MAKAUNIYAR RAYUWA

216 14 12
                                    

*MAKAUNIYAR RAYUWA*
________________________________

*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________

~DIDECATED TO~
*ANTY FAUZIYA*
   *ƳAR AMANA*

https://www.facebook.com/104534761033461/posts/119016616251942/?app=fbl

         *PART THREE*
              *PAGE 15*

*BISMILLAHR RAHMANIR RAHIM*

_____"Bayan kwana biyu da zuwan Yaya Bala wajan daddy,daddy yaje ya sami Inna da zancen,duk yanda sukai da Yaya Bala saida daddy ya faɗi mata"
   "Babu abinda ya fito daga bakin Inna sai ina ruwa da maganar kwashe wasu kaya?kuje can kuyi duk yanda zakuyi ni babu ruwana,kai ba maganar kwashe kaya ba hatta ita kanta me kayan tuni nariga dana sallamata,dan haka daga yau sai yau in har magana akan RAKIYA ne wlh kada ka ƙara tunkarata dashi,idan kuma ba haka ba...Allah yasa ki gane daddy yace snn yai fice warsa"
Bayan kwana biyu daddy ya sami motar akori kira yai magana dasu,bayan su dai-daita yaje ya sanarwa Talatuwa akan gobe zasu tafi kwasowa Rukky kayan"Allah ya kaimu tace dashi"
  Washe gari babu yanda Talatuwa batai da Rukky ba,akan tazo su tafi"Hakuri Rukky tabawa Talatuwa haɗi da cewa"bazata iya ba taje kawai"
     Dole yasa ita kadai taje"kafin ta tafi saida daddy ya ki Yaya Bala ya sanar dashi cewa"ga suna zuwa kashe kaya"Dole ya fasa zuwa kasuwar da zaiyi,da taimakon Yaya Bala Talatuwa ke lwashe kayan,lokacin ƙamaru baya gid,ita kuma iya nacan ciki batada labarin abinda ake ciki"
  Tunda sula fara tattara kaya Khadijat ke faman kai komo, bini-bini saita leƙa ɗakin,gani har su kusa gamawa yasa Khadijat tafiya sanarwa iya" da sallama ta shiga ɓangaren iya"Iya dake zaune a tsakar gida tana ɗan aikace-aikace irin tamu ta mata,jin sallamar Khadijat yasa iya dakatar da abinda takeyi haɗi da cewa"HADIZA ce?"
   Eh wlh nine iya,aiki kokeyi ne?"
"Uhmm wlh ɗan kayan nan take gyarawa,kin san lokacin isa babu wiya kaya sun bushe""wlh kuwa tou kawo na tayaki"...
  Hannu Khadijat tasa""da sauri iya ta kauda haɗi da cewa"a'a barshi kawai,abinda na ƙarema" Dan Allah ki bari na ƙarisa iya"Iya ta kuma cewa a'a"Da yake bekai zuci ba taba kuma cewa ta kawo ba,waja tasamu ta zauna,a hankali takejan iya da hira,saida tabari suyi nisa da hira take cewa"Allah sarki,dama haka rayuwa take,yanzu muda Rukky shi kenan""Iya tace wlh kuwa'ni har Allah-Allah nakeyi suzo su kwashe kaya...Jin an sosa mata inda yake mata ƙaiƙayi da sauri ya tana rawan baki tace'wasu kayan kuma?"
kayan baƙar shegiyar mana"Aiko dai suna can suna kwashe kaya,kice bakida labari?tou komai na ɗayan Saida suka kwashe,kuma idan baki mataba ba kayan Rukky bane kadai a ɗakin,harda na ƙamaru domin akan idona lokacin daya dawo daga training ba ƙarami siyayya yai ya zuba a ɗakin ba"Jin haka yasa iya sakin aikin da takeyi ta miƙe zuwa ɗakin Rukky"Itama Khadijat miƙewa tai suna tafe tana yiwa iya dariya haɗi da cewa"ƴar jaraba,ba kince bakida hankali ba,ai sai kiyi"
  Iya na shiga ɗakin dai-dai Yaya Bala na kwanto tv dake liƙe a bango"kaeeee tace dashi haɗi da cewa"ina zakakai masa?".
Inna yini Talatuwa tawa iya"ko kallo bata ishi iya ba bare ta amsa mata gaisuwa"Yaya Bala yace"wai ina kwamce mata ne,kin san har kan glass sai a hankali"""shi ɗan uwan nakane yace dakai idan suzo kwashe kayan su haɗa dashi?"ko ka mance lokacin da tazo aure gidan batazo dashi ba"..Haba iya Dan Allah...Dan Allah ubanka,waima na tambayeka kodai baƙin ciki kakeyi da ɗan uwan naka?,domin na lura duk wata hanya daza'a cucesa kaine gaba,to bari kaji wanda ya zama na ƙark idan har kabari na kuma kamaka da laifin irin haka wlh saina zana maka layi tsakaninka da ɗan uwanka"
