MAKAUNIYAR RAYUWA

126 14 2
                                    

*MAKAUNIYAR RAYUWA*
________________________________

*AREWA WRITES ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________

~DIDECATED TO~
*ANTY FAUZIYA*
     *ƳAR AMANA*

https://www.facebook.com/104534761033461/posts/109559843864286/?app=fbl

                         *PART THREE*
                                  *PAGE 6*

*BISMILLAHI RAHMANI RAHIM*

______"A hankali yake tafiya yanayi yana janta da hira da haka har sukai nisa,gani nisan da sukai ne yasa Rukky tambayarsa ina zamu?.
Cikin raha yace"tafiya zanyi na saidaki.
Gaban Rukky ya faɗi cike da tsoro ta zaro ido haɗi da cewa"na shiga uku,sai dani kuma...
Besan lokacin daya rusa da dariya ba snn yace sosai kuwa..Uhmm kawai tace"daga snn bata kuma cewa komai ba.
Gani har a lokacin beyi faki ba yasa ta kasa hakuri saida ta kuma tambayarsa.A lokacin ne yace"inda zamu zauna muyi hira ba tare da wani ya ganmu ba zamu..
Himm tace..
Saida sukai nisa sosai ya tabbata babu wanda zai gansu gidin wasu bishiyoyin mangwaro da kyashu snn yai faki,yana faki fitowa yai snn yace da ita tafito, dukkansu baya suka koma snn ya sake meda murfin motar ya rufe.
Yana rufewa matsawa yai dab da ita,duk a lokaci gaban Rukky be daina faɗuwa ba.
Kanta na ƙasa ta kasa ɗaga kai bare su haɗa ido.
Murmushi mutumi yai cikin wani irin salo yace"baby kunyata kikeji kome?.
Uhmn dai ta kuma cewa,gani har a lokacin kanta na ƙasa yasa mutumi sanya hannu ya kamo fuskanta a hankali yake ɗagawa idanusa kuwa na kansa ƙyam bayako ƙibtawa.
Rukky dake zaune ji tai wani irin abu ya tsirrrrgo mata tun daga kansa har zuwa ƙafafuwansa.da sauri ta janye fuskanta daga hannunsa haɗi da cewa"Dan Allah kabari..
Ba tare daya musa mata ba yace na bari baby,kin san bazanyi maki dole ba duk abinda kikeso nama shi nakeso, abinda bakiso kuwa har abadan nima bazanso wanan abunba.
My Queen bazan iya mantawa da keba sabida ƙaunarki, ƙaunarki a zuciyata abune rama gushewa ina sonki fiye da yanda nake son kauna,ina sonki fiye da yanda kike tunani,ina sanki my baby snn kuma a shirye nake Dana ɗauki kowani irin hukunci yayin da asirinmu ya tunu,wlh wlh wlh my baby a kanki a banida wani abu da zan wanda zan koma ina dana sani,a kanki a shirye nake da duk irin hukunci da za'ayi min a kanki a shirye nake dana aikata komai,domin kuwa duk wanda yai gigin rabamu sai naga bayansa.
My baby Allah ya jarabceni da sonki da ƙaunarki.
Baby nasan ba lallai ne ki yarda da abinda zan faɗi maki ba,amma nidai nasan har ga Allah sann kuma har cikin zuciyata gaskiya nake faɗi maki.
Bayan matata ta gida wacce nake aure a yanzu haka ban sake gani wata ɗiya mace naji tayimi kota birgeni ba saike baby, baby ina cikin wani hali,idan har ba sameki ba komai zai iya faruwa.
Nasan zakiyi duba da auren da kike dashi ko,tou wlh ba laifina bane,hasali ma ban San yanda akai na kamo da soyayyarki ba,dan Allah ki taimake ni,ki taimaki rayuwa ta baby..
Duk maganganu da mutumi keyi shiruuuuu kawai Rukky tai,domin gaba ɗaya kanta ya ɗaure gabanta sai faman dukan uku-uku yakeyi.
