MAKAUNIYAR RAYUWA

134 11 7
                                    

_*MAKAUNIYAR*_
             _*RAYUWA*_

*_🌈KAINUWA WRITERS✍🏻 ASSOCIATION_*🤝🏻

_*fcbk group*_
_*mmn uswan*_
*page Hauwaszaria*

https://www.facebook.com/379407779489539/posts/518531808910468/?app=fbl

editing is not allow⚠

         *PAGE 8*
                 *PART 2*

_*BISMILLAHI RAHMANI RAHIM*_

_______"Emargercy room suka nufa da ita."J-boy dake biye dasu a baya harya sa kai da niyyar shiga ďakin da sauri ďaya daga cikin nurses ďin ta dakatar dashi daya tsaya daga waje.
"A dole yakoma da baya"
"Bayan su shinfiďata ne likita yazo dubata,likita na shigowa dukkani nurse da suke tsaye a kanta suka kauce suka basu guri.
" suna fita Sofy ta mik'e zaune haďi da cewa"dr"
"Cike da mamaki yazuba mata ido batare daya amsata ba.
"Ko kallo idansa batai ba taci gaba da bayani daya rufa mata asiri kada ya faďiwa mijinta cewa k'arya takeyi,akwai da lilinta nayi haka.
" idan har yai abinda ta sanyasa zata biyasa ko nawane.
"Shidai shiru kawai yai yana kallonta cike da mamaki,can daga baya kuma beyi mamaki ba sabida mata da yawa susha zuwa mata da aiki irin haka.
" ba tare dayace da ita komai ba yajuya yai ficewarsa daga ďakin.
"Binsa da ido Sofy tai,cikin zuciyarta tana tambayar kanta" tou me likitanga yake nufi.kardai ace tonami asiri zaiyi?.
"Kai tsaye ďakin yara meenal ta nufa da Basik batare data jira J-boy ba,sabida bata kanta yakeba takan Sofy yake.
"Tana shiga nurse suka amshisa haďi da basu taimakon gaggawa,sannan suka shinfiďata.
"J-boy dake waje yana jiran fitowar likita.tana hango fitowarsa da sauri yaje ya taresa da yaya jikin nata?"
"Tana can ana bata treatmet kawai yace,sannan yai shigowarsa"
"Sofy dake zaune tsuruuuu tai tana me tunani makomanta.
"Zooo kawai taji an turo kofa,wata yarinyace yar madaidaiciya tashigo hannunta ďauke da drip haďi da allurai.
Cikin girmamawa ta gaida Sofy da jiki sannan ta umarceta data kwanta,tana kwanciya ta jona mata ruwa sannan tai ficewarta.
" J-boy na gani fitarta da sauri ya tareta da zan'yi shiga na dubata?.
"Me zai hana tace dashi"
"Cikin rawar jiki ya shiga." Sofy najin anturo kofa da sauri ta rumtsa idanta kamar me baccin gaske.
"Bakin gado J-boy yaje ya tsaya hannu yasa yana shafe mata gefen fuskanta haďi da kiran sunanta yana meyi mata sannu"
Yakai sama da minti biyar a haka sannan ya fice daga ďakin zuwa gun su Meenal.koda yaje ďakin Basik yariya da tasamu bacci sakamakon allurai da magugunar da suka bashi.
"Gefensa meenal ta zauna tare da zabga uban tagumi.idanuta na kansa ko k'ibtawa batayi.
"Dan k'arami katin magani dake hannunta ne take masa fifuta dashi.
" Sallamar J-boy ne yakatseta,ba tare data juyaba ta amsa  da ameen.
"K'arisowa yai bakin gadon haďi da tambayar yaya jikin nasa?.
"Shiru tai bata tanka saba.
"Nan J-boy ya fara sambatu yana cewa" wlh inacan nida likita muna k'ok'arin wajan gani an ceti rayuwarta ne yasa kika jini shiru.amma yanzu alhamdllh harma tasamu bacci.
Yanzu haka tanacan tana bacci,shine nace bari nazo na dubaku.
"Jin nasan dai da sauki ko?"
"Uhmm kawai tace,sabida takaici bata tanka masa ba,cikin zuciyarta kuma tana mamaki yanda yanzu-yanzu ya canza sai kace bashike kuka ďazu ba amma cikin k'ank'ani lokaci ya canza.Allah ya kyau kawai tace".
