MAKAUNIYAR RAYUWA

227 11 3
                                    

________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
Arewawritersassociation@gmail.com

         *PART THREE*
              *PAGE 19*

*BISMILLAHR RAHMANIR RAHIM*

_____"Daddy yana shiga sbayan ya karya yai ya shirya domin zuwa kasuwa, bayan ya dawo daga kasuwa ne, lokacin yana cin abinci,yayin da Talatuwa ke zaune suka dashi,cikin raha da dabara take tambayarsa abinda ya ɓata masa rai da safe kafin ya fita kasuwa".
   Murmushin takaici yai snn ya zayyana mata duk yanda sukayi da Inna"
    Murmusawa Talatuwa tai snn tace"Allah ya kyauta"
  Tou yanzu kai me kace?"
Meko zance da ita,tunda tazama abinda tazama,nidai abu ɗaya nasani shine aure dai babu fashi insha Allahu"
Kwarai kuwa alhj"
  Suna cikin haka kenan saiga Mu'azam yai sallama ya shigo,duƙawa yai ya gaida su bayan su gaisa Daddy yake sanar masa yanda sukai da Inna".
  "Kai Mu'azam ya kaɗa alamar rashin jin daɗi"
  "Daddy yace"amma kada kadamu,insha Allahu aure tsakanika da Rukky babu fashi,in har kaga be wuyu ba to kasa a ranka dama can Allah beyi matarka bace,dan haka kaje kaci gaba da shirinka".
   Murmushin Mu'azam yai haɗi da godiya"
   Har ya yunkura zai miƙe Daddy ya taresa da maganar wajan zama"
  Cikin Jin kunya yace"dama hayane,kuma har naba da cigiyar ɗaki"... Karaf Talatuwa ta taresa da wani irin haya kuma babu daɗin ji,shi nan ɗin da kake zaune meya sameta,kodai gidan ne beyi maka ba?"
  A'a,ba haka bane".
"Tou menene?"
Shiru yai babu amsa"
"Talatuwa taci gaba da cewa idan daki ɗaya yai maku kadan ne me zai hana ku haɗa da tawa ɗakin..
  Daddy ne ya katseta da cewa"ke kuma fa?"
  Tawa me sauri ne, basai na kwashe kayana na koma cikin gida ba".
Cikin gida kuma?"igi Mu'azam kenan".
  Eh cikin gida,saina koma ɗakin dakai samartaka kai kuma sai ku haɗu ya zama maku ciki da falo kodan yara,ko yaya kagani?".
   Shiruuu Mu'azam yai"
Daddy ne ya katse masa tunani da cewa"bakace komai ba Mu'azam".
Daddy duk yanda kukayi dai-daine"yana maganar miƙewa yai ya bar masu wajan".
Su jima suna tattanawa shida Talatuwa,daga ƙarshe dai haka suka shiri ita zata koma cikin gida shi kuma saiya haɗu dakunan ya zama masu ciki da falo".
Katin sati daddy yasa aka fara gyarawa Talatuwa ɗaki"
Tunda Inna taga ana gyara ta kasa zaune ta kasa tsaye,daga ƙarshe koran ma'aikatan tayi tace"suje su cema wanda ya sasu aikin ta koresu idan ya isa yazo da kanta tana jiransa"
Duk da haka bata hakuri ba,bin Talatuwa tai har gida, ƙafa babu takalmi bare mayafi haka ta fice daga nata gidan zuwa gidan Talatuwa"
Tana tafe siket na binta bugazai-bugazai kamar an kwatoshi daga bakin kura"
  Haka ta fasa gidan Talatuwa babu ko sallama,lokacin Talatuwa na kwance a ɗakin tana bacci,kamar daga sama take jiyo hayaniyar Inna,kafin ta miƙe tace zata fita wajan tuni Inna ta faɗo mata daki, haɗi da yaƙe mata labule".
Cikin idon bacci Talatuwa tace"a'a Rabu ne,shine babu ko sallama"...Cikin masifa Inna tace"banyi ba kuma bazan ba,mutune kirki akewa sallama ba irinku ƴan wuta ba,babu ko shakku ke ƴar wuta,muguwa azaluma manafuka insha Allahu ƙarshenki bazaiyi kyau ba".