Zan cen tv kuwa babu uban daya isa ya fita dashi daga gidan nan,idan mutum ya musa ya gwada"
Talatuwa dake tsaye kama haɓa tai tana kallon iya"
Iya na gama magana juyawa tai haɗi da cewa"idan da kuɗin uban mutum ya haɗa ya siye saiya ɗauka,shegu a sararru kawai"
   Jin muryan iya na fitowa yasa Khadijat kaucewa daga bakin ƙofar da take tsaye,a guje ta koma gefe ta raɓe tana jiran wucewar iya snn ta koma"
Iya na wucewa dariya Khadijat tai haɗi da cewa"duk kiyi ki gama kafin na ɗora daga inda na tsaya,shegeya jara babbiyar ysohuwa kawai,ai dama tara maki nakeyi da kuma ido Rukky amma tunda yanzu tabar gidan wlh saikin kwashe kashinki a hannu".
  Kai tsaye wajan mota tanufa,tana isa gidin mota salati tasa tana faɗin innallilahi wa'inna'ilaihin raju'un Allah ya tuni asirinki yau,ashe dama duk kayan da ake satami kece?"
  Hannu tasa ta fara sauko bokitai"da sauri me motar ya ƙariso wajan ta haɗi da tambayarta iya lafiya?"
Ba tare data tanka masa ba taci gaba da sauke kaya"
Gani haka yasa mutumi kwashewa yana medawa cikin motar,haka suka dunga yi tana saukewa shi kuma yana medawa,gani haka yasa iya ta hau zaginsa,zaginsa takeyi haɗi da lakatan masa hanci tana faɗin ka fita daga ido na na rufe idan haka baki akai dakai kuzo ku kwashi kayan sata tou wlh baku isa ba,domin daga kai har wanda karako duk baku isheni yi ba shege tsinanne guntun matsiyaci"
  "Duk irin zagin da zaki min bazan rama ba domin nasan darajan kaina da kuma iyayena,kayane dai bazan bari ki ɗauka ba,tsohuwar banza tsohuwar wufi kawai"""Cikin fusata iya ta shaƙe mutumi haɗi da cewa"nice tsohuwar banza?""""
   Eh ance ɗin, tsohuwar banza tsohuwar wufi".
Cukuikuyesa tai haɗi da zabga masa mamya-manyan ashariya"da yake bakin titine nanda nan jama'a suka cika wajan sai faman bawa iya hakuri akeyi data saki mutumi"
Itako tace"bazata sakeba har sai ya faɗi mata waye tsohuwar banza?"
Gani yanda jama'a suka fara bashi rashin gaskiya yasa shi rantsuwa da wlh Allah be zageta ba,ta yaya za'ayi ya zageta bayan shima yanada irinta a gida"
   Ɗaya daga cikin ƴan unguwa sukace"a rabu dashi domin idan iyace kaɗan ne daga cikin aikinta,domin sun sha jin labarinta tun suna raya masifaffiya ce".
  Yana maganar ne yana kallo iya cikin Ido ko ƙibtawa bayayi"
   A guje iya ta saki mutumi takoma kan ɗaya,zagi inda take shiga banan take fita ba rankataf iyayensa saida tazana sunayensu ta zage"Da yake tatirin yarone nunata da yatsa yakeyi haɗi da cewa" idan kika kuma zaganmi iyaye wlh babu uban da zai hana ban zabga maki mari ba".
  Duk yanda akai da mutumi da yai shiru ya kyale iya amma yaki haka suka dunga zage-zage ita dashi".
Jin shirun iya yai yawane yasa Yaya Bala cewa"dan Allah ina zuwa,bari naje na dubo abu nazo".
   "Tou Talatuwa tace"dashi"
"Yana fita yagansu cikin wanan halin da sauri ya ƙarisa wajan haɗi da faɗin haba!haba!!iya yanzu dan Allah meye haka"
  Hannu yasa yana ƙoƙarin cire mata hannu daga wiyar yaro"da taimakon jama'an da suke wajan suka ɓanɓare wa iya hannu daga wiyar yaron"
Buɗe bakinsa yace"Allah ya taimakeki wlh da kinga yanda ake tijara"
