MAKAUNIYAR RAYUWA

182 13 5
                                    

*MAKAUNIYAR RAYUWA*
________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________

~DIDECATED TO~
*ANTY FAUZIYA*
   *ƳAR AMANA*

https://www.facebook.com/104534761033461/posts/119016616251942/?app=fbl

         *PART THREE*
              *PAGE 14*

*BISMILLAHR RAHMANI RAHIM*

_____"J-boy na isa wani sabon wasa suka kafa,amarya da ango an cashe sosai,basu kega tashi ba sai bayan goma na dare,washe gari asabar bayan idar da sallah azahar aka ɗaura auren SURAYYA da MUHAMMED JIBRIN wanda ƙanan mahaifinsa ne ya amsar masa auren,bayan isha aka ɗauki amarya daga gidan iyayenta zuwa gidan miji,saida aka fara kaita gidan iyayen J-boy,gidan mahaifiyasa ne farko daga nan kuma sai gidan ƙanin babansa wato baban su RAZIƘA daga nan ba'a tsaya da ita ko ina ba sai gidan J-boy.
   "Daga iyayan amarya har wawayen a babu wanda ya kwana,suna kaita basu ɗauki wani dogon lokaci ba kowa ya watse befi minti biyar zuwa goma da fitan su ba ango ya shago wajan amaryansa Surry".

       ****
Washe gari Yaya Mu'azam yaji labarin iya na asibiti babu lafiya, ba tare daya sanar wa kowa ba bayan ya dawo daga aiki yai wanka shiryawa yai zuwa asibiti gaidata,kafin ya ƙarisa saida ya biya ya siye mata kayan su fruit snn ya ƙarisa cikin asibitin.
  Da sallama ya shiga,lokacin iya na bacci Yaya Bala ne da Khadijat zaune suna hira,ita kuma iya tana bacci.
    Miƙewa Yaya Bala yai daga kujeran daya zaune ya miƙewa Mu'azam daya zauna,shi kuma ya koma bakin gado kusa dakan iya ya zauna,saida ƙamaru ya zauna snn suka gaisa cikin girmamawa haɗi da tambayar yah me jiki?"
   "Jiki da saiki yace dashi,sann Khadijat dake zaune itama suka gaisa haɗi da tambayar jikin Rukky dasu Muhammed"
  "Duk suna lafiya Yaya Mu'azam yace"su jima suna hira snn ya miƙe da cewa"ni zan tafi idan ta tashi a gaidata"duk amsawa sukai da tou zataji insha Allahu"
  Bayan ya Mike hannu ya sanya cikin aljihunsa ya ciro naira ɗari biyar yace"ga wanan babu yawa".
   "Duk suka haɗa baki da cewa"kai haba duk da wanan ɗawainiyar da kai?"
   "Murmushin kawai Mu'azam yai" godiya sukai sosai,har bakin gate Yaya Bala yai masa rakiya snn ya dawo cikin ɗaki"bayan ya zauna ne yake cewa"Kai Khadijat wlh Mu'azam daban yake""kamar yaya?"
   "Dubi fa irin ɗawainiya da yai".
   "Tou ba dole ba,tunda uwarsa ce ummul aba'isin ciwon ta"".. Allah sarki,wlh idan kika bibiya ma besan tazo ta aikita hakan ba".
"Uhm himm tace haɗi da juya ido"tunda ya lura bason maganar takeyi ba,shiru yai be sake ɗaga maganar ba".
    Bayan zuwan ƙamaru ne Yaya Bala ke nuna masa abinda Mu'azam ya kawowa iya"
   "Tsaki yai haɗi da cewa"shi ya sani"
Gani kwana Rukky uku a gida babu ɗaya daga cikin ƴan uwan mijinta da yazo dubata yasa daddy amsar numbar Yaya Bala ya kirasa"
"Yaya Bala na gani numbar daddy da sauri ya ɗaga kiran haɗi da sallama snn ya gaidasa,bayan su gaisa ne daddy ke tambayar abinda ke tafiya tsakani Rukky da ƙamaru"
  "Ijiyar numfashi Yaya Bala yai snn yace"yayi hakuri wanan ba maganar waya bace,amma koma menene insha Allahu zaizo"
  "Allah ya kawoku lafiya yace,snn sukai sallama"
Bayan su gama waya da daddy har ɗaki Yaya Bala yabi kamaru"ƙamaru dake kwance aka kushi three seater gani shigowar Yaya Bala yasa Ƙamaru miƙewa tsaye ɗaki da cewa"Yaya kaine?"
