MAKAUNIYAR RAYUWA

156 10 6
                                    

*MAKAUNIYAR RAYUWA*
________________________________

*AREWA WRITES ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________

~DIDECATED TO~
*ANTY FAUZIYA*
*ƳAR AMANA*

https://www.facebook.com/104534761033461/posts/109559843864286/?app=fbl

*PART THREE*
*PAGE 5*

*BISMILLAHI RAHMANI RAHIM*

______"Gani number Rukky ce yasa mutumi cewa"Alhamdullhi,saida ya kwashi sama da miti biyar yana kallo screen ɗin snn shima ya meda mata da reply da barka da warhaka,snn ya tura"
Rukky dake rike da wayar a hannu gani shigowar wani saƙon ne yasata budewa,tana gama karantawa harta rubuta masa amsa sai kuma ta tuna cewa kuɗinta ya ƙare,dama four naira ne kawai ya rage mata a wayar kuma tai amfani dashi wajan tura mata saƙo.
Ije wayar tai gefe daga snn bata sake bi takan wayar ba,tashi tai taci gaba da aiyukanta.
Taiwa yara wanka tai wanke-wanke ta share ko'ina snn taje tataya iya aiki wanke-wanke da shara ta gyara mata ɗaki tasss snn tadawo nata ɗaki,gu tasamu ta zauna tana jiran ruwan data ɗora yai zafi taje tai wanka.
Ƙirim taji wayarta yayi da sauri ta miƙe take ta cire a cajin da tasa,tana dubawa taga saƙona me nuna da alamar kuɗine aka sanya mata through bank,da sauri ta buɗe tana buɗewa kuɗi tagani naira dubu biyar,duk da haka bata gasganta ba da sauri ta duba balance ɗin wayarta,a lokacin ne ta gasganta,sai dai wani abun tambaya shine babu suna ko numbar bare tasan waye ya tura mata dashi.
Komawa tai ta zauna tana tunanin waye zai turo mata da kuɗin haka, ta gaba ɗaya ta mance al'amarin mutumin nan sai daga baya snn maganarsa ya faɗo mata,cike da mamaki anya shine zai tura mata zaisanya mata kati me yawa haka?,a wani ɓangare kuma tace,ko dayake ba abin mamaki bane dan ya sanyami kuɗi me yawa haka, musanman ma idan nayi duba da girmansa,(ina nufin ba garma ta shekaru ba,girma ta kuɗi).
Shigowar su Muhammed da Muhasana ne ya katse Rukky,da sauri ta ije wayar haɗi da kiran sunan su tana tambayarsu har su dawo?.
Shiru-shiru mutumi bega Rukky ta kirasa ba yasa shi tura mata da taƙaitancen saƙo da cewa"kinga saƙo ko tou kiyi hakuri babu yawa".
Snn ta tura mata.
Tana buɗe ta karanta, murmushi tai snn itama ta meda masa da murtani da"eh wlh na gani amma ban san waye ba sai yanda""...da sauri ya kuma tura mata da murtani da"dama kinada wani ne bayan ni?.
Saƙon ya shiga wayar Rukky ne yana ɗauke da pict ɗin baby me ɗauke da ɓacin rai.
Dariya Rukky tai masa snn tace"afuwan ba haka nake nufi ba,kasan idan irin wanan saƙon ne kasan baya zuwa da numbar bare na gane wanda ya turo min da saƙon..
Uhmm yace"snn yaci gaba da cewa"yanzu naji dai-dai...
Murmushi Rukky tai snn tace"in ba haka bafa...kaeekaee wlh baby dan bakisan yanda nake jiki a zuciyata bane..sai kuma ya katse da tambayar ina yaran suke?.
Cikin kunya tace suna cikin gida suna wasa...wasa dawa?.da ƴan uwansu..dan Allah ki rinƙa kulawa dasu dan Allah..ƙara gyara muryanta tai snn tace"ina kulawa dasu mana...Nasan da haka amma inaso ki ƙara fiye da wanda kike basu..hmm Rukky tace''..dariya sosai yai, yajima yana dariya snn yace"baby kenan,ba komai bane nasan duba zakiyi da ke kika haifesu,tou amma wani abu da baki sani ba baby, wlh yaran nan da kike gani amana ne Allah ya baki idan har kikai masu roƙon sakainar kashi sai Allah ya tambayeki,idan kuma kika basu kyankyawan kulawa sai Allah ya baki lada snn kuma su kansu yaran zasuyi alfahari dake,dan haka ki kula dasu dakyau da Allah..himm kawai Rukky tace''su jima suna hira snn sukai sallama.
Tun daga ranar haka yake kiranta suyi hira sai dai rabin kiransa da dare ne saiya dai-dai ci yara suyi bacci,sabida idan har basuyi bacci ba damusu sukeyi da surutu musanman ma Muhammed tsayawa yakeyi yace"lallai sai an bashi wayar yai magana da babanshi.
Idan ko da dare ne sai sukai ƙarfe ɗayan dare suna waya ba tare da wani ya takura masu ba...

