MAKAUNIYAR RAYUWA

143 13 6
                                    

*MAKAUNIYAR RAYUWA*
________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________

~DIDECATED TO~
*ANTY FAUZIYA*
   *ƳAR AMANA*

https://www.facebook.com/104534761033461/posts/119016616251942/?app=fbl

         *PART THREE*
              *PAGE 12*

*BISMILLAHR RAHMANI RAHIM*

_____"Na'am Rukky!!,jiki a sanyaye ya ƙarisa bakin gadon haɗi da tsareta da ido yana me ƙare mata.ya jima yana kallonta snn yace da ita bata sameki haka Rukky?badai dukanki akai ba,idan ma dukane tou waye ya dukeki,nasan dai ba mijinki ba?.
   Kukane yaci ƙarfi Rukky yasa ta kasa bashi amsar tambayoyin"
  "Shiruuu Yaya Mu'azam yai yana me kallon Rukky haɗi da tunane-tunanen kala-kala tsaki yai snn yace"kukan ya isa haka dan Allah, ki ɗaure kiyi min bayani waye yai maki irin wanan mummunar dukan haka?"
   Duk da haka Rukky bata bashi amsa ba,su jima haka zaune idan ba kuka ba babu abinda Rukky keyi."Yaya Mu'azam yai rarrashi har ya gaji Rukky bata daina kuka ba"
    Miƙewa yai haɗi da cewa"ni zan tafi,domin banga amfani zuta asibitin ba,yai maganar ne haɗi da ɗan motsa ƙafarsa,da sauri Rukky tace"ba haba bane Yaya.
    Tou menene?".
   Shiru ta kuma yi,bare da tace dashi komai ba.
   Gani haka yasa Yaya Mu'azam cewa"kiyi magana Rukky domin musan ta inda zamu bullowa al'amarin"
    Cikin kuka Rukky tace"shine""
         "Shine wahhh!!?"
    "Kamaru"""wani kamaru ɗin daga ciki?badai kicemin mijiki ba?".
  "Shiruuu ta kuma yi".
"Himm Yaya Mu'azam yace"sann yaci gaba da cewa"me kikai masa da har zai maki irin wanan dukan haka?,waima na tambayeki yaushe ya dawo ne da har.....jiyane ya dawowa"Au a dawowar da yai jiya dine har yai maki wanan dukar?".
  Tou ma wai me kikai masa ne da har zai ɗauki irin wanan hukunci?gaskiya  be kyauta ba,duk irin hakurin da kikeyi dashi da uwarsa amma bisa ɗan wani dalili tasa mara ma'ana zai kamaki da duka?".
    "Uhmm Rukky tace" Snn Yaya Mu'azam yaci gaba da tambayarta da wama ya kawoki asibitin?"Yaya Bala ne da matarsa"""ok ina suke?"su tafi gida..Kenan tunda suka kawoki sukai tafiyarsu suka barki kwance kaman wata mara gata ko?"
   "Nanma shiru tai"
   "Ina shi ƙamaru ɗin yake?"
   Yana guda""Kenan tunda aka kawoki bezoba"
  "Eh,be zoba"
   "Himm,amma wlh ƙamaru ya bani mamaki snn kuma ya bani kunya,amma ba damuwa,ni zan tafi gida domin na sanarwa inna dagama kinga sai tazo ta kwana dake ko".
   Ihmm ta kuma cewa"
   Har ya juya sai kuma ya dawo da baya yace"tou shine basu tafi da yaran ba?wama ya taho masu nan din?"
   Yaya Bala ne,wai sabida suna kuka"
    Shine da zai tafi beje dasu ba?mikomin su"
   Hannu yasa ya ɗauki Muhasana ya sagalata a kafaɗarsa snn ta tada Muhammed, Muhammed na tashi yace"zo muje,su jima Muhammed na magagun bacci sai daga baya snn ya ware suka fice daga ɗakin da Rukky take haɗi da cewa"insha Allahu bazan daɗe ba zamu dawo da inna"
        Tou a dawo lafiya Rukky tace dashi"
   "Yaya Mu'azam na fita bakin gate ya sami napep zuwa gida"Yana isa kai tsaye ɗakin inna ya nufa numgume dasu Muhammed."Lariya inna tace haɗi da tambayarsa yaran waye ya kwaso masu cikin wanan daren?"..
    Be tanka mata ba,kai tsaye shigewa daga ciki yai domin kwantar dasu"
   Yana gaba inna na biye dashi a baya,leƙawa tai,da sauri ta miƙe haɗi da cewa"kamar su MAHAMMADU koko idonane?""
"Eh sune"
    "Lafiya ka kwaso mata cikin daren nan?"
   "Be tamka ba saida ya shinfiɗa yaran snn ya juyo yace"tana asibiti batada lafiya"""Subhanallilahi,meke damuta?".
   "Zazzaɓine yanzu haka ma zuwa nayi mu tafi dare dake,domin babu kowa a tare da ita"
   "Kamar yaya, babu kowa a tare da ita?,ina yan uwan mijinta?"
  "Duk suna gida"
   "Ban fahimta ba".