   Eh nine kamaru,hutawa kakeyi ne?"
  "Eh wlh,so nake naɗan samu bacci koda kaɗane"
   Bismillh yace dashi"kasancewar gajeran wando ne a jikinsa saida yajajja yaɗan sauka snn ya zauna"
"Bayan ya zauna ne Yaya Bala yace"ƙamaru wajanka nazo".
Gani Yaya, Allah dai yasa ba wani laifi nayi ba".
        "Dama akan maganar wanna yarinyar ce""ƙamaru najin haka take ya canza fuska,ƙib yai da fuska haɗi da juyawa Yaya Bala baya"
  Yaya Bala yaci gaba da cewa"yanzu iyayenta suka kirani""tou meye kuma,badai aure neba kuma banayi,ko ana dole ne?ni dallah kada a dameni da saki nedai nariga dana saketa to meya rage kuma,ni wlh har ka fara ɓatamin rai,mutum na zaman-zamansa azo masa da wata magana,ni yanzu...Kai yanzu me?"kada a sake zuwa min da maganar waccen banza".. Rukky ce banza?"eh banzace,idan da abinda yafi banza ma zan iya kiranta dashi..har yanzu akwai alamar bincike cikin al'muranka domin daga gani alama gamo kayi,idomin duk wanan abu da kakeyi ba halinka da ɗabi'arka bane"
To Yaya maganar yara kuma,ko suma duk bakaso ne?"
   "Shiruuu yai na wasu lokuta sai daga baya sann yace"eh banaso domin har kokwanto makeyi a kansu"".. Subhanallilahi innallilahi haba-haba ƙamaru yanzu abin naka har yakai ga haka??"
Uhmm yace haɗi da miƙewa,shigewa ciki yai yabar Yaya Bala a wajan"binsa da ido yai haɗi da mamakin canzawar sa". 
   Washe gari aka bawa iya sallama suka koma gida, bayan ƙomawarsu da yamma bayan sallar  la'asar Yayaa ya tasa ƙamaru a gaba zuwa gidan su daddy, daƙar yasamu sha kan ƙamaru suka tafi gidan,tun suna hanya Yaya Bala ya sanarwa Mu'azam gasu nan zuwa"tou Yaya Mu'azam yace,yana kashe waya ya sanarwa daddy da Inna"
   Ko kafin su iso Yaya Mu'azam yai masu shinfiɗa"daddy dake gidan Talatuwa saida ya sanar da ita snn ya fito zuwa gidan inna,"befi minti biyar da shigowa ba sukai sallama"jin salamar sune yaya Mu'azam dake zaune yana wasa da Muhammad saurin miƙewa haɗi da cewa"yarin uncle jirani ina zuwa ko?"
   "Kamar ba dashi akai ba,Yaya Mu'azam na miƙewa Muhammed ya miƙe tare suka fita dubo wanda suke  sallamar"
       "Suna fita Muhammed yai ido biyu da babansa,a guje ya saki hannu Uncle yaje ya kama kamaru haɗi da faɗin oyoyo-oyoyo daddy,rungumesa yai yana faɗin daddy zo muje cikin ummanmu nanan a ciki zo muje wajan ummanmu"
  Kama hannu ƙamaru yai yana ja yana faɗin zo muje wajan ummanmu"karkashe ido ƙamaru keyi haɗi da ƙoƙarin ciro Muhammed daga jikinsa"gani haka tun kafin Yaya Mu'azam ya fahimta da sauri Yaya Bala ya ɗauki Muhammed haɗi da cewa"wato bakasani ba sai daddyn ka ko son"
  Dariya Muhammed yai snn yace"kai ba daddyna bane,Kai daddyn su Khairat da Na'eem ne,juyawa yai ga ƙamaru yana faɗi ko daddy?"