Jin muryan Inna a gidan yasa gaban Rukky yankewa ya faɗi, innallilahi tace"snn ta fara hasa-hasa ta fitane ko kuwa tai zamanta,domin a yanda takeyi jiyo muryan Inna babu ko shakku a sattin take".
  Ta windo ta leƙa domin hango Inna"kasancewar suna ɗaki ne yasa bata hango ba sai sautin muryanta da take ji"
   Murmushin Talatuwa tai snn tace"Uhmm ta kanki akeji mahaukaciyar banza kawai, nasan ba'a kan komai kike wanan haukar ba sai akan auren Mu'azam da Rukky, aure ne dai babu fashi"
   Fuuuu Inna tai da niyyar wawuro Talatuwa"
    Kafin takai gannu jikin Talatuwa tuni Talatuwa tasa nata hannu ta hankaɗe Inna ta faɗa cikin kwandon wanke-wanke,kwatsatttsatsam kwanuka suka dunga karo da junansu"
  Kafin Inna ta miƙe da sauri Talatuwa tafice tabar mata ɗakin"
   Yiiiihuhuuu Inna tace"tana miƙewa ta shiga wargazawa Talatuwa ɗaki duk abinda tagani a kintse saida ta wargaza hatta garin masara saida Inna ta tsiyaye masa manja akai snn ta haɗa da garin kuka a cikin snn ta ɗauki fantekan garin ta kira akan gado tanayi tana tsinewa Talatuwa da Rukky albarka ita haɗi da cewa"in ta haihu cikin uwarta da ubanta saita wargaza auren".
   Rukky dake ɗaki babu abinda takeyi sai kuka haɗi data sani amincewar auren Mu'azam da tai".
   Duk irin haukar da Inna keyi Talatuwa na daga tsakar gida tana kallonta,da zaran su haɗa ido gwalo dakewa Inna snn tace da ita"aure dai babu fashi ba zafin rai ba mutum ya haɗiye zuciya ya mutu".
   Inna bata fita daga gidan ba saida ta tabbata ta wargaza ɗakin snn ta fita"
Duk da abin ya dami Talatuwa amma saita danne damuwarta"Inna ta fitowa tace"mahaukaciya har kin gama?".
  Wuuu tai kanta haɗi da cewa"ubanki ne mahaukurci,snn taci gaba da cewa"ai ga aikin haukan nan nayi maki nasan koba komai yau saiki yini kina gyara"
   Ke gyara ya dama".
Inna tajima tana tsine-tsinenta snn tafice daga gidan"tana fita Rukky ta fito daga ɗaki cikin kuka ta zube gaban Talatuwa tana bata hakuri bisa ga abinda Inna tai mata,a cewarta duk sune suka jawo mata".
Babu komai Talatuwa tace" Nan suka hau gyara ɗakin ita da Rukky,kafin la'asar su gyara ko ina tsaf,garin masarar da Inna ta ɓata daga dayake tanada ijiyar wani garin ɗaukar lalataccen tai tabawa tumakai makwabtansu da suke shigowa sukaci,ita kuma tai amfani da wani" Daga Talatuwa har Rukky babu wanda ya faɗiwa daddy abinda Inna tazo tai ɓarna".
   Da yamma yana dawowa kasuwa shiga gidan Talatuwa ba saida ya fara shiga cikin gida domin gani aiki,yana shiga gani ɗaki yai kace-kace da alamar anfara gyara,to komai ya hanasu ƙarisawa oho,nisan dai ba matsala kudi ba,domin saida na biyasu kuɗinsu tun daga na kayan aiki har zuwa ga tasu amma bari na kirasu naji dalilinsu nayi haka".
Hannu ya sanya cikin aljihunsa ya ciro waya,ya ɗaya daga cikin masu aikin"
Yana gani kiransa da sauri ya ɗaga, haɗi da sallama,bayan su gaisa Daddy ke tambayarsa abinda ya hanasu ƙarisa aiki".
  Nan ya kwashe duk yanda sukai da Inna ya faɗi masa"Hakuri daddy ya basu snn yace"idan bazasu damu ba gobe suzo su ƙarisa yana gida babu inda zaije har sai su ƙare".