Yaya Bala yaci gaba da cewa"idan banda abinki inake ina wanan yaron,yaron da duk unguwa shakkan yi masa magana akeyi sabida tijara da rashin sani mutunci ɗan Adam?".
   Kakkaɓe rigara yai haɗi da busa masu kura yai wucewarsa"
Komawa tai wajan motar taci gaba da sauko da kayan,duk yanda Yaya Bala yaso hanata amma taki ji"tana cikin sauke kayan kenan Talatuwa ta fito,gaba irin abinda iya keyi yasa Talatuwa komawa gefe kiran Rukky tai ta sanar da ita abinda ake ciki"
Rukky tace"ta rabu da ita,idan ma duk kayan zata riƙe tace tata ta kyaleta kawai"
  Hannu Yaya Bala yasa akai yana me takaicin yau ace wai mahaifiyarsa ce ke aikata haka"
Jama'an dake wajan kuwa kowa da mummanar kalmar da yake furtawa akan iya ba tare da suyi duba da ɗanta na wajan ba"
   Haka iya ta tunga kwasan kaya kama daga kan bokitai rover da plate cokula kofuna duk saida iya ta naɗe, tanayi tana tsinewa Rukky tana kiranta da suna bananarsa,duk kayanta ne taita kwashewa sai yau Allah ya tona mata asiri"
   Shiruuu Talatuwa tai tana kallo ikon Allah ba tare data tanka mata ba har saida ta ƙare snn tace"kin gama?"
Banza da ita iya tai taci gaba da kwashe kayan tana medawa cikin gida"
  Bayan iya ta gama ne Talatuwa tacewa drive zo muje malam"tou yace snn ya shiga mota suka bar unguwan,suna tafe yana bawa Talatuwa labarin yanda sukai da iya"
Murmushin Talatuwa tai haɗi da cewa"idan HANNE ce kaɗan ma kagani"Itama labarin irin abinda tasani akan iyan tai ta bashi"chab yace"snn yaci gaba da cewa"Allah ka rabamu da masifaffen mutum"Ameen Talatuwa tace".
   Bayan su isa gida,Yaya Mu'azam da driver suka haɗu suka kamo kayan zuwa cikin gida"da yamma daddy ya kira Rukky,da sallama ta shigo ɗakin bayan ta gaishesa ne tace"gani daddy".
     Dama akan maganar kayane..tun kafin ya fara magana ta tari numfashinsa da cewa"duk abinda kaga ya dace kayi dashi kawai,da sauri ta miƙe zuwa ɗakinta tana shiga kuka tasa"
   Nan suka yanke shawara shida Talatuwa,tace zata nemi masu siyan kayan hannu, idan suka dai-daita sai a saida masu bayan an siyar sai a sanyar sai a baka kuɗin ka ije mata idan kuma zaka juyane har zuwa lokacin da tatashi wani aure saika bata kayanta"".!!
Taran numfashinta yai da a'a Talatuwa,sisi bazan taɓa ba domin kuɗi shegen abune yanzu-yanzu sai kaga kanemesu ka rasa,dan haka acco kawai aza zuba mata kayanta har zuwa lokacin da ta tashi aure".
  Hakane kuma malam kayi tunani,ubangiji Allah yai mata zaɓin alkhairi"
   Ameen yace".
Tun safe da ƙamaru ya fita be dawo gidan ba sai bayan goman dare,yana shiga ɗaki yaga wayam,ɗaki ya koma kamar filin kallo"
  Whattt!!!? Yace,a guje ya nufi ɗayan Yaya Bala yana tafe yana kwanɗama masa kira"Jin irin kiran da ƙamaru keyi masa ne yasa Yaya Bala fita da sauri haɗi da faɗin lafiya?".
  Yanzu na dawo gidan ina shiga ɗaki naga babu kaya".
  Eh iyayen Rukky ne sukazo suka kwashe"
   What!!? Ya kuma cewa haɗi da rusawa da kuka yana faɗi why!?why!!?why!!!? Yaya, meyesa kanari suka kwwshe kayan eyye yaya?,shikenan na shiga uku na lallace,meyesa Yaya eyye yaya meyasa Yaya"
  Matsananci kuka ya kuma fashewa dashi haɗi da tambayar yayansan why"
   Gani irin kukan da ƙanisa keyi yasa Yaya Bala rungume ƙamaru yana rarrashinsa,shima kwallan yakeyi.
  Su jima a haka snn ƙamaru ya zare jikinsa daga na Yaya Bala,ɗaki ta koma Yana shiga janyo jakar kayansa yai ya shiga tattara kayansa yana zuwaba a cikin jakar,yana gamawa ya ɗauki jakarsa"Yaya Bala dake zaune yaji muryan ƙamaru na sallama",
