MAKAUNIYAR RAYUWA

139 7 5
                                    

_*MAKAUNIYAR*_
             _*RAYUWA*_

*_🌈KAINUWA WRITERS✍🏻 ASSOCIATION_*🤝🏻

_*fcbk group*_
_*mmn uswan*_
*page Hauwaszaria*

https://www.facebook.com/379407779489539/posts/518531808910468/?app=fbl

editing is not allow⚠

         *PAGE 13*
                 *PART 2*

_*BISMILLAHI RAHMANI RAHIM*_

________"Da sallama Kharat ta shiga ďakin Rukky.Muhammed ne ta tarar dasu shida Muhsana suna wasa.tambayarsu tai ina mamansu?"Muhammed yace" Ummanmu tana kici,zomuje na kaiki.
"Kama mata hannu yai zuwa ciki gun Rukky."ganisa tareda Khairat yasa Rukky tambayar Khairat da lafiya?"Khairat tace" mamanmu ce tace naraki"
"Tou,jeki kice mata ina zuwa.
"Rage injin risho tai sannan tacewa su Muhammed su jirata tana zuwa,janyo kofar kici ďin tai ta tarsu a falo suna wasa sannan taje jin kiran Khadijat.da sallama ta shiga falon.zama tai haďi da cewa gani"
"Cikin zumuďi Khadijat tace" hmmm kin san me?amma nasan kema kinsamu labari ai"...
"Labarin me kuma Khadijat?"
"Abinda ya faru mana"
"A'a wlh banji ba,wani abunne ya faru?"
"Keee kada ki medani k'aramar yarinya mana.bayan koda abin yafaru akwai mijinki agu".
"Khadijat kenan ďan mijina nagu  ai bezama lallai ace naji ba.idan kuma kina tunani zai faďimi ne wlh K'amaru ba haka yakeba.ni bema nunami wani abu ya faru ba".
"Kam lallai kam.tou dai ba komai bane,ina frg ďin daya siyewa iya?"
"Eh".
"Batasan duk abinda take faďi ina mak'e ina jinta ba.bayan wanda suka shigo dashi su fita." fitowa tai tsakar gida tana rawa da murna har cewa tai gwamma datai haka,inda badan tai haka ba da basoya mata zaiyi ba.sannan tace wai saitasa K'amaru ya rabu dake ya auro mata matar waike ba ďiyar mutumci bane...
"Allah sarki iya kenan.tou frg ďinma da take magana akai nifa nasa K'amaru yasiya mata shine take faďin haka.dan Adam kenan..." nifan duk abinda iya zatai maki harga Allah bana gani laifinta.laifinki nake gani.
"Kuma nasan bakomai ne yasa kike haka sai dan niman dingin zama.tou bari kiji idan iyace wlh ko maccah da madinah zaki goyata ki kaita ba gani zatai ba,kuma hakan bazai hana idan wani abu ya haďaku taci maki mutunci ba.
Koshi Baffa tanaji yaketa yabonki wlh ko a jikina banyi niyyar ba kuma dan wata tayi bashi zaisani nayi ba.domin bazan zauna naci kashin k'aton banza ba.idan aikin lada nake nakeso mai zai hana nakoma gida gun uwata naje can nayi tasami  albarka kwando-kwando ba tsohun wasu ba.
Ni bance kidaina yi abinda kikeyi  masu ba tunda ke kikasa kanki,amma kisani idan kinayi domin samo shigane wlh bazaki ta6a samu ba.
Idan ma iyace sai abinda ta mance.
"Duk maganar da Khadijat keyi ido kawai Rukky ke binta da ido takeyi, ba tare datace da ita komai ba.
"Khadijat taci gaba da cewa"buhun uban nan,tsofan yaci ubansa,banyiba kuma bazan ba.
Idan banda k'addara da kuma Soyayya mezanyi da irin wannan zuri'ar...jin haka yasa Rukky mik'ewa haďi da cewa" bari naje na duba abinci nadawo.
Da sauri Khadijat takamawa Rukky hannu haďi da cewa"Rukky nasan halinki batun yau ba.kada ki kullaceni a zuciya ban faďi haka da wata manufa ba.tawa ra'ayin nake faďi.kinsan kowa da ra'ayinsa.amma inaso kin san cewa iya ba irin sauran iyayen mijin ďinnan bane,iya ta wuce yanda kike tunani.
Sannan kuma ina me baki shawara.wata damace Allah ya baki idan har kikai wasa da wannan damar shi kenan.ita dama sau ďaya take zuwa bawa a rayuwa.yanzu ne lokacin da ya kamata kisan abinda kikeyi, kiyi tanaji duk abinda K'amaru zai baki kada kisa a gaba kici.tarawa zakiyi ki taimaki mahaifiyarki da yan uwanki.bance ki hanasa yiwa yan uwansa ba,amma inaso kisani idan daďi yazo ananne suke nuna shinasune amma idan wahala yazo duk darewa zasuyi dan haka kinsan abinda kike ciki.
Koda ďaukarki yai kuka tafi ki kama kanki kada ki mance daga irin zuri'ar da kika fito..
Tou kawai Rukky ce faďi har Khadijat ta gama bata shawa sannan tafice daga ďanki,zuwa ďakinta.bayan ta zauna shiruuu tai maganar Khadijat ne kawai ke mata yawo a zuciya.