"Hannu J-boy yasa a aljihunsa da niyyar ďaukar waya,a lokacin ne yatuna a gida ya barosa.subhanallhi yace sannan yace wa meenal ina zuwa,bari naje naga likita daga nan zan lek'a Sofy bayan na dubata zan tafi gida na rufe maybe na biya na sanarwa hjy,idan kuma ban samu biyawa ba zanmata waya na sanar mata kawai".
"Yana gama maganar yai ficewarsa,ido kawai meenal ta bisa dashi.
Yana fita ofishin likita yaje bayan suga juna likita yai masa bayani da zaiyi masa sukai sallama J-boy ya fice zuwa ďakin Sofy, a yanzu kam baccin gaske takeyi.gani haka yasa  J-boy janyo mata kofar a hankali yana zuwa inda yai fakin ďin mota shigewa yai haďi da fisgarta a guje yabar asibitin.
"Befi minti biyu zuwa uku da fitar J-boy daga ďakin saiga wata nurse ta shigo duba Basik.bayan ta gama abinda zaitai ne harta juya da sauri meenal ta dakatar da ita.dawowa tai da bayan,bayan ta dawone meenal ta rok'eta data ara mata waya tai plashing.murmushi tai haďi da sanya hannu cikin aljihunta ta ciro waya ta mik'awa meenal haďi da cewa"gashi"
"Da yake tariga data rik'e no hjy akai,kawai sanyawa tai ta danna mata kira.lokacin wayar yana kusa da hjy,gani bak'on no ne yasa bata ďaga wayar a lokacin ba saida akai kira kamar sau uku.ana ukun ne ta ďaga wayar da sallama.
"Cikin girmamawa ta gaida hjy.jin muryan meenal yasa hjy tambayarta ta canza no ne?"
"A'a tace,sannan take sanar da ita abinda yafaru"
"Innalillahi wa'inna'ilaihim raju'un hjy tace.haďi da tambayar garin yaya hakan ya faru?"
"Shiru meenal tai bata bata amsar tambayarta ba.
Katse wayar hjy tai haďi da mik'ewa daga zaune da take"
"Mik'awa nurse ďin wayarta tai haďi da yi mata godiya.
" befi minti goma da sallama da hjy ba saigata tayi sallama ďakin da suke"da sauri meenal ta mik'e da sannu da zuwa".
"Bata tanka ba,kai tsaye gun Basik ta nufa.tana ganisa fashewa da kuka tayi haďi da tambayar garin yaya suka k'onasa?"
Duk irin rantse-rantser da meenal taiwa hjy,amma hjy taki yarda.
Inda take shiga banan take fita ba.kuka kawai meenal keyi.sai da hjy ta k'are faďarta sannan take tambayar garin yaya hakan ya faru.sannan kuma ina taje dahar yaje ya jawo cattle ďin ruwan zafin?"
"Nan meenal ta zaiyan wa hjy iya abinda da tasani.tsaki hjy tai haďi da cewa"ba komai ne yajawo haka ba illa sakaci irin nata,idan ba sakaci ba da sakarci ba Basik guda nawa yake da zata barsa a falo shikadai koba komai hakan ya nuna baya samu kyankyawar kulawa daga gareta.
Shiru meenal tai batace komai ba.
" ina SAFIYAR take?"
"Tana can ďakinta"
"A fusace hjy ta fice daga ďakin zuwa ďakin Sofy.
" J-boy na dawowa ďakin Sofy ya shiga,dai-dai lokacin ba falka.gani J-boy kusa da ita,yasata fashewa da kuka haďi da yunk'uwara ta mik'e, cire drip ďin dake hannuta tana k'ok'arin sauka daga gadon.
"J-boy dake tsaye k'ok'arin rik'eta yakeyi haďi da tambayar ta ina zata?"
"Cikin kuka take kiran sunan Basik.zanje naduba Basik ne,wayyo Allah Basik Basik ďina"da sauri J-boy ya kamota ya rungumeta.ita kuma tana k'ok'arin fisgowa a dole zataje ta dubosa.har cea take" dan baka barni naje na gansaba wlh komai zai iya faruwa.zan shiga wani hali,ka varni kawai".
"Cikin zuciyarta kuwa cewa take ai banso ya kai wannan lokacin da raiba.shegen yaro me taurin rai kawai.
"Jin abinda take faďi yasa J-boy cewa" ki kwantar da hankalinki kinga bakida lafiya ko?niriga dana gaya maki Basik yanan lafiya yanzu da hakama bacci yakeyi.ki kwantar da hankalinki plss my dear.jin haka yasa Sofy kwantar da kanta a k'irjin J-boy tana hawaye.