****
"A ɓangaren Sofy kuwa soyayya ce kawai suke zubawa ita da alhj KABIRU,sai dai duk lokacin daya buƙaci su haɗu sai dai su haɗu a hotel.
Babu yanda beyi da ita ba da tanuna masa gidansu amma taki,kullom sai dai su haɗu a hotel,gani haka yasa alhj KABIRU cewa"in har bazata nuna masa gidan suba sai dai su haƙura da juna.
Alhj KABIRU ya faɗi hakane kawai domin a yanda yakeji a zuciyarsa bazai iya rabuwa da ita ba.
Duk lokacin da zasu keɓe tare, mafi yawancin hiransa da Sofy shine,ina sonki Sofy,bazan iya rabuwa dake ba Sofy.
Hakan ya bawa Sofy damar lallaɓarsa har ya hakuri sukaci gaba da zuba soyaytarsu.
Duk lokacin da sukeda buƙatar gani juna sai dai su haɗu a hotel.
Kamar kullum duk lokacin da suka keɓe sai tai ta ƙoƙarin haɗa jikinta da nasa.
Duk da sonta da yakeyi amma yaƙi yanrda su haɗa jiki da ita,domin a cewarsa idan har ya ɗaɗana zumarta ba zai iya haƙura da ita ba,hakan yasa ya yanke wa kansa shawarar aurenta.domin idan bata aure ba alkawari ya ɗaukar wa kansa bazai kwanta da ita ba.
Haka sukaci gaba zabga soyayyarsu harda ɗauka hotuna kala-kala wasu yana rungume da ita wasu kuma ita ke rungume dashi.
Assalamualaikum! Assalamualaikum!! Assalamualaikum!!!jin shiru da hjy tai babu amsa tura ƙofa tai tashiga cikin ɗakin.
Tana shiga taga ɗakin babu komai sai motsin ruwa da takeyi a ban ɗaki,gu tasamu ta zauna tana jiran fitowarsa,karaf idanta yakai ga wayar alhj inda samar wayar ke haske alamar an kirasa ko kuma an turo masa saƙo,hannu tasa ta ɗauki wayar gani an SAFIYANU akan saƙon yasa hjy basar da al'amarin,har zata meda wayar ta ije sai kuma ta ƙara tsurawa screen ɗin ido, sama-sama taga an rubuta(barka da safiya da fatan ka tashi lafiya,ya gida da kwanan antyna da fatan duk suna lafiya.Jiya kace zamu haɗu kuma bamu samu haɗuwa ba,tou yau fa?)....iya abinda tagani kenan.
Shiruuuuu hjy tai haɗi da zabga uban tagumi,nan ta fara tunani haɗi da zancen zuci,tana tambayar kanta,dama alhj ƴan mata yake nima bata sani ba?...buɗe ƙofarsa ne ya katse mata tunani,fuska ɗaure tace"har ka fito?.
Baƙin alhj KABIRU har kunne yace"eh na fito.
Tun daga sann bata sake magana ba,duk abinda zaiyi ido kawai take binsa dashi haɗi zubawa wayar ido.hakan yasa hankalin alhj ya koma ga wayar,da sauri yasa hannu ya ɗauki wayar haɗi da cewa"kirana aikai?, Allah yasa ba daga office bane,yana buɗe wayar yaga Soft ne,nan ya fara kame-kame haɗi da inda-inda yanayi yana sosa kai.
Gutun tsaki hjy tai snn tace waye?...
Firgigi alhj KABIRU yai da ido snn yace"wafahhh!!!.
Wanda ya kiraka,ko nace ta kiraka?.
"Shashewa yai da cewa"alhj SAFIYANU nefa ya kirani lokacin bana kusa"...bashi na tambayeka ba,wayar nace kabani...me zakiyi da wayata..wufff tai haɗi da buɗe masa ido tace"kabani nace ko...duk da haka kin bata yai a dole saita faɗi masa abinda zatai dashi..gani haka yasa hjy fashewa da kuka tana faɗin dama matan banza kake nima ban sani ba....Cikin zarana alhj KABIRU yace"matan banza kuma,haba hjy wani irin magana ne kikeyi haka.
Duk da haka bata kulasa ba ci gaba da kukanta yai haɗi da maganganu tana cewa"da wanan niman matan banzan da kakeyi ni wlh da aure kayi dayafi min... subhanallilahi alhj KABIRU yace"da sauri yadawo gabanta,kamata yai ta zauna haɗi da cewa"wlh Allah ba matan banza nake nima ba,dama so nayi idan komai ya dai-dai saina sanar dake,Amma tunda abu ya zama haka bari na faɗi maki..