Ana gobe K'amaru zai koma Ondo inda aka turasa.
siyayyar kayan abinci yai masu sosai.duk abinda yasan zasu buk'ata saida ya tanada masu.
Washe tunda safe K'amaru yaje tashar zu6a yasiye tiket sannan ya koma gida kafin magrib kuwa duk yariga ya sallami wanda zai sallama yana idar da sallar magrib  ďakin iya yaje domin suyi sallama.
Nasiha sosai iya tai masa da fatan samun nasara agun aiki.
Su jima tana yimasa nasiha sannan sukai sallama ya tafi ďakin Baffa.
Shima Baffa nasiha yai masa haďi da tunatar dashi,idan yaga guri yazo ya ďauki iyalansa.
Insha Allahu K'amaru yace wa Baffa sannan sukai sallama.
Yana komawa ďaki be tsaya 6ata wani lokaci ba sabida suriga da suyi sallama da Rukky.
"Akan bayan wata uku zaizo ya ďauketa su tafi tare.
"Yaya Bala ne yai masa rakiya zuwa tasha,suna isa dai-dai da anfara arrange kaya cikin buk kafin mutani su shiga.da yake bashida wani kaya daga shi sai jakarsa ta ratawa haka yasa suka koma gefe suna jiran agama jama'a su fara shiga.
Bayan awa ďaya passenger's suka fara shiga.k'arfe goma dai-dai motar ya tashi zuwa Ondo hannu yaya Bala ke ďagawa K'amaru yana yimasa bye bye har saida motarsu yai nisa sannan ya sauke hannu ya kami hanyar gida.
Wannan tafiyar ba irin wacce bane.domin daren ranar Rukky batai bacci ba.tun tashin su suka fara chating itada K'amaru.su ďauki lokaci me tsayi suna hira.shiruuu ta K'amaru yajine yasashi rufe data ďinsa.bacci ne ya ďauke Rukky,ita kanta batasan lokacin ba.
K'arfe bakwai na safe K'amaru suka isa Ondo state.
Bayan fitowarsa ne yakoma gefen titi yana niman taxi da zai kaisa office ďinsu.
Kamar daga samu yajiyo muryan Wugochuku yana kwaďa masa kira da  kamalu.daga haka duk yawanci mutani daya zauna dasu a river lokacin treining suke kiransa.
Ajijice ya juya.gani Wugochuku ne yasa K'amaru rugawa a guje yaje suka rumgumi juna suna marna haďi da tambayar junansu nan aka turosa?"
"Eh K'amaru yace"
"Sake jefawa Wugochuku tambaya yai da yaushe yazo?"
"Isowata kenan Wugochuku yacewa K'amaru.
Nan K'amaru yace" shima isowarsa kenan.
A lokacin ne suka gano ashe mota ďaya suka shiga batare da susani ba,sabida yawan passager ďin dake cikin motarta.
Niman taxi sukai wanda zai kaisu office ďinsu. Suna tafe suna hira har sukai isa.
Suna isa suka k'arisa cikin office ďin,cikin girmamawa suka gaida ogansu haďi da sara masa irin tasu ta sojijo sannan suka mik'a masa postin letter.yana buďewa ya karanta bayan ya gama karantarwa ne ya ďauko dan k'arami takarda yai rubutu sannan ya mik'a masu haďi da address ďin barack