Cikin zuciyarta kuma tambayar kanta takeyi wai da gaske ne abinda yake faɗi ko kuma daɗin bakine irin tasu ta maza...damko hannunta da yai ne yadawo da ita daga tunanin da takeyi.
Kamo hannunta yai ya sanya sa cikin nasa hannu snn ya riƙe da ƙarya.
Zaune dake zaune ji tai gabanta na mata wani irin ga uban ruwan dake ta zubowa daga cikin jikinta zuwa pan ɗinta.
Lumshi ido tai snn ta fara ƙoƙarin zame hannunta daga hannu.
Jin haka yasa mutumi ƙare ƙanƙame mata hannu haɗi da tambayarta yahhh dai?.
Jiki a sanyaye tace"zani gida.
Da sauri yace"tun yanzu?.
Eh wlh"..
Cikin wani irin salo me ɗauke hankali yace"why?"
"Sabida nabar yara".
Gaskiya kuma fa hanake,tou yanzu yaya zamuyi?,domin har yanzu ban gaji da gani wanan kyakkyawan fuskar taki ba.
Uhmm kawai Rukky tace snn ta fara ƙoƙarin buɗe motar ba tare da tai masa magana ba.
Gani haka yasa shi cewa"okay bari muje ko?.duk yanda Rukky taso buɗe motar ta kasa sabida yariga daya rufe ta ciki.kasa kamota yai ta dawo ta zauna dakyau snn yace"lokacin da zaki fita ina kikace zaki?.
Ba tare data kallesa ba tace"kasuwa"
Tou yanzu idan kika koma gida hannu Babu komai me zakice?.
Shiruuu tai tace dashi komai ba.
Murmushi yasake yi snn yace"yanzu abinda za'ayi shine muje na saukeki ki biya kasuwa kiyi siyayya koda kaɗan ne snn ki ƙarisa gida,kinga idan kikai haka kin cire zirgi da kokwanto a zukatan mutane ko?,hannu yasa cikin aljihunsa ya ɗibo kuɗi masu yawa yamiƙa mata.
Da farko kin amsa tai,gani ya nace mata ne yasa ta amsa snn tai masa godiya.
Babu komai my baby kinfi da haka.
Snn yaci gaba da cewa"duk da baki tambayeni waye niba amma zan faɗi maki domin gani nayi ya dace kisan da wanda kike tare.
Da farko dai ni sunana KHAMEES ni tsohon jami'in tsarone wanda na jima ina aiki a ɓangaren sojan sama,duk lokacin da za'aje yaki walau anan ƙasar ko wata ƙasa dani ake zuwa,amma yanzu haka nayi retire,bayan retire ɗina na koma har kan siyasa,wanda na riƙe muƙame da dama,kama daga kan ɗan majalisar jaha har izuwa ta tarayya yanzu haka senator ne ni.
RUKAYYA...jin ya ambaci sunata yasa gaban Rukky yankewa ya faɗi,sabida tunda yake be taɓa kiran sunata ba sai a wanan karo..
Baza ido da kunne tai domin jin abinda zai faɗi.
Yaci gaba da cewa"dan Allah dan Allah RUKAYYA inaso duk wata hulɗa da zamuyi dake yazamo sirrin,kin san babu abinda baya buƙatar sirri a rayuwa, koba komai banaso mu ɓata tarihin rayuwarmu nida ke.
Snn kuma kada ki mance da kalmar da hausawa ke faɗi duk abinda namiji yai adone akan mace.
RUKAYYA inaso ki zamo me rike Siri koda da wasa banaso wani yaji tsakanina dake,badan komai ba RUKAYYA banaso ace sanadiya na sunanki ya ɓaci.
Insha Allahu RAKIYA tace"snn yace"bari na ƙarisa dake kada dare yayi ko?.
Buɗe motar yai duk suka fita suka koma gidan gaba snn yajasu sukabar wajan.
Gani an kusa da kasuwa yasa Rukky cewa"saukeni anan ma yayi.. murmushi yai mata snn yace"A'a bazan iya saukeki anan ba.
Bari dai na duba inda ya tace snn na saukeki.
