MAKAUNIYAR RAYUWA

117 8 2
                                    


_*MAKAUNIYAR*_
             _*RAYUWA*_

*_🌈KAINUWA WRITERS✍🏻 ASSOCIATION_*🤝🏻

_*fcbk group*_
_*mmn uswan*_
*page Hauwaszaria*

https://www.facebook.com/379407779489539/posts/518531808910468/?app=fbl

         *PAGE 19*
                 *PART 2*

_*BISMILLAHI RAHMANI RAHIM*_

________"Nace ubankane bameya faruba."Jin haka yasa yaya Bala shiru be sake tambaya ba.komawa kan su daddy da Talatuwa da suke tsaye yai ya duk'a har k'asa ya gaidasu.
Eiiii Baffa yai da murya.a lokacin ne duk suka tuna da Baffan".
"Daga su K'amaru harsu Talatuwa ďinguma sukai zuwa ďakin Baffan.K'amaru ya shinfiďa masu tabarma bayan su zauna ne suka gaigaisa.ita kuwa iya k'in shiga tai,a bakin k'ofa taja ta tsaya.wata zuciya na cewa ta wuce,wata zuciyar kuma yace tatsawa sabida kada ayi maganarta a bayan idonta"
"Hakan yasa taja ta tsaya a bakin kofa tana karkaďe-karkaďe.suna haďa ido da Baffa, yai tsaki haďi da cewa" wlh kinji kunya Hanne.banyi mamaki dan kin aikata haka ba,sabida nasan kaďane daga cikin bakin hali irin naki.amma inaso ki sani insha Allahu duk abinda kika shuka saikin girbi kayanki da hannunki kafin ki koma ga ubangijinki"
Kuma sai Allah ya sakawa yarinyarnan domin ciki zallinta kin tsaneta kin ďora mata karan tsana sabida wani dalili naki na banza da wofi...dallah yimin shiru,nayi ďan..nace nayi ďan ko zaka rama matane?"""bazan rama mataba amma kisani wanda yafini yafiki shine zai rama mata bi'izillahi"
Au na ďauka ko rama mata zakayi..uhmm Baffa yace besake tanka mata ba.su daddy da  Talatuwa kuwa kai kawai suke kaďawa haďi da mamakin iya".
       "Juyawa Baffa yai zuwaga Daddy dake zaune.gyaran murya     sannan yafara da bawa daddy hakuri bisaga abinda iya taiwa Rukky haďi da faďin duk irin abin alkhairi da kyautatawa da Rukky kemasa.Murmushi daddy yai cikin zuciyarsa yace"ai dama Rukky ba daga nanba.A fili kuwa babu komai yace,sannan yaci gaba da cewa" nima ba komai ne yasa natasota a gaba mukazo sai dan naji dalilin koranta da aikai.kasan halin ďan yau,baka shedarsa...
"Murmushin takaici Baffa yai haďi da cewa" wlh babu wani abinda tai,shirine kawai irin na Hanne.amma babu komai zanyi magani abin"
"Maganinwa zakayi?"" lallaima bakaji dakyau ba..."taranta Baffa yai da mara kunyar banza mara kunyar wuwiyar banza kawai.sannan ya juya ga inna dake gefe yaci gaba da cewa"aini ban goge makiba da baki karereyamin itaba.Murmushi inna tai haďi da yunkuyar da kanta k'asa"
Daddy dake zaune balla mata harara yai.itako ko a jikinta".
"Iya dake tsaye bakin kofa.tsaki tai haďi da cewa"tunda bata karerayani ba kai saikazo ka karerayani.gurgun banza gurgun wofi kawai ba banzaba Allah ya nakasaka...kafin tak'arisa maganar sandarsa ya ďauka ya wulwula ya halbeta dashi"
"Da sauri iya ta kauce haďi da cewa" bakin azalumi,jiya ba yauba.dan kenan kayi kasha lafiya amma ba yanzu ba"