Kamata yai ya zuwa gado bayan ya zaunar da itane.
Bayan ta zauna ne ya sanya hannu ya kwaso mata k',afafunta da suke lilo zuwa kan gadon sannan ya kwantar dq ita a hankali kamar wata kwai haďi da faďin sorry ko.
Bayan ta kwanta ne yafara tambayarta yanzu inane yake mata ciwo?"
"Cikin shagwa6a tace" babu ko ina,naji sauki nidai da kabarni naje na gano jin son ďina ko zan samu kwanciyar hankali.
"Ooooo baby kiji da kanki kawai kinji"
"Nan ta fara shure-shure da k'afa haďi da yi masa k'ananan kukan shagwa6a,daya barta taje.
"Gani haka yasa J-boy sunkuyowa suna kallo juna ido cikin ido,k'iris ya rage fuskokinsu ya haďime da juna.
"A hankali yake hura mata ido,gani da fara yi masa murmushi yasa J-boy yi mata raďa.dake suka busa da dariya haďi da rungumeta...
"Babbb kawai sukaji an banko kofa.da sauri ya gaďa daga kanta.gani hjy ce yasa hjy cewa" hjy sannu da zuwa".
"Wani irin hankaďa hjy takai masa wanda ya sashi haďuwa da bango.
"hannu hjy tasa ta fisciko Sofy dake gado zuwa k'asa sannan tahau dukanta haďi da tokari.
"Da sauri j-boy yazo yana rik'on hjy da tai wlh ba laifinta bane,halima sanadiyar abinda ya farune yasata shiga wannan halin da take ciki.
"Wani wawan hankaďa ta sake kai masa,haďi da cewa" wlh na rantse da Allah idan kasake cewa uffan saina tsine maka.
Sannan taci gaba da cewa" meyai maki da kike niman kashemin shi?abin ya tashi daga kan uwarsa ya dawo kansa,tou wlh baki isa ba.muguwa yar mai mugun hali,kin halakarmi da ďah sabida wata biyan buk'ata taki.tou wlh bari kiji duk abinda kike ciki ina sane dan haka ki kiyaye 6acin rana,idan kika k'ureni wlh Allah...kuka kawai Sofy keyi tana niman taimako.duk inda hjy tasamu a jikin Sofy kai mata duka haďi da nushi kawai takeyi.
"Tanayi tana hakkin,tana cewa" yau saina danďana maki irin azabar da kika jefasa a ciki.
"Duk yanda Sofy taso ta kubce takasa sabida hjy ta banke ko ina.
"Gani hjy zatai ďayen aiki yasa J-boy zubewa gaban hjy yana magiya harda kukansa.amma besa hjy ta kyale Sofy ba saita ta tabbatar taji a jikinsa.
"A lokacin ne likata ya shigo,a cewarsa wai yanzu ne yazo wucewa yake jiyo hayaniya a ďakin.
"Da farko hankalinsa ya tashi,sabida yanda yaga Sofy kwance rana nishi sama-sama.amma da hjy tai masa bayani abinda ta aikata,bece komai ba.iya hakuri daya bawa hjy.sannan yai mata faďa data daina yanke hukuncu ciki fushi"
"medata gado J-boy yai aka jona mata ruwa.a fusace hjy ta fice daga ďakin haďi da cewa" bazan hana a baki kulawa ba,hau kisha kafin anjima na dawo na ďora maki daga inda na tsaye.
"Ficewa tai zuwa ďakin meenal.
Hjy na fita har k'asa J-boy ya duk'a yana bawa Sofy hakuri bisa ga abinda hjy tai mata.
Duk da ruwan dake hannunta amma saida tasa hannu ta kamowa J-boy nasa hannu ya mik'e haďi da cewa yai hakuri babu komai.
Idan a gareta ne komai ya wuce,sannan dan Allah yaje ya kuma bawa hjy hakuri,kada ya dawo ďakin har sai yaga ta hakuri ta yafe mata.
Da farko kin tafiya yai saida yaga ta canza masa fuska sannan ya fice zuwa ďakin su Basik.
Yana fita,tai tsaki haďi da cewa"dama wata kika mawa bani Sofy ba.sannan inaso ki rubuta ki ije yanda na zubar da hawaye,kema sai kin zubar.
Nakima sai yafi nawa,domin saina rabaki da ďanki da kika gadara dashi.kedashi sai dai ku haďu a layi amma badai ya take k'afa zuwa gidanki ba.