  Duk abinda yakeyi Inna na kallonta ta labule,taso yazo ya tareta da maganar ne,gani ya fice be tunkareta ba yasata ciza laɓɓanta haɗi da cewa"Allah ya taimakeka"
  Tun daga lokaci be sake bi takan Inna ba,cikin sati yasa Rukky ta shirya domin zuwa gida wajan iyayenta,sha biyu na arziki ya haɗa mata,shima Mu'azam ba'a barsa a baya ba,duk da siyayyar da daddy yaiwa Rukky be hana Mu'azam yi mata ba,cikin kayan har da zani da hijab kala biyu ya siyewa mamanta haɗi dasu sabulai da man shafi"
  Su Muhammed da Muhasana kayan  kala biyu-biyu ya siye masu,ranar da zasu tafi har tasha ya rakata,bebar wajan ba saida yaga tashinsu snn ya koma gida".
   Kwana ɗaya da tafiyar Rukky Talatuwa ta tare a cikin gida, ranar haukane kawai Inna batai ba,amma zagi da tsinuwar albarka sai abinda ta mance duk da haka be isheta ba ruwa ta dunga ɗibawa tana jiƙa tsakar gida, bayan ta jiƙa ko ina tasamu wajan ta zauna tana me meda numfashi,can ta hango tsummar Talatuwa rataye a igiya da sauri ta kuma miƙewa taje ta wuya ta yanka igiyar kayan suka zube a ƙasa, kafa Inna tasa ta murje kayan da kafa snn ta koma ɗaki".
  Gani duk irin abinda tai Talatuwa bata magana yasa Inna gani kamar tsorone yasa Talatuwa bata iya meda mata martani,kullum ta yayibo sharanta sai kan Talatuwa"
  Tun Talatuwa na danne zuciyarta har yakai ga ta ƙureta wani safiyar juma'a bayan daddy ya fita kasuwa, da yake ranar Talatuwa ce keda girki, tana sallamar daddy ta haɗa kayan wanke-wanke ta wanka,gefe guda ta shanya tana jira ya bushe snn takai ɗaki".
  Tana gama wanke-wanken ta share ko ina snn ta shiga ɗaki domin gyarawa,nan ma bata ɗauki lokaci ba ta gama duk wani aikinta bayan ya kai kayan ɗaki waja ta samu ta kwanta a cewarta bari tadan rimtsa kafin tai wanka".
   Tana kwanciya bacci ya dauketa, befi ashiri da keanciyarta ba kawai taji saukar ruwa a jikinta,a gigice ta tashi haɗi da faɗin innallilahi wa'innailailin raju'un buɗe idon da zatayi RABI tagani tsaye gabanta riƙe da botikin ruwa a hannunta tana faman huci kamar wata kububuwa".
      Kallo ɗaya Talatuwa tai mata snn tai tsaki,sabida tsabar takaici tama rasa ta ina zata fara,wata zuciya tace"amshi botikin kawai ki riɗa mata,wata zuciyar kuma tace"yayiwa shegiya ƙafa tana zubewa ki haye ruwan cikinta ki ɗibawa shegiya kashi,wata zuciyar kuma tace"a'a Talatuwa idan har zaki rama basai kin biyeta kin zama makauniya irinta na,idan har kikai haka kin zama kare kenan irinta,idan banda rashin hankali ina kika taɓa gani kare yai haushi ka biyesa,idan har ramawa zakiyi basai kin biyeta kunyi tashin hankali ba cikin ruwan sanyi zaki dafata da baƙaƙen maganganu wanda idan ita me hankalice ya isa tasan annabi ya faku".
     Duk da ranta ya ɓaci tai sai ƙoƙarin danewa, murmushin yaƙe tai snn tace Allah ya baki hakuri,nasan ni me laifine a gareki musamman ma idan nayi duba da irin laifin da nayi maki,kinga be kamata na biyeki ba ko shi na barki dashi ya isheki"kadafa ki mance ni maciyace wacce bata rami kanta sai dai a gina ta shiga,wlh RABI inda nasan haka raminki yake da ban tsaya ƙasa a guiwa ba da tutuni na daɗe da shiga,kaji rami da ni'eemtaccen ni'eema da daɗi? gaskiya RABi kinyi asanar duniya da lahira domin samu namiji irin Yallabai me iya tattala mace da sani darajanta sai an tona,,,wufff Inna tai kan Talatuwa tana faɗin uwarki da ubanki ne sukai asarar duniya amma ba niba"
Duk irin maganganu da Inna tai ta faɗiwa Talatuwa kin kulata tai data gaji dan kanta ta fice daga ɗakin,Inna ta fita Talatuwa ta ɗaga katifar ta jingina a bango"
   Lokacin da daddy yazo kwanciya gani katifa a jiƙe yasa shi tambayar garin Yaya ruwa ya zuba a katifa?"
