MAKAUNIYAR RAYUWA

134 6 5
                                    


_*MAKAUNIYAR*_
             _*RAYUWA*_

*_🌈KAINUWA WRITERS✍🏻 ASSOCIATION_*🤝🏻

_*fcbk group*_
_*mmn uswan*_
*page Hauwaszaria*

https://www.facebook.com/379407779489539/posts/518531808910468/?app=fbl

editing is not allow⚠

         *PAGE 7*
                   *PART 2*

_*BISMILLAHI RAHMANI RAHIM*_

_______"A guje inna tak'arisa cikin gidan haďi da rarumar Talatuwa da danbe.da sauri Talatuwa ta kauce,ruff kaji inna ta lik'u da k'asa.kafin ta mik'e tuni jama'ar dake gun suka kamota haďi da faďin subhanallhi.
"Itako Talatuwa ido kawai ta zuba tana kallo inna."cikin masifa inna ta mik'e tana faďin manafuka algunguma wlh baki isa ki auren min miji ba,mijina yafi k'arfinki wlh.
Sake rarumar Talatuwa tai da niyyar shak'ota." dukkkan matan dake gun ririk'e inna sukai haďi da cewa"haba RABI meye kikeyi haka,idan...ciki masifa da bala'i inna ta yayi6su da nayi ďin.kodan baku akayiwa haka ba yasa kowa ke faďin maganar banza...ďaya daga cikinsu ta buďe baki kenan da niyyar medawa inna martani."Talatuwa ta ďaga mata hannu da cewa"tai shiru kada tace komai."buďe bakin inna tace"ai dole kice haka."Talatuwa tace"suzo suje gida ta gode haka.."ihuuuu inna tai da yihuuuuu taji tsoro, tana gudun tonan asiri,idan ba tsoroba ki barsu mana idan yau ban tona baki asirin da fita kofar gida saiya gagareki ba.
"Murmushin kawai Talatuwa taiwa inna,domin batai mamakin abinda inna keyi ba,sabida dama tasan hakan zai faru"
"Suko matan tsayuwa sukai suna kallon inna haďi da kama ha6arsu🤔 sabida mamaki,cikin zuciyarsu kuwa ikon Allah kawai suke cewa"
"Gani yanda Talatuwa ta ďaure fuska ne yasa" inna kasa kai mata wani shak'ar sai dai bala'in kawai a baki".
"Bayan fitarsu ne Talatuwa tacewa" inna"
"Keeee saurara,inaso ki natsa ki sauriri abinda zai faďi maki.
"Ko kadan banyi mamaki dan kiyi haka ba,sabida ban ta6a daukarki cikakkan me hankali ba,ni kaina da nake mu'amula dake hakuri kawai nakeyi sabida gaba ďaya harkokinki sai a hankali.ban san abinda ke damuki ba RABI,jakancine ko da kikancine oho gakinan dai.Allah sarki gaskiya YALLABAI ya hakuri ba kaďan ba dahar ya iya zama dake har tsawon wannan lokacin.
Duba danayi da irin halin da yake ciki na damuwa yasa na nemi aurensa,badan komai ba sabida na yaye masa damuwa da k'uncin da yake ciki wanda nasan ba kowane ya sashi ciki ba sai ke...wani irin k'ulu-k'ulun takai da bakin ciki daya kama inna batasan lokacin datai wani irin kukan kura ta rarimo Talatuwa ba.
"Hannu Talatuwa tasa ta hankaďe inna sannan tai shigewarta ďaki.
Inna tajima tana tsine-tsinenta sannan ta kami hanyar gida haďi da cewa" zaizo ya samenni yau koni koke wlh.koda inna taje takoma gida bata iya shiga ďaki ba a tsakar gida ta zauna dirrrshan kai babu ďakwali sai faman zazzage kwandon masifa da bala'i takeyi ita kadai a gida kamar wacce kanta ya kwance".
"Kafin la'asar maganar auren daddy ya karaďa gari,da yake yau Khadijat taje gidansu,yana dawowa ta dawowa Rukky da labarin auren daddy ko ďakinta bata shiga ba, kai tsaye ďakin Rukky ta nufa,tun daga bakin kofar take kwata mata kira.
" Rukky dake ďaki da sauri tafito haďi da amsawa.a bakin kofa suka tsaya bakin taiwa Khadijat sannu da dawowa tuni Khadijat ta tareta da maganar auren daddy.
"Da mamaki Rukky tace" anya kuwa Khadijat? "
"Wlh Allah kenan,nima haka naji,amma gidan kina kokwanto ne mezai hana ki tambayi Baffa idan ya barki kije ki ganewa idonki maskiya.
Tou kawai Rukky tace".
Khadijat na tafita Rukky tace" idan ko da gskene daddy yai aure akwai buhun uba da inna. Waye zai ganemi inna da bala'i nasan yau sai abinda ta mance,amma dai bari naje na tambayi Baffa ko Allah zaisa ya barni naje.
Zubur ta mik'e zuwa ďakin Baffa,Baffa dake jingine da bango yaďan kishingiďa yajiyo sallamar Rukky. Amsawa yai haďi da cewa"RAKIYA ne?"
"Eh nice Baffa, gun tasamu ta zauna,sannu da shigowa yace da ita." yawwa tace"cikin dabara take jansa da hira,haďi da cewa "K'amaru yace" yanajin kewarsa".
"Allah sarki Baffa yace" sannan yaci gaba da cewa"yanda yakeji na rashinmu kusa dashi haka muma mukeji a zuciyarmu,amma da yake niman halas yaje,yasa damuwarmu ragaggene,fatanmu shi Allah ya bashi abinda yaje nima,ya ďorasa bisa kan mak'iyansa ya albarkaci zuciyarsa ya bashi masujin k'ansa.suma su saka masa da mafificin alkhairi yanda yake yi mana.
"Ameen kawai Rukky dake zaune take cewa" cikin zuciyarta kuwa har wani daďi da shauki takeji yanda Baffa keta kwararowa mijinta addu'a.
Saida ya k'are tsaf sannan tace" kana buk'atar wani abu?"a'a Baffa yace"sannan tasamu damar niman izinin tafiya gidan su daddy "
"Gani yamma yayi da farko kin yarda yai a cewarsa bayaso tana fitan yamma sabida babu kyau.
Jin haka yasa Rukky cewa" ba daďewa zanyi ba Baffa"
Tou yace"sannan yace yara fa?"
"Suna ďaki." eh nasan suna ďaki amma dai ba barinsu a tsakar gida zakiyi suyita watangaririya bako?"
"Muhammed ne kawai zan barsa dasu Khairat""" Aaahab Baffa yace sannan yaci gaba da cewa"badai gun HADIZA zaki barsu ba?".
"Eh ita Baffa"
"wacce HADIZAN kenan?badai tamu ba?"
"Eh fa Baffa"
"Aaahab wacenan sha-sha-shan yarinyar, k'azamiyar banza da wofi itace har zaki ďauki MUHAMMADU kikai mata,tou wlh ban yarda ba,idan har bazaki tafi dashi ba sai dai ki hakura da tafiyar.
"Jin haka yasa Rukky cewa" tou naji zan tafi dashi ďin.tana barin ďakin Baffa ďakinta ta koma,wanda ta sake yiwa Muhamme da muhsana bayan ta shirya sune sannan tai nata wanka ta shirya,saida taje ta sallami Baffa da Khadijat sannan ta kami hanya.

