MAKAUNIYAR RAYUWA

182 14 2
                                    

_*MAKAUNIYAR*_
             _*RAYUWA*_

*_🌈KAINUWA WRITERS✍🏻 ASSOCIATION_*🤝🏻

_*fcbk group*_
_*mmn uswan*_
*page Hauwaszaria*

https://www.facebook.com/379407779489539/posts/518531808910468/?app=fbl

         *PAGE 20*
                 *PART 2*

_*BISMILLAHI RAHMANI RAHIM*_

_________"Yana shiga."gani Rukky yai zaune akan kushin ta haďa kaida guiwa.jiki a sanyaye ya k'arisa yaje ya zauna kusa da ita.
"Saiya ďaga hannu zai ta6ata sai kuma ya janye." a hankali yakai hannunsa jikin Rukky.
Da sauri ta janye jikinta haďi da juya masa baya,taci gaba da kukanta.
"Cikin zuciyarsa yace" Subhanallah"
"Nan yafara kiran sunata.a hankali yake kiranta haďi da cewa" dan Allah kiyi hakuri kiyafemin...uhmm Rukky tace haďi ta mik'ewa tai shigowarta cikin ďaki"
"A guje ya mik'e yabi bayanta.yana shiga zubewa yai a gabanta haďi da kamo k'afafuwanta yana bata hakuri haďi dayi mata alk'awarin hakan bazai sake faruwa ba"
"Duk da haka besa Rukky tadaina kukan ba.gani haka yasa K'aruma mik'ewa a hankali yaje ta bayanta cikin sanďa ya rungumo ta baya haďi da zuro fuskanta a kafaďarta yaci gaba da bata magana masu daďi da sanyaya zuciya".
"Tsakani mata da jimi sai Allah.tun Rukky na k'ok'arin kwacewa harta hakuri.duk da haka K'aruma be daina bata magana ba.