Saida sukai nisa da kasuwa sosai ya tabbata babu wani wanda zai gansu snn ya sauketa haɗi da cewa ta gaida masa abokinsa Muhammed da ƙanwarsa..tou kawai tace.
Da sauri tabar gun ta ƙarisa kasuwa,koda ta shiga kasa siyan abinda takeso tai kawai yan tarkace ta siyo ta fito ta sami napep da zai kaita gida.
Rukky na isa gida saita taje ɗaki ta ije kayan dake hannunta snn taje ɗakin khaidijat domin kiran su Muhammed.
Gani lokaci anfara kiraye-kirayen sallar magrib yasa Rukky sauri domin kada sallar ya wuceta,koda ta shiga ɗakin khaidijat ganita tai zaune tana kallon ita da yara,kai kawai ta kaɗa snn ta sallama,jin sallamarta ne yasa su Muhammed da Muhasana duk suka miƙe sunayi mata oyoyo.
Juyawa khaidijat snn haɗi da cewa kin dawo?.
Eh tace,snn tace"bari naje nayi sallah,saida taiwa su Khairat magana dasu tashi suje suyi sallah snn ta juya zuwa ɗakinta.
Bayan Rukky ta ƙare aikinta tai shirin kwanciya,koda ta kwanta babu abinda kema yawo a zuciya ya hanata sukuni sai daɗaɗan maganganu  KHAMEES yaita faɗi masa,kora tai yunƙurin kauda abin a ranta amma saita kasa.
Tana cikin haka kenan saiga saƙon alhj KHAMEES ya shigo wayarta,koda ta karanta bata meda masa reply ba,ɗora wayar tai akan ƙirjinta taci gaba da tunani,daren ranar kusan kasa bacci tai sabida tunani.
Al'amarin ƙamaru kuwa tattarasa tai ta jingine a gefe,ko gwada kiransa ma ta daina yi bare yaga kiranta yaki ɗauka ko kuma idan ma ya ɗaga ya faɗi banza.
Har kokin rayuwarta kawai takeyi,kira da saƙo kuwa babu ƙabƙabtawa duk lokacin da alhj KHAMEES zai kira Rukky maganar sa ta farko shine yara.
Ina yara suke,suna lafiya,tai masu wanka ta basu abinda.
Hakan ba ƙarami farantawa Rukky rai ya keyi ba.
Gani bata damu data kirasa ba sai dai shine ke kiranta yasa alhj KHAMEES ƙorafin wai bata sonsa shine kawai yake sonta.
Kahuri Rukky ta bashi snn ta faɗi masa dalilinta na rashin kiran da batayi masa.
Da haka rayuwa yaci gaba babu ƙamaru babu dalilinsa.
Daga iya har yaya Bala hankalinsa ba ƙaramin tashi yai ba.
A ɓangaren Rukky duk da haɗuwa da alhj KHAMEES da tai amma beyi ta daina kiran ƙamaru.lokaci-lokaci saita nemi number wani lokaci ya shiga amma bazai ɗaga ba wani lokaci kuma baya shiga.
A ɓangaren su daddy da inna kuwa kullum ciki faɗa suke domin kullum inna cewa take tagaji da irin zaman da takeyi a gidan mijinta musanman ma yanda magana ya karasa gari duk inda kashiga maganar kenan ƙamaru ya tafi aikin soja ya mance da iyayensa da kuma matarsa da yara.
Gidan suna gidan biki majalisu daga Yaya Mu'azam har daddy basujij daɗin yanda aketa yayata magana.
Idan abun ya ciyo inna shiryawa takeyi taje ta sami iya har gida ta zageta tasss son ranta ba tare da sani daddy ko Yaya Mu'azam ba.
Duk da masifar iya amma a wanan karo baya aiki domin a duk lokacin da inna zatazo gida da faɗa hakuri kawai iya ke bata snn tace''insha Allahu zatasan abinyi.
Gani haka yasa duk abinda Allah ya hurewa daddy da Yaya Mu'azam suke kaiwa Rukky.
Shiko Yaya Bala kwashi yara yayi ya sanyasu a makarantar dasu Khairat suke zuwa..da yake pravent school ne ba ƙaramin kuɗi yake kashewa ba idan term yai.class ɗaya aka sanya su wato nursery 1