Gu yasamu ya zauna kusa da ita,bayan ya zauna ne ya fara da cewa"dama wata yarinya na samu...cikin masifa hjy tace"kasamu kamar yaya?.
Be tanka mata ba,yaci gaba da cewa, dai-dai wane bamuyi ba yasa ban sanar maki ba,na bari har sai mu dai-dai sann na sanar maki...doguwar tsaki hjy tai snn taci ƴar wani gidace snn waye ubanta a garin nan... murmushi alhj KABIRU yai snn yace"ba ƴar gidan uban kowa bane amma ina yi mata kyankyawan zato snn.. kyankyawan zato kamar yaya alhj?hannu tasa zata fisge wayar dake hannunsa,da sauri ya kauda wayar haɗi da cewa"me zakiyi da wayata..abu zan duba tace.. murmushi alhj ya kuma yi,yasan ba komai bane ke damu hjy irin zargi.
Cire code ɗin wayarsa yai snn ya shiga album ciro hotou SOfy wanda take ita kaɗai, yai haɗi da cewa"nasan ba komai kikeson gani ba illa hotoun ta,tou gashi..
Kallo ɗaya hjy taiwa hoton Sofy ta tsanke da salati tana faɗin innallilahi wa'inna'ilaihin raju'un,alhj mezan gani??eh alhj yanzu matar ɗauka kake nema??..
Cikin rawan jiki alhj KABIRU yace"wani irin magana kikeyi haka ehh,waima matan wani ɗana daga cikin kike magana.....ɗanka JIBRIN mana..take zufa ya fasowa alhj KABIRU,jikinsa sai ƙyarma yakeyi,besan lokacin daya fito da ragowar hotunan ya nunawa hjy ba.
Bayan sallar isha duk suka haɗu a gidan alhj maman J-boy.
Tunda J-boy ya cewa"Sofy ta shirya hjynsa na nimansu jikin Sofy yai sanyi,babu irin tambayar da batai masa ba daya faɗin mata dalilin kiran da hjy keyi masu amna yace be sani ba.
A dole badan tasoba ta shirya suka nufi gidan hjy.
Ko kafin su isa su alhj KABIRU da matarsa duk su isa su kawai suke jira.
Sallamar da zasuyi falon sukai ido biyu da alhj KABIRU da kuma matarsa hjy take cikin Sofy yai wani irin ƙara da ƙugi,ta jima tsaye a baƙin ƙofa bata ƙarisa daga ciki ba har saida J-boy yace"yaya dai Sofy,ƙariso mana"
Uhmm himm tace"snn ta ƙarisa daga ciki,tana shiga ƙasa ta samu ta zauna jiki a sanyaye haɗi da jawo mayafin dake kanta ta rufe fuskanta dashi.
Shiko alhj KABIRU dake zaune gaba ɗaya jikinsa ya jiƙe da zufa sharrkaf,yama rasa da ita zai fata.
A ɓangaren hjy matarsa kuwa sai faman cewa take Allah ya tuno asirinki manafuka kawai..
Har ƙasa J-boy ya duƙa yana me gaida iyayensa.
Daga hjy har alhj KABIRU babu wanda ya amsa masa,hjyn J-boy ce tai gyaran murya snn taki sunan SAFIYA..
A sanyaye Sofy ta amsa da na'am...meke tsakaninku da alhj KABIRU,babbbbb babu komai tace"""cikin tsawa hjy tace"zaki faɗi gaskiya ko yaya?.
Jin haka yasa Sofy fashewa da kuka haɗi da cewa"wlh kuskure ne ayi hakuri...kafin Sofy ta rufe baki tuni hjy tasa ƙafa ta tokare Sofy dake zaune kusa da ita,tana faɗin ayi hakurin ubanki shegiya manafuka... yunƙurawa J-boy yai haɗi da kamo Sofy dake can gefe yana faɗin wai menene hakane dan Allah..tsawa hjy ta dakawa J-boy tana me cewa ubankane,,,nace ubanka ne,fisgo Sofy dmtai dake raɓe a jikin J-boy yana ƙoƙarin rufeta da duka...duk yanda taso kamo Sofy J-boy ya hana,domin yariga daya shiga tsakiyarsu.
Gudun kada ayi mugun aiki yasa hjy mataer alhj KABIRU mikewa ta jawo Sofy tazo inda take zaune,snn hjy da J-boy suma suka zauna.
Bayan kowa ya koma ya zauna ne hjy matar alhj KABIRU ta tsare Sofy da cewa taji tsoron Allah ta tuna cewa zata mutu ta kwanta a kabarinta ita kaɗai sai kuma halinta ta faɗin gaskiya...
