MAKAUNIYAR RAYUWA

164 12 0
                                    

_______"Ni bance haka ba,amma gani nayi duk wata kulawa da zan bashi ba kamar uwarsa ba...Sofy kenan,yanzu na fahimce ki,kawai dai kinaso kicemin bazaki iya riƙemin Basik bane... A'a J-boy kada muyi haka dakai.har ga Allah ba haka nake nufi ba.gani nayi har yanzu Basik yarone yana buƙatar uwarsa kusa dashi.
Amma tunda ka kasa fahimta ta shi kenan babu komai...
Banza da ita J-boy yai,har taƙari maganar ta bece da ita komai ba.
Kujerar rover dake gefe yaja ya zauna haɗi da ciro wayarsa daga aljihu ya fara dannawa.
Itama komawa tai ta kwanta haɗi da juya masa baya.
Can kome yagani kuma oho,miƙewa yai ya ɗauki Basik dake lwance kusa da ƙafar Sofy ya ɗorasa a cinya.
Titi direct Meenal tabi har ta isa gida.tana isa ana kiraye-kirayen sallar asuba.
Gani gida rufe yasa Meenal bubbugawa haɗi da kiran sunan inna.takai minti biyar tana bugon ƙofa sann inna tajiyo muryan meenal kamar a mafarki.
A gigice ta falka,tana falkawa sake sauraro tai tana me cewa"kamar fa muryan Amina nake jiyowa a ƙofar gida.sake kiran da Meenal tai ne yasa inna miƙewa da sauri tana faɗi subhanallilahi inna'lillahi'wa'inna'illaihin...ta katse da tambayar kanta me kuma yakawo Amina cikin daren ga?yo kodai mijinta ne ya korota.duk tana tafene tana maganar.tana isa ta buɗe gida.
Inna na buɗe gida"Meenal ta rusa da kuka haɗi da kiran inna"J-boy ya koreni snn ya kwace Basik..hannu inna tasa ta kamowa Meenal nata hannu haɗi da cewa zomuje daga ciki.
Bayan su shiga ɗakine Meenal ta kwashe duk abinda ke faruwa ta faɗiwa inna.tanayi tana kuka.
Hakuri inna tabawa Meenal haɗi da rarrashi,shi kuma J-boy ɗin tace zaizo ya sameta..
Tunda hjy ta tashi sallar asuba taji gabanta na faɗi.inna'lillahi'wa inna'lillahi'wa'inna'illaihin raju'un kawai take faɗi cikin zuciyarta da haka har tasamu tai sallar asuba.har a lokacin hanakalinta be kwanta ba,gabanta be daina faɗi ba.
Gani haka yasa hjy ce"duk yanda akai akwai abinda ke faruwa,babu in da ya faɗo mata sai gidan J-boy.hannu tasa ta razo wayarta dake ƙarƙashin pilo, number J-boy ta binciko ta danna masa kira.dai-dai lokacin J-boy ya fito daga masallaci kenan,yana sagale da Basik a kafaɗarsa,sabida tare suka tafi masallacin.
Jin wayarsa na ringing haɗi da kiran sunan hjy kamar yanda yai setting,idan ta kira ya rinƙa sanar dashi itace ke kiransa.
Jin wayar ya fara magana,da your mom is calling you yasa J-boy saurin sauke Basik yasa hannu cikin aljihu ya fiddo da wayar,yana siddowa yai receiving call ɗin da sallama.
Cikin girmamawa ya gaidata kamar yanda yasaba ko a gaban idonta,harda duƙawarsa bayan su gaisa hjy ke tambayarsa kwanan su iyalansa.
    Murmushi J-boy yai snn yace"duk suna lafiya,gama Basik ɗin nan"
Da sauri hjy tace"bashi mu gaisa"
Karawa Basik wayar yai a kunne haɗi da cewa"ga hjy"
Koda aka kara masa wayar shiruuu Basik yai kamar wanda baya magana"
Gani haka yasa J-boy cewa"kai gaisuwa mana Basik,hjyce fa,hjynka".