  "Dan Allah inna yanzu ba lokacin wani dogon zancen bane,ɗauki mayafi kawai kizo muje,idan yaso in mu ina can mayi maganar"..."Kai Mu'azam idan kasan akwai matsala ne tun yanzu gwamma ka sanar dani domin bazan..."A'a iya wlh babu wani matsala,idan ma akwai tou ba wani me yawa bane amma in har akabi abin a sannu..."kamar Yaya,ba fahimce kaba Mu'azam".. Dan Allah inna kizo muje kawai"Nanfa inna ta turke babu inda zata idan ba Mu'azam ya faɗi mata abinda ya sami Rukky ba".
"Duk da beso faɗi ba amma dole yasa shi ya faɗi mata.."buuuuuran ube inna tace snn taci gaba da faɗin yanzu shi ƙamaru ne yakama Rukky da duka wanda har haka?toma yaushe ya dawo garin da har zai kamata da duka da har zai takata ga kwanciyar asibiti,toma ina uwarta tasa take?koda yake koda tana kallo ba magana zatai ba,tunda ba son Rukky takeyi ba"
   "Can kuma tai murmushin haɗi da cewa"Allah sarki yaro,taka kyau take bata ƙarko,to wlh wanan dukar da kaiwa Rukky kada kaga kamar kaci bulus domin saina rama mata,snn kuma a jikin uwarka zan rama mata...Haba inna dan Allah kibar wanan zancen muje idan yaso komai menene saiya bi baya"Ya jikin nata?tana can rai a hannu Allah ko?domin kasan yanda dikan soja yake,ba imanine dasu ba"
  "Uhmm kawai Mu'azam yace"
  Kyale ta ɗauka haɗi da cewa muje"
Har sukai bakin zaure wani tunani ya faɗowa Mu'azam,Ina zuwa yace"juyawa yai zai koma ciki,Inna tace"Lafiya naga zaka koma daga ciki?"
Eh,yarane zan kwaso na kaisu gidan Talatuwa,sabida be dace mu tafi mu barsu su kaɗai kwance anan babu kowa ba"..
Cikin masifa ita tace"babu inda zakakai min jikoki,wato saresarin ta lashesu kafin safe ko?".
   "Subhanallilahi wanan wani irin magana ne kuma haka?".
   Hakane mana Mu'azam a yanda naji labari kafatalin zuri'arsu masune,Dan haka cisu Muhammed bazai zama abu me wiya a gareta ba,sann ma idan banda abinda ga Sani kwance a ɗaki,na tabbata idan yaji motsi zai leƙasu.
Duk da haka Mu'azam be yarda ba saida yaje ya sanarwa Yaya Sanin snn yazo suka tafi.
   Suna fita suka hau napep zuwa asibiti.
   Rukky na zaune shiruuu ta shiga duniyar tunani har su inna da Yaya Mu'azam suka shiga ɗakin bata sani ba.
Koda inna ta ƙarisa bakin gado zubawa Rukky ido tai tana me ƙare mata kallo ba tare da Rukky ta dawo daga tunanin da take ba"
  Ta jima tsaye snn tasa hannu ta taɓata haɗi da kiran sunanta Rukky! Rukky!! Rukky!!!,ana ukkune Rukky tai firrrgigi haɗi da cewa"naaaa'm,karaf tai ido biyu da Inna dake tsaye kanta"
   "Yaya Mu'azam dake tsaye yace"kinga ni Inna"babu mamaki tun fitata take wanna tunani,yanzu sabida Allah meye amfani irin haka?"
   "Uhmm Mu'azam kenan" Snnu RAKIYA yaya jkin?"
   Jiki da sauki Inna, ɗan sunkuyawa tai ba tare data sauka daga gadon ba tace"Inna yini Inna"
  "Lafiya kala RAKIYA,Yaya jikin?"
    "Jiki alhamdullhi,na samu sauki".
  "Yanzu sabida Allah abinda sukai su kyauta kenan,dan rashin imani da rashin tsoron Allah sai su taru su kama jimganki kamar wata jaka,tou wlh bazai sabu ba,yanda suka ɗumama maki jiki nima saina ɗumamawa uwarsa jiki,domin idan ba uwarsa ta daka ba wlh bazan huce ba"
     "A'a Inna abin abun a hankali,domin abinda yafi damuna da bata min rai yanda sukazo suka zuɓeta sukai tafiyarsu kaman wata mara gata,yo ko wanda bata sani ba,ai be kamata kai masa haka ba bare kuma..."Barsu kawai Mu'azam duk rance sukaci,kuma sai su biya,domin kaɗan zai rage ba'a kawota asibiti ba"
   "Ina shi ƙamaru?ko har yanzu bezo ɗin bane?"
  Kai Rukky ta ɗagawa Yaya Mu'azam da a lamar eh"
   "Uhmm Allah ya kyauta iya abinda Yaya Mu'azam yace kene,snn ya juya gun Inna yace"ni zan tafi gida,amma in Allah yasa mu wayi gari lafiya da zaran mu idar da sallar asuba zanzo na dubi kwananaku".
     "Tou Allah ya tashemu lafiya"