Gani haka yasa daddy mik'ewa haďi da cewa"mu zamu tafi"".
"Hakuri sosai Baffa yabawa daddy haďi da alk'awarin hakan bazai sake faruwa ba.sannan kuma yana rik'on Rukky data koma ďakinta.
" murmushi Daddy yai sannan yace"babu komai,Allah ya kiyaye gaba ya kuma k'ara hakurin zama".
"Har sun mik'e da niyyar tafiya" inna tai gyaran murya haďi da cewa"inada magana".
Take daddy yaka mata tsawa da cewa"banason zancen banza,idan har na isa dake ki tashi kawai mutafi,domin bana buk'atar naji kince komai akan wannan maganar...daga sama har k'asa inna ta kalli daddy haďi da murguďa masa baya.juya fuskanta tai gefe sannan taci gaba da cewa"RUKAYYA dai yarinyar ďan uwa nane dan haka babu wanda yaisa yaimin ikon da ita,kuma ya hanani magana akanta..Baffa dake zaune shiruuuu yai yana me sauraron yaji abinda zatace game da Rukky.cikin zuciyar kuma yace"Allah mai ikon ashe ko inane tsiyar,bani kadai nake fama da irin wannan matsalarba a gidana"
"Juyawa ga iya inna tai haďi da nunata da ďan yatsa tace"ga Rukky nan wlh summa tallahi idan nasake jin makamancin irin abinda kikai mata yakuma faruwa wlh nida kece,domin wanda nayi maki kaďane bisa ga wanda zanyi maki nan gaba...daddy dake tsaye jikinsa yai sanyi matuk'a gaba ďaya kunya ya lulu6esa ji yake kamar k'asa yabuďe ya shige.domin duk maganar da inna keyi agabansu yaya Bala da k'amaru takeyi ko tsoron idonsu batayi.
" Shewa iya tai haďi da tafi sannan taci gaba da cewa"ina yar take?yarinyar da kika kasa riketa bisa gaskiya da amana.masifa da azaba babu irin wacce batashaba a gunki.aini banson kinasonta ba tunda baki wanketa kinbawa ďanki ba.sabida kinsan ba abin arziki bane yasa aka lik'awa ďana ko tou ta Alla ba takuba.shegiyar yarinyar mara kunya wacce tak'are gantalewa ta k'are rabawa maza kanta a titi shine har...wuff K'amaru yai hannu iya yakama zuwa cikin gida side ďinta.
"Itama inna mik'ewa tai da niyyar binta har cikin gidan"
Hannu daddy yasa ya kamota batare dayace komai ba.da k'arfi ya rik'eta yana janta kamar wata tunkiya".
Rukky dake zaune kwalla kawai takeyi.sabida tsabar bakin ciki ko motsi takasa tunda ta zauna aikin kenan".
Shiko Baffa cewa yai da k'amaru ya kyaleta iya a masa maganinta".
"Suna fita Rukky tamik'e irama tafice daga ďakin Baffa zuwa nata ďakin.tana ďauke da Muhsana.shiko Muhammed jikin yaya Bala yaje yahau ya zauna yasa wasa.yaro ba mutunba saiya girma,duk abinda sukeyi wasarsa kawai Muhammed keyi.
" Suna fita daga ďakin iya tace"ehhhh dai atafi,Allah ya raka taki gona.itama yar taki tananan tafe domin yanzu nan zanemo almajirai su tayata kwashe kaya.yau dai muyar da kwallin mangwaro mu huta da k'uda.irin tsiya kawai,shegu mayu tou wlh ta Allah ba takuba.
"Juyowa inna tai tace" ubankine maye.duk garinku waye besan ubanki shine sarkin mayuba.kuma idan kikabar Rukky ta kwana a gidan nan ban gode maki ba.
Ehhhhh dai a tafi.saita biyoki...jin haka daga iya har inna kowa k'ok'arin kwacewa yakeyi domin yadawo ya ďora daga inda ya tsaya"