Sann Basik yace"inni"dukkansu dariya sukai haɗi da cewa"lafiya ƙalau maigida na,ina mamanka?.
Cikin tsami baki irin na Basik yace"mama ta tafi...da sauri hjy tace"ta tafi ina Basik?.daddy ya koyeta.. subhanallilahi hjy tace..shima J-boy ɗin dake tsaye jin haka da sauri ya fisge wayar haɗi da kashewa..
Kafin waya a aljihu hjy tasake kira,duk da haka be ɗauki wayar ba har ya katse,ya kuma yunƙurin sake medawa cikin aljihu kenan saiga wani kiran yasake fshigowa dole yasa J-boy daga waya da sallama.lafiya?,abinda hjy ta fara cewa kenan.
Take ya fara inda-indan ta ina zai fara,gani kashi a ciki bayan magani yunwa yasa J-boy faɗi duk abinda ya faru, harda zubewar cikin Sofy snn yace Meenal ce ta zidda mata..salati hjy tai ta sanarwa ubangiji.ina Amina take? hjy ta jefi J-boy shi.
Shiruuu yai yakasa bata amsar tambayarta,saida ta sake magana snn yace"tana-tana gida..sai kuma yai shiru.
Wani gidan?.
Gidan su yace"..
"Yanzu sabida Allah ka kyauta kenan?daga jin magana baka tsaya kai bincike akan ba saika zattar da hukunci?"
A'a hjy,ban yanke hukunci ba saida nayi bincike,kuma nagano itace batada gaskiya..
Tou ka kyauta.yanzu ina Basik ɗin yake?.gashi nan.
"Nan ina?"
"Tare dani".
Kajirani ga ninan zuwa yanzu in Sha Allahu.ta kashe wayar ne haɗi da miƙewa,ba tare data canza hijabin dake wiyarta ba ta ɗauki pot tafice daga ɗakin zuwa asibiti.
Suna gama waya da hjy J-boy ya meda wayarsa cikin aljihu haɗi da kamawa  Hannu suka fara tafiya,suna tafe yana yimasa faɗi.da haka har suka ƙarisa ciki.
Lokacin idon Sofy biyu,jin anturo ƙofa yasata sauri meda idon ta rufe
Bayan J-boy ya zauna ne yasa hannu yana bubuga filon da kanta ke kai haɗi da kiran sunanta.yajima yana kiranta bata buɗe ido ba sai daga baya snn ta buɗe.
A hankali take buɗewa kace me baccin gaske ne haɗi da miƙe.
Suna haɗa ido tace dashi har ka dawo?.
Eh wlh nadawo,yaya jikin?.
"Jiki alhamdullhi"
Likita ya shigone bayan fitata?.
"A'a,babu wanda ya shigo"
"Ok kawai yace,snn yaci gaba da cewa"bayan na idar da sallah ina fitowa daga masallaci saiga kiran hjy.
Bayan mu gaisa ne nake sannar da ita,tace gatanan zuwa.
Shiruuu tai a fili amma cikin zuciya kuma tace"bari kagani.
Gyara kwanciyarta tai snn tabi Allah tabi gado ta narke haɗi da murtiƙe ido.
Da yake motar gida ne yasa bata ɗauki lokaci me tsayi ba ta iso asibitin.turo ƙofarta ne yasa J-boy miƙewa yanufo bakin ƙofar haɗi da yi mata sannu da zuwa.
Ƙara buɗe ƙofar yai saida ta shiga snn ya meda kofar yarufe.kujeran da yake zaune ya gyara zata haɗi da cewa"gagun zama hjy.
Hjy na zama ta meda kallonta ga Sofy dake kwance.kallo ɗaya tai mata tagano duk sharri ne irin nata,murmusawa tai ciki zuciya tace"ta yaro kyau take bata ƙorko.
"Maganar J-boy ne ya katse hjy.duƙawa yai a gabanta yana gaisheta.da fara'a ta amsa haɗi da tambayarsa yame jiki?.