  "Ameen"
Bayan tafiyar Yaya Mu'azam kusan kwana Inna tai tana masifa"Rukky dake kwance ne ke bata hakuri,da haka har safe yayi,suna idar da sallar asuba saiga Yaya Mu'azam yai sallama shida daddy.
  Da dake zaune kan dadduma ta miƙe ta taresu da sannu da zuwa, bakin gado Yaya Mu'azam ya zauna,shi kuma daddy a kujeran rover dake gefe,bayan ya zauna ne Rukky ta duƙa har ƙasa ta gaidasa,amsawa yai haɗi da tambayar jiki"da sauki tace"
  Inna na idarwa suka gaisa,bayan su gaisa ne suka ci gaba da magana akan dukan da ƙamaru yaiwa Rukky haɗi da tambayarta laifin da tai masa har ya kaisa ga duka."
        Shiru Rukky tai kanta na ƙasa,duk irin tambayar da sukai mata bata amsa suba,da haka har su daddy da Yaya Mu'azam suka miƙe zasu tafi,suna Sallama kenan saiga Yaya Bala ya shigo,yana shigowa  gani su daddy yasa shi duƙawa suka gaisa bayan su gaisa dasu daddy ne ya juya ya gaida Inna haɗi da tambayar me jiki,da sauri duk suka amsa ije ledar daya shigo dashi yai bisa kan teburin dake ɗauki haɗi da cewa"babu yawa ayi hakuri"
Bayan ya miƙene sukai waje shida Yaya Mu'azam,suna fita suka sake wani sabon gaisuwar..Yaya Mu'azam ne ya katse Yaya Bala da tambayar garin Yaya hakan y faru?"
Saida Yaya Bala ya nuna mutuƙar damuwarsa snn ya fara zayyana wa Yaya Mu'azam iya abinda yasane(duba da yai da ba ƙima da mutuncinsa bane ayi irin wanan mummunar aikin daga bakinsa yasa duk cikin zantawar da sukai da Yaya Mu'azam banda maganar saki)qkoda Yaya Mu'azam ya koma ciki be sanarwa kowa ba saida sukabar asibitin,suna hanyar komawa gida Yaya Mu'azam ke sanarwa daddy".
  Cike da mamaki daddya yace",yanzu shi ƙamaru ne ya aikata haka?yaron da nake masa kallon me hankali da sani ya kamata shine zai aikata haka?,amma babu komai rayuwa ce.
Bayan fitar su daddy ne Rukky ta miƙe haɗi da cewa ina zuwa Inna"Ina zaki kuma?"
  "Fitsari zanyi"
  "Fitsari kuma,bayan wanda kikai yanzu da zamuyi alwala?"
Eh tace"
Ɗaukar duta tai ta fice daga ɗakin, tana fita gangarawa tai can nisa da ɗakin, ta jima tsaye a wajan snn ɗaki daga cikin ma'akatan wajan tazo wucewa,da sauri Rukky tace"bawar Allah jimana dan Allah"
  Tsayawa tai snn tace"lafiya?"
   Dan Allah wayarki zaki arami""Wayata kuma,gaskiya kiyi hakuri bazan iya ba"tun kafin Rukky tai magana tuni nurse din tai wucewarta"Hanata wayar da tai besa Rukky fusata ba musanman ma idan tai duba da yanda duniyar ta zama abin tsoro"
  Da haka saida ta tsaida nurse har uku tana roƙonsu dasu bara aron waya tai kira amma duk ƙin bata sukai,ana huɗune ta amince zata bata tai magana amma da sharaɗi,sai dai ta faɗi numbar wanda zata kira ta sanya mata cikin wayar idan akai receiving call ɗin saita bata"Rukky bataki ba,haka ta dunga kira numbar matar na sanyawa cikin wayar tata bayan ta gama ta danna kira,tayi kira yafi sau uku ba'a ɗaga ba,gani haka yasa nurse cewa"kinga wanda kike kira yaƙi ɗaga wayar ko?waima wayene kike kira da har zaiki ɗaga kiran haka?"
    Jiki a sanyaye tace"mijina ne" da yake tana ɗaya data cikin wanda suka bawa Rukky taimakon gaggawa lokacin da aka kawota tace"Allah sarki kill baya kusa da wayar ce,duk a tata gani wanda ya kawota shine mijinta wato Yaya Bala"sai tace bari dai na kuma gwadawa"Sake kiransa tai, ringing farko aka ɗaga wayar da sallama.Jin sallama yasa nurse miƙawa Rukky wayar tace gashi ya ɗaga"
Sallama Rukky tai haɗi da cewa"nine Rukky"
Dariya alhj KHAMEES yai haɗi da cewa baby kece???.....
Bazan gajiya da baku hakuri ba,wlh aiyukane sukai min yawa yasa,amma insha Allahu koda babu yawa zan rinƙa ƙoƙarin ina typing kullum,domin idan ba haka nayi ba gaskiya labarin zai kaimu har wani lokaci domin yanzu aka fara..Idan baku mance ba ya kamata kowa ya amshi sakamakon sa.
Daga