Kuka Sofy tasa duk yanda sukaso Sofy tai bayani Amma taki,gani haka yasa alhj KABIRU cewa"duk su dakata,saida kowa yai shiru snn ya fara bayani,tun daga farkon kiransa da tai har izuwa wanan lokaci.
Dukkansu salati sukasa suna masu sanarwa ubangiji..
J-boy dake zaune sharrkam yai da zufa,hular dake kansa ya cire Yana fifita dake..
Sofy kuwa wani kukan ta sake rusawa haɗi da rikewa J-boy ƙafa tana faɗin na tuba ka yafeni..
Da sauri J-boy ya fisge ƙafarsa snn ya hankaɗeta yana meyi mata Allah ya isa..
A ɓangaren alhj KABIRU da hjy matarsa kuwa sai fama faɗi masa maganganu barasa daɗi takeyi.
Hjy maman J-boy ce ta dakatar da hjy haɗi da bata hakuri snn taci gaba da cewa"idan tai la'akari ba laifinsa bane,domin inda yasa Sofy ce wlh bazai aikata hakan ba...
Da sauri alhj yace"ohoooo faɗi mata dai,ballema wlh babu abinda ya taɓa shiga tsakanina da ita gatanan ma ku tambayeta..tsawa hjy ta daka masa tana cewa"dallah kaimin shiruuu..jin haka yasa hjy cewa"ya isa haka snn ta juyo ga Sofy dake zaune tana faman uban kuka tace"tai masa shiru in ba haka ba wlh yanzu sai taci ubanta ba wani abu bane a gunta..da sauri Sofy ta haɗiye miyau.
Snn hjy ta sake komawa ga J-boy wanda ke zaune be iya cewa"komai ba JIBRIN! JIBRIN!!JIBRIN!!! tace dashi...da sauri J-boy ya amsa da na'am"".
Sau nawa na kiraka?..
"Sau uku hjy.
Idan nina haifeka inaso ka saki SAFIYA yanzu nan...ba J-boy ba hatta jama'ar dake gu saida sukaji wani irin.
Duk da yasan bata kyauta ba amna saida yaji wani iri.
Tou yace"snn ya juya ga Sofy dake zaune yace"ni JIBRIN na saki matata SAFIYA saki ɗaya.. alhamdullhi hjy tace,snn ta juya ga Sofy tace"fice ki bani waje shegiya yarinya kawai,kuma wlh daga yau babu ke babu JIBRIN..gani har a lokacin zata zaune bata miƙe ba yasa hjy cewa"zaki tashi ki fice ko sainaci ubanki..
A sanyaye Sofy ta miƙe tabar gun.tana fita daga gidan hjy kai tsaye gida ta nufa tana zuwa taje ta kwashi kayan sawanta snn ta fice daga gida.
Bayan fitan Sofy hjy taita bawa hjy matan alhj KABIRU hakuri da tai masa uziri hakan ba halinsa bane wannan ma sheɗan ne.
Saida ta dai-dai su bayan su tafi hjy tasa J-boy a gaba da faɗa,inda take shiga banan take fita ba.
Tunda hjy ta fara magana guiwar J-boy na ƙasa hakuri kawai yake bata.
Sofy na fita daga gidan J-boy kai tsaye hotel ta nufa,ita isa tasa aka kawo mata abinci taci snn tai wanka bayan ta fito daga wanka ne bakin gado tasamu ta zauna snn ta sanya hannu ta zare wayarta tana ɗauka number malam ta nimo snn ta danna masa kira.
Malam dake zaune kan sallaya yana lazumi gani kiran Sofy ne yasashi shafa addu'ar da yakeyi snn ya ɗaga kiran da sallama.
Cikin da fara'a suka gaisa bayan su gaisa ne Sofy take faɗi masa duk abinda ya sameta harda sakin da J-boy yai mata.
Salati malam yai ya sanarwa ubangji ya jima yana mamaki hali irin na Sofy,haɗi da cewa"wato dai har abada wanan yarinya bazata daina aikata zina ba.. maganar Sofy ce ya katsesa da sauri yace"na'am ina jinki.
A gaskiya SAFIYA bazan boye maki ba,wanan aiki yafi ƙarfine inda ace bakida igiyar kowa nema da sauki amma zina da aure?,gaskiya ƙazanta da hakki yai yawa..
Kamar yaya Sofy tace"dashi".
Sai dai ki sami wani yai amma baniba.
Tou kawai tace,da sauri ta yanke wayar,tana kashe wayar tai tsaki snn tace matsiyaci ko a tandun mai ƙasa shi haka zai fito bazaiyi arziki ba..