              ****

" koda Rukky ta isa gida inna ganita tai buju-buju kamar wacce tai wanka da dusa,sai faman bala'i rake zazzagawa a tsakar gida.kai babu ko ďan kwali daga ita sai buje.tana cewa "yau nida kaine a gidan nan,inanan zakazo ka sameni komai dare ina nan ina jiranka sai dai idan bazaka shigo ba.
Kai kawai Rukky ta kwaďa sannan ta k'ariso cikin gidan.
"Duk'awa tai har k'asa tana gaida inna.masifa ya hana inna amsawa.
"Gani haka yasa Rukky mik'ewa ta shige cikin ďakin inna,gani ďaki babu gyara komai a barbaje yasa Rukky cire hijabin dake wuyarta sannan ta sauke goyo nan tahau gyarawa inna ďakin.
Saida ta ninke kayan ďakin kam sannan ta share haďi da kakka6e ko ina.
Kafin ta gama ta ďorawa inna ruwan zafi.tana gamawa dai-dai da ruwan yai zafi,juyewa yai taiwa inna bayi sannan tazo ta sanar da ita da taje tai wanka.
"Cike da masifa inna tace" uban wankan!nace uban wankan ko.
Wankan me zanyi,wama zamma wankan?bayan wanda nakeyi danshi baya gani,tunda gashi yaje yai aure.bazan ba,nace bazan ba.
"Cikin zuciya Rukky tai murmushi haďi da cewa" inna kenan.dama maje faďa banza bare sarki yai sak'o.
"Cikin hikima da rarrashi tlalla6i inna har ta yarda taje tai wanka,kafin ta fito Rukky ta ciro mata kaya mai kyau wanda bata cika wasaba ta ije mata haďi da mai.
Koda inna ta fito dakar ta yarda tasa kayan,sannan sukaci gaba da hira.duk irin faďar da inna keyi." hakuri kawai Rukky ke bata da haka har dare yai,misalin k'arfe tara daddy ya shigo hannunsa ďauke da leda guda biyu.da sauri Rukky ta mik'e zuwa inda yake tsaye.kallo ďaya daddy yaiwa inna dariya ya kamashi.
Duk'awa Rukky tai har k'asa ta gaidashi haďi da yi masa fatan alkhairi.
"Inna dake zaune,tsaki tai sannan tace,shima yasan gaskiya babu wani alkhairi da zai gani a wannan auren,masifa da bala'i yanzu ya fara gani.kuma wlh idan ya kuskura yace ta tare anan gidan wlh sai dai buzunta amma ba ita ba,idan kuma yana gani kamar k'aryane ya kwada ya gani".
Har daddy yasa k'asa da niyyar shiga ďakin cikin dabara ba tare da inna ta ganta ba tace dashi kada ya shiga".
"Murmushi kawai yai,sannan ya ďauki ledar daya shigo dasu guda ďaya ya mik'awa Rukky sannan sukai sallama ya fice daga gidan.
" Rukky na shiga da ledar tsawa inna ta daka mata data fita mata dashi,idan ba hakaba saita 6ata mata rai"
Komawa tai da baya daje ta ije ledar sannan ta dawo nasiha haďi da misalai taiwa kawowa inna har saida inna ta nufasa sannan Rukky taje ta ďauko ledar nama ta shigo dashi.farantin rover taje ta ďauko ta juye tsiran a ciki ta turawa inna gabanta.
Da farko inna kinci tai amma daga baya cikin tai sosai tanaci tana tsinewa Talatuwa da HARUNA albarka.
Haďi da cewa "tayi imani Talatuwa bazataga annabi ba, sannan kuma ita yar wutace,dama tun a duniya Allah yake bayyana yan wuce,tou Talatuwa tana ďaya daga cikinsu.
Tana cikin tsine-tsinen albarkanta kenan saiga kiran hjy ya shigo wayar inna. Saida Rukky tai receiving call ďin sannan ta mik'awa inna.da sallama inna ta kara wayar a kunninta bayan su gaisa hjy take faďi mata abinda ya sami Basik.
Wani sabon tashin hankali ya sake kama inna.salati tai haďi da tambaya garin yaya hakan ya faru?".
Nandai hjy taďan tak'aita mata iya abinda tasani sannan sukai sallama.
"Gani goma ya wuce yasa Rukky cewa zata gida idan Allah ya kaimu gobe zataje ta dubasu.tou inna tace"bayan ta goya Muhsana sannan ta rungume Muhammed dake bacci.
" Har bakin kofa inna tai masu rakiya saida suka sami napep suka shiga sannan ta koma gida.
"Maganar auren daddy me dami inna ba sai dare.tunda ta kwanta maganar yake mata yawo a zuciya,sai faman sake-sake da juyi takeyi ita kaďai a ďaki babu abokin shawara.
" shiko daddy yana can yana shan shagalinsa.duk da shekarunsa besa su saurarawa junansu ba,daddy ranar sai abinda daddy ya mance.sabida gajiya har makara sukai.ko kafin su buďe kofa rana yafita.
"Asalatun farko bayan ta idar da sallah asibiti kawai ta wuce,gun duba jikin Basik.Mu'azam kawai tasanarwa mawa ga inda zata.
Hakan yasa koda daddy ya shigo be ganta ba.dayai tambaya Mu'azam yake sanar dashi inda taje da kuma abinda yafaru.
Allah ya kyauta daddy yace.bayan la'asar su uku shida Mu'azam sai yaya Sani suka tafi gaida Basik. Harka kayan wasa daddy ya siyewa Basik sannan suka k'arisa cikin asibitin...!!!!!!!!




      Comment
                 N
                 Share

MAKAUNIYAR RAYUWAWhere stories live. Discover now