MAKAUNIYAR RAYUWA

139 8 4
                                    


*MAKAUNIYAR RAYUWA*
________________________________

*AREWA WRITES ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________

~DIDECATED TO~
*ANTY FAUZIYA*
     *ƳAR AMANA*

https://www.facebook.com/104534761033461/posts/109559843864286/?app=fbl

         *PART THREE*
              *PAGE 8*

*BISMILLAHR RAHMANI RAHIM*

______"A guje alhj KHAMEES ya nufi titi haɗi da faɗin na shiga uku na lalace.
Wayyoo Allah Rukky Rukky rukky.sunan da alhj KHAMEES yaita memetawa kenan,can nisa ya hango jama'a su tsattsaya kowa da abinda yake faɗi,gani haka yasa alhj KHAMEES ƙara guje da yakeyi.
Yana isa gun bibige mutune dake tsaye yai ya kutsa ciki,gani ƴar akuyace kwance matanciya yasa alhj ajiyar zuciya haɗi da lumshe ido.
Duk jama'ar dake gun shi suka koma kallo.
Ba tare daya ce dasu uffan ba juyawa yai ya koma.
Cike da mamaki suke binsa da ido kowa da abinda yake faɗi a kansa.
Ashe koda Rukky ta fita daga hotel baya bi titi ba ta baya tabi saida tai nisa snn ta taaya ta hau napep.
Rukky na shiga sukai karo da Khadijat,gani yanayinta yasa Khadijat tambayarta da daga ina kuma haka?.
Jikin Rukky ba rawa tace"unguwa naje..bata tsaya ta jira jin abinda Khadijat zata kuma cewa"ba da sauri tanufi ɗaki.
Rukky na shiga faɗawa tai kan kushi ta rusa da kuka,kuka take wiwi babu ƙabƙabtawa.
Kai kawai Khadijat ta kaɗa domin jikinta be bata ba,sake bin Rukky tai ɗakin.
Tana shiga taga Rukky na kuka,da sauri ta ƙarisa inda Rukky take hannu tasa tana ƙoƙarin ɗagota haɗi da tambayar lafiya?. Kwace jikinta tai tasake kifa kaita taci gaba da kukanta.
Duk irin tambayar da Khadijat taiwa Rukky Rukky batai magana ba,gani haka yasa Khadijat samu guri ta zauna,ido kawai ta zubawa Rukky tana meyi mata kallon tuhuma,abubuwa kala-kala suke zuwama Khadijat a zuciya sai dai har a lokacin bata daina tambayar Rukky ba.
Rukky bata tanka mata ba saida tai kukan daya isheta snn tace"mashine ya bugemu... subhanallilahi Khadijat tace"snn ta sake jefa mata tambaya garin Yaya?.
Shuruu Rukky tai tana me share kwalla.
Cikin zuciyar Khadijat kuwa sake tambayar kanta takeyi da ina Rukky taje da har mashin ya bugeta,bayan duk fitan da zatayi saita sallameni koda ko bata faɗimin inda zata ba.
Gani tsareta da ido da Khadijat tai mata yasa Rukky miƙewa da sauri tayi cikin ɗaya.
Sake binta da ido Khadijat tai,har Rukky ta shige bata kauda idonta daga kallon Rukky ba har saida Rukky ta shige.kama haɓar bakinta tai tana me mamakin Rukky ta jima a haka can daga bisani kuma tace"koma menene idan yai tsami zamuji koda ko ba'a soba.
Miƙewa tai ta fice daga ɗakin.
Koda Rukky ta shiga cikin ɗakin ci gaba da kuka tai tana me data sani biyewa zuciyarta da har alhj KHAMEES yaci galabarta.
Cikin zuciyarta tace"kaicon kin Rukky,ina wayonki ina iliminki ina tsoron Allahrki duk suka tafe?,take taji ta tsani kanta...
**Duk inda su Yaya Bala suka kai sai su faɗiwa ƙamaru,da haka har suka isa suna isa suka kirasa suka sanar dashi gasu su isa,yanzu haka suna tashar daya faɗi masu su sauka a gun.
Cikin dajin daɗi da murna ƙamaru yace"ga shinan zuwa ya saukesu.
Tou yaya Bala yace"gefe guda suka koma suna jiran zuwan ƙamaru.
Ƙamaru na gaba magana dasu miƙewa yai ya ɗibe ruwa zuwa bayi domin wanka.
Yana shiga SHUKHURAT ta ɗauki wayar ya kashe gaba ɗaya snn tai ficewarta da wayar.
Ƙamaru be ɗauki dogon lokaci a bayi ba yafito koda ya fito ya shirya dogowar riga kawai yasa snn ya samu gu ya kwanta.
Tun daga lokacin daya shiga bayi be sake tuna wani magana makamanci su Yaya Bala ba.
Su Yaya Bala da suke tsaye suna jiransa, bini-bini sai iya tai magana"har yanzu be isa bah?.