Gani haka yasa K'amaru k'ara rike iya da k'arfi duk fisge-fisgen da takeyi da kinbinsa zuwa ciki amma takasa kwacewa daga hannunsa.
Haushi da takaici ya kama iya.nan tahau zaginsa tana kwashe masa albakar.duk abinda sukeyi a kunni Rukky.in banda kuka babu abinda takeyi"
A 6angaren Khadijat rawa kawai take zubawa haďi da kwashe sheoky dan murna"
"Ita kuma inna bari tai har saida sukakai dai-dai bakin k'ofar fita.ru6a6iyar gate ďin tarike gam taki fita daga gidan a dole sai daddy ya kyaleta taje taci uban iya.gani haka yasa Talatuwa zuwa kusa da inna.tace yanzu sabida Allah meye kikeyi haka?.wlh hakan ba tsari bane..." Dallah jacan banza 6arauniya kawai.kema ina zuwa gareki kada kiga nayi shiru ki ďauka hakura nayi.inanan zuwa maki.aszaluma macociya...murmushi kawai Talatuwa taiwa inna haďi da cewa"su RABI ikon Allah.matan a gidan alhj Usman kibada kanki asare kije gida kice ya faďin.."ubankine zaiba da kansa asare..
"Hannu daddy ya ďagawa Talatuwa alamar kada tasake magana.sata a gaba yai suka fice daga gidan sukabar inna anan tana faman sauke ruwan bala'i.tajima tanayi sannu tafice daga gidan.
Iya tayi-tayi takwace hannunta daga na K'amaru amma takasa.takaici yasa tahau zaginsa haďi da cewa"idan yanaso ya gama da duniya lafiya yaje kawai ya rubutawa Rukky takardan sakinta idan kuma yaki rubutawa ya biyata nononda tashayar dashi.a gigice K'amaru yasakar mata hannu.jikinsa na rawa ya zube agabanta hannu bibbiyu yasa yarik'e mata guiwarta yafara bata hakuri yanayi nayi kuka.data hakuri tajanye wannan maganar.
Ko a jikin iya.k'afa tasa ta hankaďesa tai shigewarta ciki"
"A guje K'amaru ya mik'e sauri yake haďi da gudu yana tafe yana kwaďawa yaya Bala kira.
"Da sauri yaya Bala yamik'e daga zaunen da yake fitowa daga ďakin Baffa yai haďi da tambayar K'amaru da lafiya?".
Shima Muhammed fitowa yai.gani babansa na kuka yasashi rusawa da kuka haďi da zuwa ya rungumesa.
"yaya Bala ne ya ďauki Muhammed sannan yaci gaba da tambayar K'amaru. Cikin kuka K'amaru ke faďiwa yaya Bala abinda iya tace dashi".
Baffa naji yakirasu zuwa ciki.bayan su shigane Baffa yaita bashi musalai kala-kala haďi da kawo masa ayi da hadisan manzon tsira ahaihim salatu wassalamu.sannan ya sake jadadda masa aurensa da Rukky yananan daram babu abinda ya samesa.
Duk da haka basu gamsu ba.badan su raina da abinda Baffa yace dasu bane.tashi sukai zuwa wajan limamin unguwarsu.shida yaya Bala, bayan su gaisa yake tambayarsu abinda ke tafe dasu.yaya Bala be boyewa malam komai ba.duk yanda K'amaru sukai da iya saida yaya Bala ya faďiwa malam.
Shiruu yai na ďan wani lokaci sannan yafara basu musalai kamar yanda Allah subhanahu wata ala yace cikin suratun *ISRA'I AYA TA 23* _*wa k'ada rabbukha Allah ta'abuduu illa iyya'hu wa bilwalidayni ihsana, immayablu ganna inda qibara ahudu huma awqilahu huma falah taqul Allahuma uffil wala tanhar huma waqul Allahuma qaula kariymmah*_