  Dariya Mu'azam yai haɗi da cewa yaro man kaza,yaro ba mutum ba saiya girma"bari naje na sanarwa daddy zuwan ku"
   Ok yace"
Yana shiga tare suka fito shida daddy, Mu'azam na riƙe da tabarma a hannu suna isowa ya shinfiɗa haɗi da cewa"bismillh"
Saida daddy ya zauna snn suma suka zauna,cike da girmamawa suka gaisa da daddy,snn suka gaisa da Mu'azam"Fuskan ƙamaru a ɗaure duk gaisuwar da sukeyi be tanka ba,gani haka yasa daddy miƙe masa hannu haɗi da sallama"
   Ɗauke kansa yai gefe haɗi da noƙe hannunsa ciki"Yaya Bala dake zaune kusa dashi,ƙara matsawa yai gab dashi,ba tare dasu daddy da Mu'azam su gani ba yake dangwalo ƙamaru haɗi da magana dakai alamar ya gaishesu"
   Ba tare da ƙamaru ya kawo kome a zuciyarsa ba yace"lafiya kuwa mutumina?"
   Yaya Bala yai murmushin yake haɗi da cewa"bayajin daɗi ne, daƙar ma ya it's zuwa nan"Allah sarki sukace,snn daddy ya sauke hannunsa"
Tashi Mu'azam yai daga inda yake zaune zuwa kusa da ƙamaru,hannu yasa ya dafe masa kafaɗa haɗi da cewa"Sorry my friend,ina fatan dai kasha magani kafin kafito ko?"
  Uhmm kawai ƙamaru yace"
Daddy dake zaune ƙarewa ƙamaru kallo yai yasan akwai abinda ya ƙudurta a zuciyarsa,be sake bi ta kansa ba,ya beda hankalinsa ga Yaya Bala"da cewa"dalilin kiran da nayi maka jiya shine tunda yarinyar ga tadawo babu ɗaya daga cikinku da yazo dubata bare ayi maganar komawarta ɗakinta""Eh gaskiya ne daddy,amma ayi hakuri wlh uzururukane sukai min yawa yasa"
Haka ne tou Allah ya shige mana gaba"duk suka am'sa da amen"
Snn daddy yaci gaba da cewa"a gaskiya banji daɗi abinda ya faruba duk da dai ansan yau da gobe,tsakani harshe da haƙorima an saɓa bare zaman tare,a gaskiya zan iya jure komai amma banda maganar duka,idan laifi tayi maka kai namiji ne kanada hanyoyi da dama wanda zaka hukuntata dashi basai ka duke ba".
  Gaskiya ne Yaya Bala yace"snn yaci gaba da bada hakuri"
Daddy yaci gaba da cewa"wlh banji daɗi ba kwata-kwata Dan Allah a kiyaye,ga matarka nan da yaranka ka ɗauketa ku tafi, Allah ya ƙara hakurin zama".
   Yaya Bala dake zaune shiruuuuu yai yana me nazarin ta inda zai fara yi masu bayani babu aure a tsakaninsu,can wani tunani ya faɗo masa,da sauri yace"tou daddy mugode sosai Allah ya ƙara girma"
Kai ƙamaru ga matarka nan sai ka kiyayi gaba"""wahh badai niba domin tuni nariga dana datse igiyar dake tsakanina da ita,dan haka taje Allah ya gama kowa da abokin arzikinta""har ya yunkura zai miƙe da sauri Yaya Bala yasa hannu ya jawosa yadawo ya zauna"daga daddy har Yaya Mu'azam babu abinda suke furtaea sai innallilahi wa'innailailin raju'un, Mu'azam dake zaune ji yayi kamar ruwan zafi aka watsa mafi,take zuwa irin zufa suka fetse masa yanda kasan wanda yafito".