       "Duk irin tsigewar da Inna tai mata Saida ta faɗiwa Daddy"Cike da takaici daddy ke magana,daga ƙarshe yace"Nasan maganinta,duk yanda Talatuwa taso jin irin hukunci da zai yankewa Inna kin faɗi daddy yai"
  Bayan isar Rukky gida da kwana biyu daddy ya kira ta numbar ta yace"tabawa mmnta"
Bayan Rukky ta baiwa mmnta suka gaisa cikin girmamawa snn daddy yai mata jajen abinda ya faru"
  Murmushin tai haɗi da cewa"baby komai,kadan ita aure abune me rai da zaran shan ruwa ya ƙare shi kenan"
  Hakane daddy yace"Snn yake sanar da ita maganar Mu'azam".
  Murna sosai tai haɗi da cewa"Rukky da Mu'azam ɗin ai duk suna ƙarƙashin ikonsa suke dan haka yaje yai duk abinda daya dace" fatan alkhairi duk sukaiwa juna snn daddy yace"idan maigidanta nada waya ta bashi numbar yanason magana dashi".
    Tou tace"snn sukai sallama"
mijinta na dawowa daga kiwo ta sanar masa"
  Babu damuwa yace"Snn ya amshi numbar daddy, bayan ta bashi yakisa,suna gaisawa daddy ya sanar dashi maganar auren"fatan alkhairi shima yai snn yace"bashida iko akan Rukky amma tunda akwai wani ƙanin babanta wanda be daɗe da dawowa ƙauyen ba insha Allahu zaije ya sanar dashi daga nan zai bashi numbar sa".
   Cikin Jin daɗi daddy yai masa godiya,washe gari yaje har rugan Baffa Ibran ya sanar dashi abinda ke tafe dashi daga nan ya bashi numbar daddy"
Take daddy ya kirasa sukai magana,nan suka yanke ranar auren wani juma'a me zuwa"
    "Jin an dai-daita yasa mmn Rukky ta shiga gyara ƴar, musamman take shiga jeji ta sassaƙo ɓawon itatuwa tazo ta harhaɗa da mahaɗi ta dafawa Rukky,nasha dana tsarki,ga kuma ɗanyan nono da kullum take sha babu dare babu safe"
    Cikin ƙanƙani lokaci Rukky ta game tai gam,ga kuma jika da tai a ciki"
   Ana sauran kwana biyar daddy ya tura Mu'azam gida jalingo,kafin ya isa tuni ya kira ƴan uwansa ya sanar dasu,hakan yasa Mu'azam na isa suka  amshesa hannu bibbiyu"
    Washe gari har da Mu'azam ɗin akakai kayan aure gidan Baffa Ibran,ranar juma'a bayan saukowa daga masallaci aka ɗaura auren Mu'azam da RUKAYYA, da yamma bayan sallar magrib ɗangin uwa da matan Baffa Ibran suka raka Rukky gidan mijinta wato Mu'azam"
   Ɗaki musamman ƙanin daddy yasa aka gyara masu"
   Ƴan kai amarya basu daddy ba kowa ya watse tun kafin hasken farin tawa ya disashe domin shine fitilarsu idan dare yayi" 
      "Misalin ƙarfe tara Mu'azam ya shigo ɗaki".
   "Lokacin Rukky na zaune bakin gado kanta rufe yake da mayafi,Jin sallamar Mu'azam yasa Rukky gyara zama haɗi da ƙara janyo mayafin dake kanta ta ƙara rufe dukkani jikinta dashi".
     "Jiki a sanyaye Mu'azam ya ƙarisa shigowa daga ciki haɗi da sallama"
Ciki-ciki Rukky ta amsa,ba lallane yaji ba"
      "Yana shigowa bakin gado,ije ladar dake hannunsa yai a gefe,sufi minti goma babu wanda yaiwa ɗan uwansa magana,ƙirjinsa kuwa sai faman dukan uku-uku yakeyi,daga ɗaya jikinsa yai sanyi wanda shima kansa besan dalili ba"
     Kasancewar shine namji yasa shi ƙarfin halin kiran sunanta"
   A hannnkali Rukky ta amsa da na'am"
  Kinga yanda Allah ke ikonsa ko?wai yau muke zaune a ƙarƙashin inuwa ɗaya"Daga yau ni Mu'azam za'a kira da sunan mijinki,kai Allah na gode maka Allah abin godiya"
Yanzu dai kamata yai mu tashi muyi sallah domin godewa Allah ma ɗaukackin sarki daya nuna mana wanan rana me tarin albarka a garemu"
     Miƙewa yai yanufi bakin ƙofa da niyyar fita,juyawar da zaiyi can ya hango batikin fyanti haɗi da babban butan rover a bayan ƙofa,tafiya yai yaje ya jijiga butan domin ji akwai ruwa a ciki ko babu?"