"Su Talatuwa suna hanyar komawarsu gida sukai karo da yaya Mu'azam.ganisu da yaine yasa shi saurin k'arisawa haďi da tambayarsu daga ina haka?".
"In brief daddy yasanar dashi abinda duk yafaru.
"Kai Yaya Mu'azam ya kaďa haďi da tambayar yanzu ina Rukky take?"
"A lokacin ne Talatuwa tatsoma masu baki da cewa" tana gidanta"
"Gudanta kuma?"
"Daddy yace"eh gidanta"!!
Tou yaya Mu'azam yace haďi da tsurawa daddy ido.alamar tambaya"
"Gani haka yasa daddy dafa kafar Mu'azam haďi da cewa" ina zaka?"
"Babu ko ina"
"Tou muje gidan"
"Tou kawai yace.
Nan suka kami hanya.suna gaba Talatuwa na biye dasu a baya"ashe duk abinda sukeyi inna dake tafe tana hangosu.gani su tsayane yasata k'ara ďaga k'afarta domin kamosu.gani suci gaba da tafiya yasata tsaki,duk da haka bata daina sauri ba.tana tafe tana maganganu".
"Suna isa bakin k'ofar gida,da sauri Talatuwa tasha gabansu da niyyar shigewa nata gidan..." daddy yace"kai nan zamu shigo"
"Gidan Talatuwa yanuna masa.har Mu'azam yasa kai" inna dake can tana zuwa.ihuuu ta kwaďawa Mu'azam haďi da dakatar dashi."Duk kansu juyawa sukai.domin gani wacce take ihu tana kiran sunan Mu'azam".
Gani inna ce yasa daddy tsaki haďi da cewa"mushige dallah.dukkansu kai sukasa zuwa cikin gidan.gani haka yasa inna rugowa a guje itama shiga tai cikin gidan suna shiga ďaki Talatuwa tashiga ta ďauko tabarma tana fitowa  daga ďaki inna na shigowa.keeekeeekeee tacewa Talatuwa haďi da tambayarta me zatayi?"
"Daddy yabata amsa dai-dai da tambayar da tai.da cewa me idonki ya gano maki...batabi takan daddy ba.juyawa tai gun Mu'azam tace" dashi mekazoyi a wannan tsinanne gidan.uwar me ka ije da zaka shigo ďauka.dallah shige muje.
"Daddy yace"babu inda zashi..kaeeee samugu kazauna..bazai zauran ba.nace bazai zaunarba.
"Murmushi  Mu'azam yai haďi da komawa gefe yaja ya tsaya yana kallo ikon Allah. k'arisowa tai takamo masa hannu tana jansa dayazo su tafi.
Shiko ko gezau beyiba" gani haka yasa Talatuwa cewa"haba baiwar Allah, meye kikeyi haka...ubankine nakeyi.nace uvankine nakeyi.wlh na rantse da Allah idan baki kiyayeni kin fita daga hankataba wlh saina wulak'antaki na tozartaki a garin nan.waima na tambayeki.
Ubanwa yace kisami baki a maganar Rukky? ".
Ko duk cikin niman dingin zaman ne.
Mu'azam najin haka kama hannu inna yai yana janta tazo su fita daga gidan.
"Cikin masifa inna ta fisge hannunta haďi da cewa" karabu dani naci uban aszalumar matannan macuciya mara mutunci 6arauniya kawai.insha Allahu sai Allah ya tona asirinki.sai duniya susan asiri kikawa mijina ya aureki.
"Da kaukausar murya daddy yadaka mata tsawa haďi da cewa" tafice masa daga gidq idan ba hakaba sai ranta yai mumunar 6aci.cikin tsiwa tace"na nawa kuma.dallah malam kaimin shiru.bakin manafuki.algugumi kawai insha Allahu wannan auren babu inda zashi.yar wuta kawai..cikin zafin rai daddy ya ďaga hannu zaikaiwa inna mari..
"Da sauri Mu'azam yasha gaban innar marin ya sauka akansa..
" jikin daddy yai sanyi sosai.ita kuwa Talatuwa tana ganin haka da sauri tabar gun ďaki tashige.
"Take idanu Mu'azam ya ciko da kwalla.
Inna dake tsaye hannu tasa ta dage kuncinta kace ita aka mara.tsayawa tai galala tana me kallon daddy.
batare Mu'azam yace uffan ba kamo hannu inna yai suka fice daga gidan"
  "Tsayuwa daddy yai agun yai shiruuu yana me juyayin abinda yai be kyauta ba.daga ďaya yaji babu daďi a zuciyarsa"
"Su Mu'azam suna shiga kai tsaye ďakinta ya kaita tana shiga ya fice zuwa nasa ďakin.
Zama yai a bakin gado yana mai juyayin daddy haďi da tambayar kansa anya kuwa daddyn daya sanine.shidai a iya sanisa da iyayensa tunda ya taso yasha gani inna takaiyiwa daddy abinda yafi haka amma be ta6a ďaga hannu ya daketaba sai yau.kodan auren da yaine yasa shi canzawa?"
A bangaren innama irin abinda taketa tambayar kanta dashi kenan.sama da shekara ishirin da biyar tanayiwa HARUNA abinda yafi irin abinda tai yau amma be ra6a daga hannu ya daketa ba saiyau.lallai duniya juyi-juyi yau gareka gobe da wanika.
Da irin wannan tunane-tunane inna ta yini.hakan yasa daga ďaya yinin ranar jikinta a sanyaye yake.koda yaya Sani yashigo gani yanayin da take ciki yasa shi tambayarta lafiya?.
"Kin faďi masa tai sabida tasan bakan gadone dashi ba.yanzu saiya bisa har gidan Talatuwar yatada masu hankali.
Shima kansa daddy yinin ranar beshigo cikin gidansa ba.a gidan Talatuwa ya yini har dare.bayan isha jikin inna yai tsami,duk inda tajuya zataji yanayi mata ciwo.dak'ar ta lalla6a zuwa ďakin Mu'azam tasanar dashi batajin daďi.
Allah ya sauwake yace" haďi da mik'ewa rifa yajawo yasanya sannan yafice.chamis yaje ya haďo mata magugunar ciwon jiki yakawo mata.bebar ďakinba saida tasha.da kansa yake ciro mata yake bata haďi da ruwa.saida duk ra shanye kamar yanda me chamis ďin yace sannan yace ta kwanta.koda ta kwanta bebar ďakinba zama yai sukaci gaba da hira harda bacci ya ďaukota sannan yamik'e saida yaja mata kofar haďi da kashe mata wutar ďakin sannan yaje ya kwanta.
Cikin dare Mu'azam ya nemi bacci yarasa.duk irin abinda zaiyi dan bacci yazo yayi amma baccin yak'i zuwa.nan yashiga tunani iri-iri gana inna da daddy sannan kuma gana Rukky da daddy yasanar masa.cikin zuciyarsa yace"ohoo waya sanima tun zuwanta gidan take fuskantar haka daga uwar mijinta?.komai ya tuna oho.lumshe ido yai cikin zuciyarsa yace"Allah sarki Rukky..

MAKAUNIYAR RAYUWAWhere stories live. Discover now