  Yanda kasan zararre ƙamaru ya koma yana cewa"tou meye kuma aure ne dai banayi nariga dana saketa tun ba yauba,muguwa azaluma macuciya insha Allahu sai Allah ya sakami mazinaciya kawai"cikin zafin rai Mu'azam ya tashi ya shako ƙamaru haɗi da nunasa ɗan yatsa yana meyi masa gargaɗi da kada ya kuma faɗin hakan"
    Duk miƙewa sukai suna ƙoƙarin cirewa Mu'azam hannu a wiyar ƙamaru"
   Hannu ƙamaru yasa ya igije Mu'azam yai snn yace"an faɗi ance mazinaciya fasiƙa ƴar wuta"..wani wawan mari Mu'azam ya kaiwa ƙamaru,wanda su kansa besan da zuwansu ba,sai saukarsu da yaji"cikin zafin zuciya Mu'azam ke magana duk abinda zakai Kai amma kada ka sake ka ɗorawa ƙanwata laifin da bataji ba bata gani ba"""ubanwa yace"sharri nayi mata?"
   Take agun Mu'azam yace"kada ka kuskura ka zaganmi iyaye domin idan har kai kuskuren aikata haka ina me tabbatar maka zan iya aikata komai akan su"
   Gani suna ƙoƙarin komawa su haɗi yasa daddy kamo Mu'azam shi kuma Yaya Bala yakama ƙamaru yana jansa yana yi masa faɗa akan abinda yai be dace ba""Cikin masifa yace"dallah ni ka kyaleni na faɗi abinda ke raina,wanan ai rainin hankaline ta Yaya za'a dakeni kuma a hanani kuka,mazafa takebi da aurena akanta..ihuuu da Mu'azam yai ne haɗi da fisgewa daga hannu mahaifinsa yasa Ƙamaru katse maganar da yakeyi"ita kuma inna dake cikin gida a guje ta fito haɗi da tambayar ihun me nakeji haka?"
   Ƙamaru yaci gaba da memeta kamar mazinaciya fasiƙa mebin maza"
Innallilahi wainnaalehe raju'una Inna ke faɗi haɗi da cewa yau me zanji me zangani"
Eh maza takebi da aurenta,dan haka taje na saketa saki uku,ni ban iya zama da fasiƙar mace ba""ihuuu Mu'azam yai haɗi da tsalle sai jikin ƙamaru"nan suka kama kakula, Muhammed dake tsaye kuka yasa haɗi da komawa cikin gida a guje yaje yana sanarwa Rukky yana kuka,daddy da Uncle suna dambe"Aguje Rukky ta fito,dai-dai Talatuwa itama ta fito, duk maganar da sukeyi a kunninta kasancewar katanga kawai ya rabasu"
Gani irin abinda ke faruwa rusawa da kuka Rukky tai haɗi da cewa"na shiga uku,yau mezan gani, dukkansu su biyun babu wanda tai ƙoƙarin karewa domin kowa nada nasa muhimmacin a gareta,kuka kawai takeyi haɗi da kiran sunayensu da su bari"
  "Babu ɗaya daga cikin su day saurareta,bare yasan tanayi"
    Shima Muhammed kuka yakeyi haɗi da kiran daddynsa, musamman ma yanda yaga ana dimgansa"
   Cuku-cuku suke suna dambe daga Yaya Bala har daddy suyi iya ƙoƙarinsu wajan gani su rabasu amma su kasa"Gani yanda Allah ya bawa Mu'azam sa'a yake jimgan ƙamaru yasa Inna bata damu ba,amma da alluran sojan ta motse wani irin kuuuwa yasa haɗi da yunkura take ya juya Mu'azam ya koma ƙasa,nushi kawai yake kai masa kamar wanda be taɓa sani inda ya fito ba"wani nushin da ƙamaru yai masa yasa bakin Mu'azam fashewa gani yanda jini ya burrrso daga bakin Mu'azam Inna tasa kuwa haɗi da cewa"wayyoooo na shiga uku ɗan shegiya zai kashemin yaro"faɗinwa tai ƙamaru ɗin ta cukwai-kwaiyesa da zaninta ya ƙasa gani gabansa bare yata wajan dukan,yaci gaba da cewa"shege ɗan banza yau saina ramawa yarona ɗan shegiya wanda basu gaji mutunci ba".