  Cike tam yaji butar daga yai yaje yai tsarki snn yai alwala, ijewa Rukky yai a bakin ƙofa bayan ya shigo ita kuma ta fita taje tai nata alwala tana gamawa ta shiga dashi ɗaki"
  Jansu sallah raka'a biyu,bayan su idar su jima suna addu'a snn suka shafa, bayan su shafa ne yasa hannu ya jawo ladar daya shigo dashi buɗewa yai snn yace da ita bismillh"
Kasancewar ƙauye ne ba wani kayan maƙulashe za'a samu kamar birni ba"
   Tsirene kawai ya samu da fanta na rover"Kunya ya hana Rukky ci,babu yanda Mu'azam beyi da ita data ci amma taki daga ƙarshe shi yaci kayansa snn yaje ya wanke baki yadawo ɗakin"
     Sanyawa ƙofa sakata yai snn yazo Saida ya rage kayan jikinsa,rigar captani dake jikinsa ya cire yabar doguwar wando da sigileti snn ya kwanta".
  Bayan ya kwanta ne itama ta tashi taje ta gefe ta haye gado,can jikin bango ta raɓe, befi minti biyar da kwanciya ba bacci ya ɗaukesa"Rukky dake kwance tana kallonsa cikin zuciyarta tace shi kuma wanan wani irin angone haka?kodan sabon shiga ne?ko kuma jiki yake na bisa?aiko idan hakane ba binka zanyi ba,duk da sonda nake maka idan baka biyo ni sai dai mu zauna haka"
   Ance bacci ɓarawo batasan  lokacin da bacci ya dauketa ba"
   Masalin ƙarfe biyu da rabi Mu'azam ya falka,gani Rukky kwance kusa dashi, wani irin daɗine ya kamashi,ƙara matsawa yai kusa da ita hannu yasa yana fashe fuskanta,yanda yake sharar fuskanta a hankali haka yakeji wani irin abu na ratsesa,sunkuyawa yai da fuskansa kan nata a hankali yake kissing nata"
Tun daga lokacin daya falka itama Rukky ta falka amma bata yarda ya gane ba"
     Gani bazai iya jure abinda yake jiba yasa Mu'azam rungumeta tsaf a ƙirjinsa,na ɗan wani lokaci daga snn besan lokacin daya hayeta ba,befi minti biyar da hayeta ba kome tajiyo oho da sauri ya miƙe ya cire singiletin dake jikinsa yai hurgi dashi,snn yaci gaba".
  Can anjima kuma ya sake cire doguwar wandon dake tsaye da ita,bayan wani minti biyar ɗin kuma ya sake cire gajeran wandon daya rage,daga ƙarshe dai komawa yai babu komai a jikinsa sai faman saffa da marwa yakeyi wanda bana macca ba".
   Cikin mafarki ƙamaru yagano Rukky kwance da wani namiji ba shiba,ihuuu yasa wanda shi kansa besan cewa a zahiri yakeyinta ba,haɗi da faɗin aa dan Allah wlh matata ce,wlh matata ce,dan Allah kada kaimin haka"
   Duk irin abinda Mu'azam keyi akan Rukky haka Ƙamaru ke gani"Wani irin ihuuu ƙamaru yasa haɗi da faɗin ooooooooo Rukky...
   Bazan gajiya da baku hakuri ba akan rashin editing,nasan zakuyi karo da error's masu waya Dan Allah kuyi hakuri.Afuwan afuwan afuwan please.Ngd sosai da comment ɗinku haƙiƙa kun nunamin so da kauna wajan zubo ruwan comment,insha Allahu idan kuka haka hakuri dani da haka komai zai warware insha Allah ngd.######
        
  
  

MAKAUNIYAR RAYUWAWhere stories live. Discover now