    Bayan wata hudu

****
    Tun bayan rabuwarsa da Sofy J-boy ya tare a gindin Surry wani lokaci sai ya kwana biyu Meenal bata gansa ba,tun tana kaiwa hjy ƙaransa har ta gaji ta hakura ta zubawa sarautan Allah ido.
Duk abinda ya rarumo agun hjy Surry yake kaimawa.
Gani Yana niman medata ATM machine yasa hjy yanke shawarar medasa a bakin aikinsa.domin kuwa duk yanda goma ta lalace tafi biyar albarka.
Duk yanda yakai ga kashewa matan waje kuɗi dole yaiwa Meenal idan beyi mata yauba zaiyi mata goma,idan ma beyi mata ba dole yaiwa Basik.
Musanman ta kirasa tace''yazo tanason ganisa idan yasamu lokaci.
J-boy beyi kasa a guiwa ba wajan amsa kiran mahaifinsa,take yabar abinda yakeyi ya kami hanya domin jin kiran hjynsa.
Nan da nan ya isa gidan hjy,da sallama ya ƙarisa daga ciki.
Hjy dake zaune a falo ta amsa snn tace"dashi bismillh.
Yana shiga ya zube a gabanta kamar yanda ya saba snn yace"da ita barka da warhaka,Yaya zafi?. Da yake lokaci na zafine.
Alhamdullhi tace"bayan ya zauna ne tafara dani masa nasiha ta jima tana yi masa nasiha snn tace"yace gun alhj KABIRU yace"itace ta turasa".
Tao yace"be zauna wani hira ba sallamarta yai yana fita ya nufi gidan alhj KABIRU da yake lokacin yamma yayi ba lallane idan yaje office ya samesa ba shiyasa ya nufi gida,domin yasa gidan alhj KABIRU ya tashi daga aiki babu inda yake tafiya sai gida.
Kai tsaye gida alhj KABIRU ya nufa,da yake ba wani nisane tsanisu ba yasa be ɗauki lokaci ba ya isa gida.
Da sallama ya shiga,yana shiga sukai karo da hjy a falo, duƙawa yai har ƙasa ya gaidata haɗi da tambayar alhj.
Yana ciki tace dashi,bari naje nai maka magana dashi.
Tou J-boy yace,tana shigowa yahau kan kushi ya zauna.
Hjy na shiga suka fito tare , J-boy na gani fitowarsu da sauri ya miƙe har saida alhj ya zauna snn shima ya zauna.
Bayan su gaisa ne J-boy yace"hjy ce ta turoni gunka...
Eh ina sane da zuwanka.dama ba komai bane yasa ta turoka akan maganar aikinka ne...da sauri J-boy yace"aiki kuma,wani irin aiki?.
Alhj KABIRU yaci gaba da cewa"tun farko itace tace a sallameka daga aiki sabida rashin jin maganarka,babu yanda beyi da ita ba da tayi hakuri ta rabu dakai amma taki yarda da haka.nima kaina dana zauna nayi nazari naga hakan shine dai-dai,domin kuwa idan bata wanan hanyar bace za'a hukuntaka babu wata hanya.
Shiru J-boy yai yana me sauraran maganganu alhj KABIRU.
Alhj KABIRU yaci gaba da cewa shine tasa yanzu a medaka a bakin aiki amma da sharaɗin...tun kafin J-boy yaji sharaɗin yace"na amence koma ta menene..dariya alhj KABIRU yai snn yace"sharaɗin shine sai kayi mata alkawarin bazata sake niman matan banza ba..jikin J-boy na rawa yace ehh wlh naji na ɗauka, daga yau na rabu dasu kenan koma waye su.dariya alhj KABIRU ya kuma yi snn ya dauki key ɗin office ɗinsa yabasa.hannu babbu J-boy ya amsa snb yai masa godiya....



Dan Allah kuyi hakuri da typing error,duk da nasan ba editing nakeyi ba amma error ɗin yau yafi na kullum muni, I'm sorry plsss kuci gaba da hakuri dani dan Allah.ngd sosai





📚✍️

MAKAUNIYAR RAYUWAWhere stories live. Discover now