Wawurota ƙamaru yai ya yarfeta agefen""yiiiihuhuuu shege dan banza zai kasheni"kafin ya kuma meda hannunsa jikin Mu'azam tuni ya igijesa ya faɗi a ƙasa ya miƙewa,suna cikin haka saiga Yaya Sani yadawo a masge gani abinda ke faruwa ba tare daya tsaya jin yanda akai ba,kawai tsintar uwarsa yai yarfe a ƙasa"jarrrrdubin ƙwau yace"da sauri ya shiga daga ciki yaje ya ɗauko zabgegen wuƙarsa a guje  ya tunkaro ƙamaru dake ƙoƙarin kwace jikinsa daga riƙon da Yaya Bala yai masa"Yana cewa"mu za'a kawowa during uwa?rabu ɗan shegiya yai saidai uwarka ta haifi wani,ɗagawa yai zai kaiwa su Yaya Bala ihuuu duk sukasa daga Inna har Talatuwa,a guje Inna taƙaƙume tana ihu"da sauri daddy da Yaya Mu'azam sukazo suka kwace wuƙar daga hannunsa"shiko ƙamaru tsayuwa yai yana faɗi aida kun barsa yazo"nandai aka haɗu hade da jama'ar da suke tafiya duk aka haɗu aka rabasu"da ƙar aka lala I Yaya Sani zuwa cikin gida,koda ya shiga be daina ɗurawasu ƙamaru asha riya ba"
   Gani har a lokacin Rukky bata daina kuka ba yasa Inna hayiyiƙeta da masifa da bala'i haɗi da cewa duk ita taja,gashi sanadiyar ta za'a kashe mata yaro,wlh inda wani abu ya sami Mu'azam babu abinda zai hana ta rama akanta"snn kuma saita faɗi mata gaskiya akan maganar da ƙamaru ya faɗi gaskiya ne ko kuwa?".
    Kuka lawai Rukky keyi ba tare data bawa inna amsarta ba"gani haka yasa Inna kwarrrrma uwar ihu ta haɗi da rufe Rukky da duka inda take shiga banan take fita ba"
  Daddy dake wankewa daddy baki da Talatuwa da take zuɓa duk kan Inna suka dawo,bayan su kwace Rukky daga hannunta sukaci gaba dayi mata faɗi da cewa"be kamata tayi haka ba,kamata yai tayi bincike kafin ta ɗauki hukunci snn ma idan banda abinta abinda batai tana layi ba shine yanzu da aurenta zatayi?"""Hayayyaƙe Talatuwa tai da masifa tana cewa"Dallah jacan banza almura makira baƙar alguguma macuciya,waima ba nace ki daina shiga harkata ba?.Uhmm Allah ya ganar dake"""ya ganar dake dai,banza kawai,kuma wlh daga yau sai yau idan ina magana da yarana kika sake sanyami baki sai kinyi mamkin abinda zanyi maki,,,
   "Daddy dake tsaye yace"waike lafiyarki kuwa?""'dallah rufemi baki,duk bakun ba kenan,baƙaƙen algugume snn ta juya ga Rukky taci gaba da cewa"ke kuma yau ɗanna zaki barmi gidana domin bazan iya cin gaba da zama dake ba"Zina fa,kinko san sharrin zini,tou bazai yuwu idan masifa yatashi faɗo maki ya haɗa dani ba,shiga ɗaya tai cikin zafin nama ta kwasowa Rukky kayanta tazo ta watsa mata haɗi da cewa",ga tsiyarki nan maza kwashe ki ficemi daga gida...wanane kuma baki isa ba,sai dai koke ki fita ki bar mata gidan..cikin masifa inna ta Hayayyaƙe daddy da cewa"wlh baka isa ba,wlh kayi ƙarya,domin babu inda zani,kae kuma maza tashi ki ficemi daga gida tunda ba gidan ubanki bane"Inna na maganar ne haɗi da hankaɗe Rukky,kayanta kuma da ƙafa takeyi mata hurgi dashi..
  Mu'azam dake zaune yana tallafe da kansa kai kawai yake kadawa sabida saran da kansa keyi yasa bazai iya magana ba"Ran daddy ya ɓaci,cikin zafin rai besan lokacin daya kaiwa Inna mari ba haɗi da cewa"idan kika kuma kwatankwacin irin abinda kika aikata yanzu a bakin aurenki... innallilahi Talatuwa tace"da sauri tasha gabansa haɗi da cewa"ba'ayi haka ba,insha Allahu Rukky bazata zamo sanadiyar mutuwar aurenku ba,juyawa tai ga Rukky haɗi da cewa,zo muje gidana akwai ɗaki ɗaya da babu kowa saiyi zamanki a ciki,duƙawa yai ta tattarawa Rukky kayan da Inna ta watsar mata bayan ta gama tattarawa ta miƙe haɗi da ɗaukar Muhasana ta cewa"Muhammed zo muje"Oho!!dai Inna tace"snn taci gaba da zage-zagenta".