Godiya sukai sannan suka fice daga office ďin.
A ranar sukai komai basu samu wani matsala ba sabida ranar aiki sukaje.
Suna barin office wani taxi suka sake ďauka wanda yasan garin,suka faďi masa sunan inda zai kaisu.
"Take yace yasan guri.abuk suka zuba kayansu sannan suka zagayo suka shiga motar zuwa barack".
"Suna isa suka sauka a mota bayan su biya mai taxi kuďinsa suka sauka haďi da ďaukar jakarsu suka k'arisa bakin gate.
Wasu sojiji da suke tsaye a bakin gate ďin da alama masu gaji ne tambayarsu sukai daga ina?"
"ID card suka fito dashi daga aljuhunsu suka nuna masu aannan suka barsu suka shiga daga ciki haďi dayi masu sannu da zuwa"
Koda suka isa ďakunan da aka basu duk akwai mutane a ciki.anriga yaji masu Transfer amma posting letter ďinsu beriga ya fito ba yasa basubar ďakunan ba.
Wani ďaki guďa ďaya shine kawai babu kowa a cikin.gani haka yasa suka sauka a cikin har zuwa lokacin da mutane dake ďakunan zasu bar ďaki su kuma su koma cikin.
Gani ďakin babu komai yasa bayan su huta suka fita zuwa kasuwa.
K'amaru ya siye katifa mai inchi goma shabiyu.haďi da buhun shinkafa da indomie"shi kuma Wugochuku ya yasiye kayan miya dasu tukunya da gass.suna barin kasuwar saida suka biya sukai reple sannu suka k'arisa guda.
Saida suka isa gida sannan suka tuni basu siye banbun ruwa ba da bokati.dole Wugochuku yasake komawa kasuwan."shi kuma k'amaru ya tsaya domin yi masu abinci.
Be daďe ba yadawo dai-dai lokacin K'amaru yariga daya gama girki.zama yai sukaci.sukaci suna hira.suna cikin ci kenan saida kiran Rukky yashigo wayar k'amaru"
Ďagawa yai haďi da sallama,bayan su gaisa ne yake faďi mata duk yanda aikai harma bata wayar yai suka gaisa da Wugochuku sannan sukai sallama..

****
Bayan sati biyu da auren daddy Talatuwa ta shirya zuwa gidan su hjy domin duba jikin Basik.kafin ta tafi saida ta shiga gun inna ko tanada sako.
Da sallama Talatuwa ta shiga gidan.lokacin inna na tsabar gida tana wanke-wanke.
Duk sallamar da Talatuwa keyi inna naji amma taki amsawa.saima wani dogon tsaki da taja haďi da cewa"shegiya dubeta dallah harda wani sallama saikace tasan darajar sallamar da taleyi.maciya amana kawai.
Duk maganar da inna keyi Talatuwa najinta."itama tasan tanajine yasa ma tak'ara value ďin muryanta take maganar da k'arfi tanayi tana kallonta.babu alamar tsoro ko shakka a indon inna......!!!!!!!







Comment
              N
          Share


📚✍

MAKAUNIYAR RAYUWAWhere stories live. Discover now