Da sauri yace"
Jiki alhamdulli.
Bata wani jima ba tamiƙe da cewa"zan tafi, Allah ya ƙara sauki"
Ba tare da tatsaya wani magana ba,hannu tasa ta ɗauki Basik haɗi da cewa"zomuje gida.
Da sauri ya miƙa mata hannu ta ɗaukesa suka fice daga ɗakin.tana gaba J-boy na biye da ita a baya.bayan su fitane suka samu gu suka tsaya.
Hjy ta fara da yanzu sabida Allah ka kyauta kenan...me nayi kuma hjy?,wlh hjy duk abinda na faɗi maki in har akan Meenal ce gaskiya nake faɗi maki.kuma wlh ki tambaya kiji."waye zan tambaya..."Sofy nama,ita zama faɗi maki duk abinda yafaru.da kuma irin hakurin da takeyi da ita.
Wlh hjy bazakisan waye Meenal ba sai kin zauna da ita.batun yanzu ba Meenal ke niman hallaka Sofy,gashi duk irin abin alkhairin da zatai mata ko taiwa yaronta bata gani..yanzu sabida ta kwashi ƙarya ta faɗi maka shine kai kuma ka yarda ko.tou bari kaji JIBRIN wlh-wlh-wlh in har kasake kasani AMINA bazan yafe maka ba..jin haka yasa gaban J-boy mummunar faɗi,gam-gam-gam.nan yafara daya sani furta sakin da yai mata.shiruu yai yai kwasake,duk irin faɗar da hjy keyi masa bece da ita komai ba.snn taci gaba da cewa"zanje na dawo da ita ɗakinta kuma wlh idan har naji wani abu makamancin haka yasake faruwa babu ni babu kai sai dai kanemi wata uwar amma baniba.snn ta juya taci gaba da tafiya tana faɗin yaron banza yaron yofi kawai.
Wanda besan me sosa ba.tana shiga mota kai tsaye gidan su Meenal ta nufa..
daddy da Yaya Mu'azam suna dawowa daga masallaci da yake yau a inna ce keda girki kai tsaye ɗakinta yanufa shida Yaya Mu'azam da sallama suka shiga, daddy na gaba Yaya Mu'azam na biye dashi a baya suka shiga ɗakin inna.
Lokacin Meenal na sallah,ita kuma inna tariga ta idar da nata sallar.yana shiga daga cikin karaf ya hango meenal na sallah.ba tare daya zauna ba yace"bakuwa kikai?"
     Wacce baƙuwa?Amina ce. Subhanallilahi
Amina kuma?.
Himm inna tace".
Mu'azam dake zauna cikin zuciyarsa yace"Allah ya kyauta"
Koda daddy ya zauna bece komai ba har sai da meenal ta sallame sallah snn.juyowa tai ta gaidasu snn Yaya Mu'azam ke tambayarta dalilin dawowarta gida.
  "Nan Meenal ta zayyana masu dukkani abinda ya faru.tanayi tana kuka.
      Shiruuuuu Yaya Mu'azam yai na ɗan wani lokaci snn yace"ina shi megidan naki yake?.
Yani gida Meenal tace"harya buɗe baki da niyyar magana sallamar hjy ce ta katsesu.dukkansu da fara'arsu suka amsata.
     Gani taja ta tsaya yasa daddy cewa"bismillh snn ta ƙarisa daga ciki.bayan ta zauna suka gaisa cikin girmamawa,tun kafin daddy yai magana hjy ta taresa da bada hakuri.tana duƙe a gabansa guiwa bibbiyu tana bawa daddy hakuri haɗi da alkawarin hakan bazai sake faruwa ba.duk yanda inna daddy sukaso yin magana hjy ta hana.gani haka yasa Yaya Mu'azam cewa ta tashi su tafi kawai, Allah ya kiyaye gaba.jin haka yasa Meenal rusawa da kuka harta buɗe baki zatai magana da sauri hjy ta dakatar da ita da cewa"banason jin komai daga gareki.tashi kawai muje.hannu hjy tasa ta kamowa Meenal dake zaune nata hannu haɗi da cewa tashi muje.bayan Meenal ta miƙe hjy tasake duƙawa taiwa su daddy godiya snn suka tafi.