   Gani har a lokacin bakin Mu'azam be daina zidda jini ba yasa daddy cewa"zo muje kamis,kemis dake kusa da gidansu suka tafi,saida aka wanda bakin aka sanya masa maganin da zai tsaida jini haɗi Dana sha snn suka dawo gida.
    A ranar magana ta karaɗe unguwa kowa da irin abinda yake faɗi,hatta ƴan majalisar su Mu'azam sunaji zuga sukai suka zo gaishesa haɗi da nuna masa rashin jin daɗi abinda sukai shida ƙamaru ɗin"
   Su jima suna hira snn sukai sallama, suna barin wajan Mu'azam wasu daga cikinsu suka ƙarisa gidan kamaru,shima su nuna masa nasa kuskuren fiye da tunani me tunani daga ƙarke har abin ya zame masu faɗa, ƙamaru yace"babu ruwansu dashi,daga yau duk irin abinda zaiyi bece kowa yasanya masa baki ba,Dan haka kada kowani shege ya sake zuwa masa da maganar be kyauta ba,hakan da yai shine dai-dai idan dah abinda yafi hakama zaiyi"
  Ɗaya daga cikinsu yace"tou shi kenan tunda yaka yace"babu ruwansu dashi"""eh babu ruwanku dani,kada wanda ya ƙara shiga harkata"jin yace haka suka jikinsu suka fice daga gida haɗi da cewa"akwai ranar kin dillaci,da ƙafarka zaka biyomu"
     Washe gari daddy da Mu'azam suka tasa Rukky a gaba data faɗi masu gaskiya abinda ƙamaru ya faɗi akanta"
      Tunda daddy ya fara magana babu abinda Rukky keyi inba kuka ba,har ya ƙare magana"gani irin kukan da takeyi ne yasa Mu'azam amsar bakinta da cewa"duk da dai baka shedan Dan Adam amma wlh daddy ban yarda Rukky zata aikata abinda ƙamaru ke zarginta dashi ba,sai dai ko shiga tsakaninsu akayi,shi kuma beyi kyankyawan bincike akai ba ya tashi ya yanke hukunci, Alhamdullhi da abin yazo da haka, Allah ya fitarwa kowa da hakkinsa,idan Rukky ce ta cucesa Allah ya saka masa,idan kuma shine ya cuceta Allah yai gatgawan saka mata"
      Amen daddy yace"
    Snn lokacin ne daddy ya sanarwa Rukky da maganar saki"Take taji kamar an watsa mata ruwan zafi, wani sabon kuka tasa haɗi da faɗin innallilahi wa'inna'ilaihin raju'un Alhummah ajirni fi musibati..take ta nemi natsuwarta ta rasa,kukane yaci ƙarfin ta wanda yasata ƙasa ƙarisa addu'ar da takeyi,gani haka daddy yace"ta tashi ta shiga daga ciki,daren ranar kusan kwana Rukky tai tana kuka har saida taji kanta ya fara amsawa snn tai hakura da kukan"
    Bayan kwana biyu Yaya Bala yazo har zo har gida yabawa daddy da Mu'azam hakurin abinda ɗan uwansa ya aikata,snn suka tsaida maganar yara,Yaya Bala yace"taci gaba da riƙesa a hannunta har zuwa lokacin da zatai aure saiya amshesu,shi kuma duk abinda Allah ya hure masa zai rinƙa kawo mata.
   Maganar kayan kuma duk lokacin da kuka shirya kwashewa ku sanar dani"
  Tou yace snn sukai sallama,bayan ya koma cikine yake sanarwa Talatuwa duk yanda sukai da Yaya Balan"""!!!!!!
Sorry 4d typing error

MAKAUNIYAR RAYUWAWhere stories live. Discover now