_Abin nufi anan idan akwai dalilin ta shari'a tou yaya biyayya ga iyaye?. Nasan wajibine biyayya ga iyaye.Menene da lilin da zaisa uwa tace"ďanta ya saki matarsa?" "shine rashin kunya". Idan har ya tabbata iyalinka zata wulak'anta maka uwarka rashin kunya,tou ai basai an faďi ba._

_Abin nufi anan shine bayan biyayya ga Allah da manzonsa babu wani biyayya daya rage a gareka saina iyaye.dalilin saukar da wannan ayar kenan daga Allah subhanahu wata ala sai kuma annabinsa  (Muhammadu (S.A.W) babu wani biyayya da yazama dole akanka saina iyaye._

_An tambayi Muhammed bin Sale Al,husainiya rahatuplahi.Cikin littafin fatawul jama'a lilmar'a muslimah a cikin shafi na ďari shada juzu'i na arba'in da ďaya akai tambaya" yaya matsayin_ _biyayya ga uwa take agun ďanta?"_
_Kamar yanda yazo ciki alkur'ani mai girma cikin SURATUN ISRA'I haka yasake memetashi.Biyayya ga uwa abune mai matuk'ar muhimmanci akan ďanta ko yarta_

"Matarka tanayiwa mahaifiyarka rashin kunyane?.
" daga K'amaru har yaya Bala da sauri sukace"a'a.rashin kunya ba ďabi'ar Rukky bane"
Nan malam ya shida masu cewa"aurensa yananan daram.amma tunda haka yafaru mafi alkhairi kawai yarabasu.rabasu da zaiyi shine kwanciyar hankalinsa.tunda alamu ya nuna yanaso matarsa,sannan kuma uwarta ta takura masu.yin hakan shine kawai mafita a garesu..godiya sosai sukai masa sannan sukai sallama.
*tou yan uwana mata abinda nakeso mugane anan shine,dan Allah yariga ya haďaka da abokin zama mai hali irin na iya saidai hakuri.ga misali,iya uwar miji take agun Rukky ko?,tou inaso muyi misali da karan kanmu.yau inda ace  uwarka/uwaki ce keda irin wannan halin yaya zakiyi?na farko dai nasan bazaki gujeta sabida mugun halinta ba.na biyu kuma kece kizo gida yini kawai kina shiga kiga matar yayanki tana sa'isa da mahaifuyarki,gashi kuma kinriga da kinsan mahaifuyarki ďince masifafa.shigan mata zakiyi ko kuwa zuba ido zakiyi kiga ana cimata mutunci?.idan mukai la'akari da irin wannan musalai wlh masu hali irin na iya koda sukai gomane zamu zauna dasu lafiya.yanda bazakiso a wulak'anta maki taki uwarba haka shima jikin da kike aure. Uwar mijin tankar uwarkace,inda bata haifaba bazaki gani ko auraba.kinga kenan tanada matuk'ar muhimmanci a rayuwarku kedashi. Nifa a tawa gani rashin sani darajan nagabane zaisa katsaya kuna musanyar miyau dashi.sannan kuma mutum koda wuta yake fitowa daga bakinsa saita ta6asa zaiyi maka.dan haka biyayya ga iyaye ko nagaba yanada matuk'ar muhimmaci a rayuwarmu.*
"Suna shiga gida har yaya Bala ya nufi hanyar side ďinsa da sauri K'amaru yarikesa haďi da cewa" dan Allah yaya muja kak'ara bata hakuri bisaga abinda ya faru".
"Murmushi yaya Bala yai sannan yace" kafara tafiya zan biyoka"
"Tou kawai K'amaru yace sannan kowa ya kami hanyar ďakinsa".....!!!!!!




  Comment
              N
              Share





📚✍

MAKAUNIYAR RAYUWAWhere stories live. Discover now