15

5.8K 462 3
                                    

Hoton Sa'adatu ne tsaye tana cire Traditional Beads da aka mak'ala mata su a kan kitsonta da kuma wuyanta, da alama bata ma san an d'auketa ba.
Ya shagala da kallon pic d'in yana doka uban murmushi. Musa dake gefenshi yana kula da yanayin abokin nashi ya dungure shi da k'afarsa.
"Mallam menene haka?" Anwar ya tambayeshi a kasalance yana k'ara zooming jikin Sa'adatu ta kowanne curve.
"Gaye naga ka tsunduma ne da yawa, nan ma baka wannan ba."
Dariya suka saka dukansu suna kyakyatawa Musa har da share fake hawaye.
"Shege mutumina."

Nazifa da Adama suna can gidansu Anwar bikin Fareeda. Da yake cikin gari aka kaita yasa a ranar akayi bud'an kai aka watse.
K'arfe 9 da mintuna Abdallah ya dawo dasu gida. Ba yanda basu yi ba akan Anwar ya barsu su kwana a Family House ya hana.
"Wallahi ji nake yi kamar in shak'e Amaryar in na shiga. 'Yar banza, dangin kwad'ayi." Inji Nazifa.
Abdallah dake cire musu kayansu a bayan booth ya kwashe da dariya.
"Easy Aunty Nazifa. Mata kuna da aiki wallahi."
"Abdallah ka fita a ido na. Shin na kira sunanka ko raini ne. Sutumit (stupid)."
Adama dai bata kulasu ba tayi shigewarta cikin gidan kirjinta na bugu. Yanzu akwai wata a cikin gidan nan bayan su?
Imam ne yayi hanyar part d'in Sa'adatu jin hayaniya irinta 'yan biki.
"Kai, kai, Imam d'an k'aniya ina zaka je?" Cewar Adama
"Can d'akin zan je Mama. Ina ga an kawo Amaryar Abban ne, dama yace idan mun dawo zamu ganta tunda ya k'i zuwa dani gidansu." Ya bata amsa cikin zakwad'I murna fall a fuskarshi.
Tsayawa tayi tana kallonshi kamar ta tsinkeshi da mari. Yafutoshi tayi da hannu fuskarta babu alamun wasa, in Banda yaro da rashin wayo bai San kishiya aka yiwa uwarsa ba, shi murna ma yake yi. Gunguni ya fara ya nufosu.
"Mama ita kuma me sunanta? Abba ya fad'a min na manta." Laila ta tambaya a lokacin da Adama tasa key tana bud'e musu part d'inta.
"Ban sani ba. Kije ki tambayi Abban naku don nima na manta." Suka shige taja k'ofarta ta rufe ba tare da taje ta musu sannu da zuwa ba.
Gefen Nazifa kuma Abdallah na sauk'e mata kayanta itama ta d'auka tayi part d'inta.
Tana shiga wanka ta watsa, duk jikinta yayi sanyi lokaci-lokaci kuma kirjinta na bugawa yana mata ciwo.
Doguwar rigarta na bacci ta zura tayi kwanciyarta kan gado. Kuka ta fara a hankali tana share hawayen dake sauk'a kan pillow nata.
Kad'an-kad'an take jin hayaniyar 'yan bikin da yake tafi kusa dasu daga part d'inta sai na Amarya, da alama basu ma da niyyar bacci. Haushi ne ya turnuk'eta tayi dialing numbern Anwar. Ringing biyu ya d'auka.
"Kina ina ne?"
"Ina d'akina mana."
"To kizo mana, tun d'azu Abdallah yace ya dawo daku."
"Kai da kake da Amarya me zanzo na maka?. Ni ba wannan ba, mutanen nan sun dame ni da hayaniya, daga zuwa har sun fara nuna hali. Wannan ai rashin tunani ne, mutane sun kwaso gajiya zasu hanasu bacci."
"Kin gama?" Ya tambayeta cikin sassanyar murya.
"Ehh na gama, saura ka je ka musu magana su rage balum (volume) d'in muryoyinsu."
"Sai da safe Nazy." Tit ya katse wayarsa yana murmushi. A ranar da ya kamata yafi kowa farin ciki bazai bari ta 6ata mishi rai ba. Dama already ya kwanta, kuma yasan ba zuwa zata yi ba shima kuma baya buk'atarta a yanzu. Kiranta ne ya shigo wayarsa ya kashe, Sa'adatu ya k'ira suka raba dare suna hira.
Nazifa ta yi ta kiran Anwar tana jin line busy, kishine ya turnuk'eta tayi jifa da wayar ta had'u da bango ta tarwatse, itama Nazifan tarwatsewa tayi da kuka. Fita tayi zuwa side d'in Anwar tayita bugawan duniyan nan yak'I ya bud'e ta koma ta d'auko key ta gwada sakawa ta samu ya rufe da lock d'in k'ofar ba yanda zata bud'e. Karshe dai hakura tayi ta koma cikin gida ta nufi part d'in Sa'adatu.
Har bakin k'ofar taje ta tsaya kamar tayi knocking amma tana shakka, don taji daga bakin dangi wad'anda suka kawo musu abinci wai 'yan uwan Amaryan gansama-gansama ne ga tsayi kamar samudawa, karamar cikinsu wai zata iya zaune Adama.
Tana nan tsaye ta kasa bugawa ta kasa komawa d'akinta. Wata Mage ce ta fara kuka Nazifa ta runtuma da gudu ta shige d'akinta tana tsine duk 'yan gidan albarka.

MATAR K'ABILA (Completed)Where stories live. Discover now