Bayan su shiga mota ne hjy ke tambayar Meenal abinda ya faru.
Nan Meenal ta zayyana wa hjy komai,tanayi tana kuka.
Uhmm hjy tace snn taci gaba da cewa"JIBRIN!JIBRIN!!JIBRIN!!! Allah ka shirya min shi.hakuri kawai hjy taita bawa Meenal haɗi da cewa insha Allahu komai ya kusan zuwa ƙarshe.
Har gida hjy takai Meenal hakuri ta sake bata snn taci duk abinda take buƙata ta sanar da ita,snn sukai sallama..
       
       "Tun bayan rabuwarsa da Surry ta addabesa da kira,gani Sofy ta fara ɗagowa yasa J-boy kashe waya,duk kiran da tai baya shiga.
Gani har kwanan su biyu ba'a sallame su yasa J-boy sanfawa tunda ya fita sallar azahar be sake dawowa asibitin ba.yana fita gida ya koma yai wanka ya sharya cikin ƙasaitaccen shiri yafita.da yake tunda Meenal tadawo gidan be magana da ita.hakan yasa koda yazo fita tana  zaune a falo yazo ya wuceta ba tare da yace da ita komai ba..
Kwana Sofy uku a asibiti,babu J-boy babu alamarsa,tayi kiran harta gaji wayarsa baya shiga.gani haka yasa Sofy niman sallama.Meenal na zaune a falo Sofy ta turo ƙofa ta shigo.gani Meenal ce zaune a falo yasa Sofy Jan dogun tsaki haɗi da cewa banza kawai.da sauri ta ƙarisa daga cikin ɗakinta.
  Ƙyalƙyalewa da dariya Meenal tai haɗi da cewa"Allah ya ƙara.tun da J-boy yabar gida be dawo ba,yacan yana cin duniyarsa da tsinke shida Surry.
    A ɓangaren hjy kuwa kullum saita kira Meenal ta tambayarta halin da suke ciki.
  
       ****
Tun daga ranar da akai Baffa asibiti Rukky keta ɗawainiya dashi.daga iya har Yaya Bala su iya ƙoƙarinsu a kansa amma Baffa baya gani,komai idan ba Rukky ce tai masa ba bayane.hakan yasa iya tai fushi tace bazata ƙara tafiya asibitin ba.tunda Rukky yake aure yaje ya zauna da ita.
Babu irin hakurin da Yaya Bala bebawa iya ba amma taki zama dole haka ya gaji ya kyaleta.
Da yake in da aka tura su Ƙamaru babu network sosai hakan yasa ba kullum yake samu yai magana da gida ba sai ranar da suka samu network.Rukky dake zaune da Baffa kamar da wasa tai trying number sa,cikin sa'a yashi.da sauri ta miƙe tabar ɗakin.
Ƙamaru dake bakin aiki ji kawai yai wayarsa na ƙara.da sauri yasa hannu ya ciro.gani number Rukky ce cikin rawan jiki ya ɗaga haɗi da sallama.cikin girmamawa ta gaidasa haɗi da tambayarsa yaya aiki?.
Alhamdullhi yace snn ya tambayi su iya da Baffa da kuma yara.duk suna lafiya tace,su jima suna hira snn take sanar dashi rashin lafiyar Baffa Amma tace da sauri.
Duk da haka Ƙamaru be yarda ba cewa yai idan tana kusa dashi ne bata shi wayar suyi magana.
   Kowa tai daga ciki ta karawa Baffa wayar a kunne sukai magana da Ƙamaru snn Ƙamaru ya yarda.besuyi sallama ba saida yace wa Rukky ta lissafa masa duk abinda tasan yaƙare masu.nan Rukky ta lissafa masa snn sukai sallama da cewa zataga alert.zuwa anjima.