Eh kawai Yaya Bala cewa"gani tafara damuwa yasa Yaya Bala sake kiransa,sai dai a wanan karon wayar a kashe yake..
jin shiru har a lokacin ƙamaru bezo ba ɗauko waya yai ya sake kiran numbar ƙamaru sai dai a wanan karo be samesa ba.
Duk da haka saida ya gwada kira har sau uku customer care na cewa"a kashe wayar yake.
Cike da mamaki Yaya Bala yace"badai kashe wayar yai ba?,ko kuma matsala cajine?.
Duk shi kaɗai yake maganarsa ba tare da iya taji ba.
Shiru-shiru ƙamaru be zoba ba har shabiyun dare, jin tsutsaye su fara kuka gashi ƙafa ya ɗauke sai tsirarun jama'a wanda ba'aza rasa ba yasa iya tahau masifa tana cewa"itafa yunwa takeyi, sabida Allah ace tun safe mutum besa komai a cikinsa ba,ita wlh bazata iya ba,duk yanda zaiyi sai dai yayi.
Bayan ta gamawa Yaya Bala nasa kuma ta koma kan ƙamaru tana faɗin yanzu ya rasa wanda zai wulakanta sai ita?lallai Allah yai ɗan is....da sauri Yaya Bala ya tare da dan Allah tai hakuri,snn kuma tai masa uzuri babu mamaki aikine ya tsaresa ko kuma ma yana hanyan zuwa ɗaukarsu.
Humm iya tace"
Can ya hango me shagon kayan tireda,zo muje yace wa iya.
Suna isa bakin shagon saida ya tambayi me tiredan abinda yake saidawa,bayan mutumi ya faɗi masa ne ya juya ga iya ya tambayarta me zataci?.oho tace"dashi"
Ina zuwa yace"gani zai tafi ya barta yasa iya cacumesa haɗi da tambayar ina zaka ka barni ni kadai a nan?.
Abinci ne zan siyo maki..
A'a ban yarda ka barni ana ba,sai dai muje tare.
Tou yace"ɗaukar mosgo ɗin kayanta yai snn suka tafi,suna tafe tana balbale masa da masifa.
Wani irin ƙulu-ƙulun baƙin ciki ne ya kama Yaya Bala,cikin zuciyarsa yana cewa"yanzu nine kamaru zaiyi wa haka,inda yasan ba shida lokacinmu daya faɗi mana tun farko da bamu zoba,amma babu komai.
Daga shi har iya kowa da zancen zucin da yakeyi.
Da haka saida suka karaɗe tashar basu samu abinci ba,
Masu shagunar kayan sanyin ma basu wuce mutum biyu zuwa uku ba.
Gani haka yasa Yaya Bala tambayar iya kodai ya ciye mata buredi da coc ne?.
Jiki a sanyaye tace"Yaya zanyi?.
Ƙarisawa sukai bakin shagon snn ya siye mata.
Gani becin dake gefen shagon yasa Yaya Bala cewa"su zauna,babban buredi ya amsa masu da coc ɗin gora  ɗaya ɗaya.
Iya naci tana faɗin sake kwadawa ko Allah zaisa ya shiga, bini-bini sai Yaya Bala ya sake gwada kiran ƙamaru amma har a lokaci wayar a kashe yake.
Tunda SHUKHURAT ta fita bata dawo ba sai misali ƙarfe ɗayan dare snn ta dawo,tana shiga guri ta samu tai kwanciyarta snn kamaru ya jima dayin bacci.jin motsinta ne yasa kamaru falkawa hadi dayi mata sannu da dawowa.eh kawai tace"dashi snn tai kwanciyarta.
Shima meda kansa yai yaci gaba da baccinsa sabida fitan safe yakeso yai zuwa gurin aiki.
Suna cikin cin buredi kenan Ugochuku ya faɗo wa Yaya Bala a rai, yawwa yace"
Iya dake zaune tace"lafiya ko kasamesa ne?.
A'a, ban samesa ba,tunowa nayi da abokinsa bari na kirasa na sanar dashi gamu a tashi,idan ma bazai samu zuwa ya ɗauke mu ya taimaka mana ya tayamu nemo kamaru da yah..
Eh wlh gwada mugani..
Cire waya yai daga aljihu ya binciko numbar Ugochuku,sai kashhh koda ya kira numbar itama a kashe yake.
Uhmm kawai iya tace,snn taci gaba da cewa"yanzu nine kamaru zaiyi wa haka?lallai duniya.
Dan Allah dan Allah kiyi hakuri kiyi masa uzuri iya..humm take cewa"snn ta shiru
sai abin ya sake ciyota snn taci gaba da masifarta.
Duk da shima ransa a ɓace yake bisa ga abinda ƙamaru yai masa,amma dole ya danne masa domin idan har ya nuna idan har ya nuna tasa ɓacin ran kaɗanne zai rage iya bata tsinewa ƙamaruba.
Yaya Bala be nemi taimakon kowa kowani ɗan Union ba sabida yanda yaga yanayin gari yake,da alama idan yaje ninam taimakon gurin kwana su hanasa haka yasa beje ko ina ba sukai zamansu a gun har zuwa gari ya waye.

MAKAUNIYAR RAYUWAWhere stories live. Discover now