          ****

Da yake yau tuwon shinkafa ne Meenal zatayi yasa jin anfara kiran sallar la'asar ta m'ike daga zaunen da take,nan tabar Basik yana wasa da kayan wasansa.
taje kici domin jona ruwa,Cattle ta ďauka ta zuba ruwa sannan ta jona,a cewarta kafin ta idar da sallah ya tausa kawai sai dai ta juye a tukunya ta zuba shinkafa.
"Meenal na jonawa ta fice daga kucin ďin.
Harta shige sai kuma ta tuna da Basik data barsa a falo shi kaďan.kamar ta juya tazo ta ďaukesa sai wata zuciya tace" jeki dallah babu abinda zai samesa"
"Wata zuciyar kuma tace" a'a meenal koma ki ďauki ďanki"nan hankalinta ya kasu kashi biyu,tana raba biyu ďaya.
"Tajene ko kuwa?,nan dai tabuyewa ďayar zuciyar da yace da ita insha Allah babu abinda zai samesa.
Haka ta shige ta barsa yanara wasansa agun.tana shiga ďaki bayi taje tai alwala sannan tazo ta fara sallah.tunda meenal ta fara sallah zucuyarta keta rawaito mata abubuwa iri-iri na tsiya,hakan yasa hankalinta ya kasu kashi biyu.ďaya nan ďaya kuma yangun Basik.
Motsi kaďan sai fabanta ya faďi,hakan yasa taita sauri domin gani ta idar da sallah.
Har meenal takai goshinta k'asa domin sunjuda a yayin raka'a na uku kawai tajiyo ihu Basik.