RUKKY
KHADIJAT
TALATUWA
SHI KANSA UBAN GAYYA KAMARUDEEN ƊIN
DA KUMA IYA
SNN GA J-BOY.kadafa ku mance wani auren zaiyi,shin wani iri zamane zasuyi da Meenal?sann menene makomamta yayin da J-boy ya gano wanda ta nuna a matsayin iyayenta ƙarya ne tai masa.snn kuma menene makoman Sofy,shin zata tuba ta koma ga iyayanta ko kuwa haka rayuwarta zai ƙare a bariki?'snn kuma da alhj KHAMEES shimma waye shi,snn kuma menene alaƙarsa da kamarudeen,shin idan asiri ya tuno kamarudeen zai iya jada alhj KHAMEES ko kuma haka zai kyalesa,snn meye makomar Yaya Mu'azam haka zai zubawa Khadijat ido yaci gaba da zama da ita da karantarta ga kuma rashin gani mutunci da darajan uwarsa da batayi,shin rabuwa da itane zaiyi ko kuwa haka zasuci gaba da zama?
   Kai bari na tsaya haka koda na cikaku da surutu,domin kuwa idan har kukai hakuri imsha Allahu a hankali komai zai warware.

Labarin MAKAUNIYAR RAYUWA labarine me tsayi wanda ni kaina bansan zaiyi tsayi haka ba,snn kuma ban san zai kaina har izuwa wanan lokacin ba tare dana ƙare ba.amma yanzu ga zaɓi, duk yanda kukace haka za'ayi.

Na harhaɗa maku labarin sabida muyi saurin gamawa ko abin abun a hankali a warware komai?"

   Sai naji daga gareku
   Farin cikinku shine abin alfaharina
   Fatan alkhairi gareku masoya 🌹❤️ aduk inda kuka..##mmn uswan ce##.

MAKAUNIYAR RAYUWAWhere stories live. Discover now