   Suna gama waya kenan Ugochuwu yafito yana sallamar ƙamaru.nan Ƙamaru ya ɗauki kuɗi ya bashi yasaidan yashi cikin gari Dan Allah ya sanyawa Rukky a acc.
    Ba'ayi awa hudu ba Rukky taga alert ya shigo mata,taji daɗi sosai tayi ƙoƙarin kiran ƙamaru domin tai masa godiya amma number yaƙi shiga.bayan Ugochuwu ya gama abinda shigo dashi cikin garine a hanyarsa ta komawa dajin da suke aiki ya haɗu da wata budurwa da alama abinci take saidawa.
  Tana zaune kusa dashi.daga ita har shi babu wanda yaiwa ɗan uwansa magana saida sukai nisa sosai,snn magana ta haɗasu. Ugochuwu ne ya take mata ƙafa da takalminsu ta sojoji ba tare da sani ba.
Ihu tasa haɗi da kiran my leg my leg,tanayi tana karkarɗa ƙafar.
Da sauri Ugochuwu ya ɗaga ƙafar haɗi da cewa"sorry ban sani bane.babu komai tace,amma duk da haka bata daina jininin ƙafarta na zafi ba.gani haka yasa Ugochuwu cewa"komai zasu sauka ne yakaita asibiti?.
   Da sauri tace a'a ya bari kawai.da haka har suka kama hira a cikin hiran ne yake tambayarta abinda take saidawa?.
    Ugochuwu yai tambayar ne sabida ganinta da yai riƙe da kayan miya haɗi dasu pilatain.eh tace masa.
   Cikin ba'a yake cewa"mai zai hana bazata rinƙa kai masu in da suke ba?.
  Itama da yake abin nemane ya samu yasa bataƙi tayin da yai mata ba.gani sukai in da zata sauka ne yasata cewa"a faɗi mata wajan da suke.nan Ugochuwu ya faɗi mata tace"insha Allahu gobe zata kawo masu abincin. Haka haka suka rabu,amma cikin zuciyar Ugochuwu gani yake kamar ba zuwa zatai ba,sabida nisan da gun yake dashi tsakaninsa da cikin gari.
    
     Bayan la'asar saiga Yaya Bala yazo asibiti.
   Cikin girmamawa Rukky ta miƙe ta bashi gu ya zauna,bayan ya zauna ne suka gaisa.bayan su gaisa ne yake tambayarta Yaya jikin Baffa ɗin?.
   Da sauki tace.duk lokacin Baffa na bacci sabida be Dade da shan magani ba.su jima suna hira snn Baffa ya tashi daga baccin da yakeyi.
  Gani yana yunƙurin miƙewa yasa Rukky tafiya da sauri tallafosa ta jiginashi da bango.bayan ta jigina sane taje ta ɗibo masa ruwa tazo in da yake tana miƙa masa..
   Kai ya kaɗa alamar a'a bazai shaba.
   Meda ruwan tai ta ije.miƙewa Yaya Bala yai taje bakin gadon ya zauna kusa da Baffa hannu yasa ya kamowa Baffa nasa hannu,a hankali yake jinsa da hira.
   Gani haka yasa Rukky cewa Yaya Bala ita zata tafi,amma tana gama abinci zata dawo.
   Adawo lafiya yace da ita".
     Rukky na fita daga asibiti saida ta fara zuwa banking,domin cire kuɗin da Ƙamaru ya tura mata.
   Tana isa ATM taga uban layi,tsayawa tai tai shiruuu tana tunanin ta ina zata fara.gashi idan tace zata tsaya har sai layi yazo kanta zatayi daren abinci.
Dan ƙaramin tsaki taja haɗi da juyawa"karaf tai karo da wann mutumi da suka taɓa haduwa.da sauri Rukky taja da baya haɗi da cewa"Subhanallilahi.
Murmushi yai mata snn yace ina zaki.....?????

 
    

MAKAUNIYAR RAYUWAWhere stories live. Discover now