"Surawa da gudu tai zuwa inda tajiyo ihun Basik ďin,kai tsaye kici ta nufa.tana shiga ganisa ta kwance tana faman juyi a ruwan zafi.itama ihuu tasa haďi da kai hannu tana k'ok'arin cetonsa.
" ihun meenal yasa J-boy fitowa a guje daga shi sai gajeran wando.Sofy kuma towel ne kawai take ďaure dashi a k'irjinta.yana gaba Sofy na biye dashi a bayan suka nufi kicin.
Suna shiga,gani halin da Basik ke ciki yasa J-boy kwarrrma ihu haďi da faďin nashiga uku,Basik,J-boy ya faďi hakane haďi da  kai hannu zai ceto ďansa.da sauri Sofy ta rik'esa haďi da faďin a'a J-boy. Baka gani shokine?.
"Fisge jikinsa yai yasake kai hannu.duk abinda sukeyi meenal bata sauraresu ba.janyosa waje Sofy tai haďi da jawo kofar tasa key ta rufe kofar haďi da cewa" bari naje na cire fisďin.a guje ta fice waje.
"Gaba ďaya daraba ya 6acewa meenal, har a lokacin bata samu mafitar da zata ceto ďanta ba.kuka kawai takeyi haďi da faďin Allah sarki Basik. Basik dake kwance yace kuka,a hankali muryansa ya fara raguwa,numfashinsa na niman ďaukewa.
"J-boy dake waja sai faman kai komo yakeyi a falo haďi da lek'a kicin ďin.
"Gani numfashinsa ya ďauke yasa meenal kwarrrma ihu haďi da kiran sunan J-boy tana faďin shikenan Basik ya mutu.
"Kukan kura tai tasake komawa gun Basik ďin.wani shokin ďin ne yasake ďauketa ya lik'ata da bango,ihu takwarma haďi da kwaďawa J-boy kira yazo ya ceceta.juyi kawai takeyi domin gaba ďaya ji tai kamar an zare mata lakkan jikinta haka yasa bata samu k'arfin guiwa wani yunk'uri ba.koda Sofy ta fita zagawa tai ta windom duk abinda J-boy keyi Sofy na kallonsa tana dariya haďi da cewa kaďan kenan daga cikin aikina.ta jima tana kallonsa tana dariya.shiru-shiru da J-boy yaji ne yasa shi zufita yana k'ok'arin buďe kofar.
"Gani kofar yaki buďuwa yasa J-boy sanya k'afarsa yana tikarin kofar.   jin kanta tai ta timo da k'asa batare datan yanda hakan ya faru ba.sake mik'ewa tai ta koma ga Basik.a lokacin ne tagano ashe butar data jona ruwan ne ruwan dake ciki cattle ďin ya zube amna har a lokacin cattle ďin yana jone da wuta.ashe ba kukan ruwan zafi kawai Basik ke kukansa ba harda shokin.
Nan meenal tafara tunani yanda zata raba cattle ďin da wuta.ta jima tana juye" juye sai daga bayan sannan wani dabara ya faďi mata rarrafawa tai taje ta buďe loka ta ďauko k'arami addan dake zuwa cikin setin kayan ciki kukan kura tai ta harba adda,take igiyar ya yanke gani haka yasa meenal zuwa ta ďauki ďanya sannan ta m'ike zuwa kofa.
"Shirun da J-boy yaji ne yasa shi tikarin kofar da k'arfi take kofar ya buďe,gani Basik a hannu meenal yasa J-boy kar6ansa haďi da jujugasa yana kiran sunansa.gani yaba motsi yasa J-boy rusawa da kuka yana faďin wayyo Allana na shiga uku.a guje ya nufi waje,meenal na biye dashi a baya.itama kukan takeyi.
" hangosu da Sofy cewa"shegu kawai,ai wlh bama haka nasoba.
Tabaro inda take tsaye tana kallonsu ta zagayo,tana zuwa kai tsaye gun J-boy tanufa.gani halin da Basik ke ciki ihu tasa haďi da yanke jiki ta faďi sumanma.nan hankali J-boy ya sake tashi.take ya mik'awa meenal Basik yai kan Sofy dake kwance shaff.
"Ko kallonsu meenal batan ta shigewarta mota tai tana rungume da ďanta tana kuka.
K'inkimar Sofy J-boy yai zuwa mota,a baya ya shinfiďata sannan ya rufe motar.a guje ya zagayo yazo ya shiga mota ya tayar fisgar motar yai a tsiyace ya fice daga gidan.
"J-boy na tada mota Sofy ta buďe idonta tana masa dariya mara sauti.ta glass take kallonsa idan taga zasu haďa ido da sauri take rufewa ta koma ta kwanta.shiko J-boy
Bini-bini saiya lek'a ya duba halin da cike ciki sannan ya koma kan Basik dake rungume a hannu meenal.
Da haka har suka isa asibitin,kai tsaye emergency aka nufa dasu dukkansu,k'afar J-boy babu ko takalmi.a guje yakebin nurse ďin da suke tura kekan da Sofy ke kwance akai....!!!!!!!!


Dan Allah kuyi hakuri da jina shiru da kukayi kwana biyu,wlh abubuwane sukai min yawa,sannan kuma jiya nayi typing me yawa domin share laifina amma kusan ance komai rabone wlh duk ya zube.dan Allah kuyi hakuri dani.nagode sosai sannan inayiwa kowa fatan alkhairi.Allah ya bar zumunci me ďorewa ameen.




Commen
             N
          Share


📚✍

MAKAUNIYAR RAYUWAWhere stories live. Discover now