***
Gani waya sukeyi basu haɗu ba yasa mutumi cewa Rukky yanaso su haɗu a yau ɗinna.
Take RUKKy taji gabanta yai mumunar faɗuwa, shiruuuuu tai batace dashi komai ba.jin tai shine yasa mutumi dariya snn yace"nasan tunani kikeyi sabida nace inaso mu haɗu ko?.
Kala-kala da murya tace"eh wlh"
"Allah sarki my baby kada ki damu,duk yanda zanyi zanyi domin gani na kare maki mutunci da darajanki.
Tou Rukky tace,snn yaci gaba da cewa"
abu ɗaya nake buƙata dake.
Inajin ka Rukky tace".
Snn yaci gaba da cewa"zan jiraki ta citily hotel kizo ki sameni anan,sabida gurin yafi sirri kome kikace?.
Tou kawai Rukky tace.
Suna sallama kamar yanda tai dashi 4-30PM ta shirya cikin doguwar riganta ta shadda,saida takai su Muhammed da Muhsana gurin su Khairat snn ta sallami Khadijat da cewa bari naje kasuwa na dawo ba daɗewa zanba.
Tou kawai Khadijat tace"tana me ƙarewa Rukky kallo.
Rukky na fita tasami napep tahau,da yake babu kowa a ciki,ita kaɗai ce kawai yasa Rukky cewa kada ya dauki kowa.duk tana maganar ne a tsorace,da haka har saka kai kusa da in da yai fakin motarsa,yana zaune yana kallon hanya,duk da besan waye a cikin napep din dake dufaresa ba amma jikinsa ya basa cewa"Rukky ce.
Da sauri ya ɗauki waya ya kirata.rukky na gani shigowar kiran sa da sauri ta ɗauki wayar haɗi da sallama.
Kece cikin napep ɗin da nake hange?.
Eh tace".
Ok,sauka a gu,saiki ƙariso da ƙafa.
Tou ta kuma cewa,tana kashe wayar tace ya sauketa agun.sai dai tabiya me napep kuɗinsa snn ta ƙarisa inda take fake da mota,duk rakun Rukky idonsa na kanta har ta ƙarisa,tana ƙarisowa buɗe mata ɗayan gefen yai haɗi da cewa bismillh.
Gabanta ne yasake mumunar faɗi,Amma sai ta danne da bismillh ta shigo motar tana shiga ya rufe motar ta ciki snn ya juya gareta,suna haɗa ido da sauri ta kauda fuska.
Shiko cewa yai wowww!!! My baby na daɗe ina kallon taurari dake sararin samaniya yayin da naga wacce tafi kowace haske a cikinsu,wanan kuwa ba kowa bace sai ke masoyiyata.
Jin nawin kalaman dayake faɗi yasa kunya kama Rukky da sauri taja mayafin da take rufe dashi ta rufe fuskanta..
Dariya mutumi yai snn yace"my baby kunyata kikeji ko?,tou bari mu ƙaresa inda zata zauna muyi hira ko?saida ya ƙara ƙarfin AC ɗin dake kunne snn ya tada motar suka fara tafiya....!!!!!








📚✍️

MAKAUNIYAR RAYUWAWhere stories live. Discover now