta.
Aunty Nafisa tayi kwafa ta tashi ta fita ta nufi side d'in Nazifa. Kwankwasawa ta shiga yi amma shiru ba'a bud'e ba tafi minti uku tsaye a gurin, anan Anwar ya shigo ya sameta. Jumfa da gare ne a jikinshi farare kyal yasha aiki mai tsada, hular kansa da takalmin k'afansa suma white, ko baka sanshi ba idan ka ganshi dole ka bashi suna Ango don yafi kama dasu, fuskar nan tashi sai annuri take fitarwa ga murmushi da yak'I barin fuskarsa mai kyau da kwarjini. A hanzarce ya iso gurinta game da russunawa ya gaisheta kana yace,
"Adda lafiya dai ko?".
"Lafiya lau Anwar, dama zan kar6i abune gurin Nazifa". Ta fad'a mishi haka don bata son wani abu ya 6ata mishi rai a yau. D'an murmushi yayi yana gyara garen nashi.
"An kaiwa bak'I duk abunda suke buk'ata ko Adda?"
"Duk an kai musu Ango, nace wai da anyi bud'an kai zasu tafi ne ko sai gobe?"
"A'a sai gobe Adda, dare zai musu a hanya kuma ya kamata su huta gajiyan tafiya tukun".
"Hakan yayi dai-dai".

Nazifa Fitowanta daga wanka kenan taji ana ta bugun k'ofarta wanda ta tabbatar Adama ne ko dangin Anwar don haka tayi biris tak'i bud'ewa, kwata-kwata tak'I yin gayya a cewarta k'awayenta zasu mata dariya, hatta uwarta da ta haifeta bata da labari, shiyasa ko da suka zo auren Farida suka ji labarin auren cewa sukayi baza su zauna ba tunda Nazifa bata fad'a musu ba. Gogar kuwa ko a jikinta, dama tafi son hakan wai kar dangin Amarya su rainata in sunga kalan danginta, a yanda suka fada yau da asuba zasu kama hanyar Sokoto tunda an gama bikin Farida jiya. Wayarta ta d'auka ta kira Rocky.
"Hello, Rocky har yanzu baku shigo ba gashi har jarababbun nan sun fara buga min k'ofa wallahi".
"Ke dalla muna make-up ne ga Hamdy har yanzu ta kasa za6en kayan da zata saka".
"Ni dai kuyi sauri don Allah, anjima kad'an zaki ji sun dawo."

Acan 6angaren Amarya Sa'adatu kuwa tun asuba suka tashi da shirin yau zasu koma ana gama abunda akace za'ayi. Takwas na safen bayan sun gama karyawa har wasu sun fara shiga wanka dangin Ango suka shigo gaishesu, sosai suka yaba da karamcinsu, har Adda Nafeesa na tambayan ko suna buk'atar wani abu? Suka ce 'A'a ai sun gama musu komai. Bayan sun tafi ne suke yiwa Sa'adatu murnan samun dangin miji masu karamci kana suka ci gaba da shirinsu.

09:33AM

Gida ya cika mak'il da mata kowacce tasha ado don ganin ta haska. Adama kanta yau sai da Jamila ta d'an gyara mata fuska duk wanda ya ganta sai ya k'ara juyawa yana tunanin anya wannan Adama ce? Ita ko duk sai ta jita a takure tana jin kunyan idon mutane. Abokan wasa aka shiga tsokanarta wai taji tsoron zuwan Amarya ta fara kwalliya.
Nazifa ma na can Hamdy na zuba mata kwalliya sai dai hancinta da yayi k'ato an kasa sirintar dashi Hamdy sai tsuka take ja.
"Wannan hanci naki Nazifa ai kwandala kan shiga ciki ta zauna".
Rocky ta kwashe da dariya har da rik'e ciki, Nazifa kuma ta murmusa amma can k'asan ranta taji haushi sosai.
"Baki da kyau Hamdy wallahi. Ke kuwa Nazifa banza ce, kina ji tana zagar miki halitta baza ki rama ba?".
"To me zance tunda ni na kawo kaina? Ai tasan tana da kyau ne bata da abun zagi. Ni dai ayi mini mekoft (make up) in fi kowacce jaka kyau".
Hamdy da taji dad'in comment d'in Nazifa tace,
"Sha kuruminki Nazy, yau idan Anwar bai sake baki miyau ya d'iga ba to dole idanun Akuyoyinki su fad'o k'asa".
Shewa Rocky ta saka suka tafa da Nazifa.
"Woo ke shegs".

Anwar ne zaune a d'akinsa shi kad'ai yayinda sauran abokansa ke palour ana ta hira da barkwanci kafin lokacin bud'an kai yayi.
Zama yayi a kan kujeran mirror yana kallon kanshi ta ciki, sai dai ba ainihin fuskar tashi yake kallo ba, rayuwarsa gaba d'aya da ya faru yake tunawa har rana mai kamar ta yau.
Murmushi yayi tunowa da mafarin soyayyarsu da
*ADAMA*.
TUNA BAYA....

MATAR K'ABILA (Completed)Where stories live. Discover now