  Shigo mana yace dashi"
Basai na shigo ba"Jin haka yasa shi miƙewa yana fita gani ƙamaru yai rataye da jaka a kafaɗa"Zan tafi yace"
Ina zaka tafi?".
Jin kalmar zan tafi furum Khadijat ta fito daga ɗaki"
Shiruuu yai kafin ya buɗe baki yai magana wasu kwallane suka sake zuwa masa,da sauri ya juya yaci gaba da tafiya"
Hannu Yaya Bala yasa ya rikesa haɗi da cewa"Wai meke damuka ne ƙamaru?"".Fisge jikinsa yai yaci gaba da tafiya,duk yanda Yaya Bala yaso hana ƙamaru tafiya amma abin ya faskara,domin kuwa har abin ya koma masu kamar danbe"
Gani haka yasa Yaya cewa"Khadijat tai maza taje ta kira masa iya"
  A guje Khadijat ta ruga zuwa kiran iyan har tana tutuɓe, tare suka fito gani halin da suke ciki yasa iya rusawa da kuka kama jamar ƙamaru tai tana roƙonsa da kada ya tafi ya barta, duk irin kuka da magiyar da iya ke masa amma besa ƙamaru ya saurareta ya tsaya ba,yana fisge jakarsa a guje ya fice daga gidan.
  Ihuuu iya tasa haɗi da faɗin na shiga uku na lallace"
  Yaya Bala da Khadijat suka kamata zuwa ɗaki, daren ranar yanda iya taga rana haka taga dare,domin irin kukan da tai ko lokacin mutuwar Baffa batayishi ba"
Ƙamaru na zuwa tashar zuɓa yasami mota zuwa Ondo state"
Bayan kwana biyu Talatuwa ta kira dallaliya tazo har gida,bayan su kuma gaisawa ta nuna mata kayan,ɗaya bayan ɗaya,bayan ta gama dubawa ne suka fara ciniki,da farko kaman bazasu dai-daita ba cikin hukunci Allah kuma suka dai-daita,gama ɗaya kayan tasiye amma banda katifa da kuma akwatuna,domin a cewar Talatuwa be kamata ta saida katifa ba tunda a tabarma take kwana,data siyar da katifar gwamma tabar kayanta ta rinƙa amfani dashi"
Bata kwashe kayan ba saida ta cakewa Talatuwa kuɗinta rass snn ta kwashi kayan".
   Miƙewa Rukky kuɗin tai tace"ga kuɗin nan tabayar"
A'a ki ije kawai,kona amsa babu abinda zaiyi dashi"
Kaiwa ɗaki tai ta ije har saida daddy yadawo snn ta bashi kuɗin"
Yana amsa fita dasu yai daga gida,tafiya yai cikin gida wajan har ɗaki yasami Mu'azam ya bashi snn yai masa bayani akan kuɗi"babu damuwa yace,washe gari yakai banking ya ije cikin Account ɗinsa"
    Tun daga lokacin Mu'azam ke iya ƙoƙarinsa duk wani abinda yasan zata buƙata ita da yara yana siye masu iya karfinsa,tun daga kan sabulun wanka da wanki klin man shafara nata dana yara duk Mu'azam ke siye mata"
A ɓangaren Yaya Bala shima yana ƙoƙarin sosai akansu hakan yasa Rukky batasan walahar da mata ke shiga yayin da zasu zaman Iddah ko takaba ba"
Yara kuna suna zuwa school din da babansu ya sanyasu(wato yaya Bala)Gani suna tafiya hannu empty babu lunch Yaya Mu'azam ya siya masu lunch boxes da cartoon ɗin bobo da kuma indomie, kullin sake Rukky ke dafa masu su tafi dashi school ɗin"
  Akace yaro wawa gani su Muhasana da Muhammad suna tafiya da lunch box yasa su Khairat da Na'eem sanwa Khadijat kuka a dole sai tasiye masu irin kular su Muhammed snn kuma ta rinƙa dafa masu abinda suna tafiya dashi school".
   Gani su sata a gaba da magana ɗaya,kullum maganar kenan sai dai a siya masu lunch boxes yasa Khadijat cewa"idan Abbansu ya dawo su faɗi masa".
Suna faɗi masa yai masu alkawarin gobe idan yaje kasuwa zai siya masu tare da indomie da bobo ɗin"
   Uhu sukasa suna tsalle Abba yace"zai siya masu irin kular su Muhammed"
  Tun daga ranar daya siyo suka fara samu matsala da Khadijat sabida makara"
  Dama can yaya lafiyar kura bare kuma ta haukace"dama tun can basu fita akan lokaci,kullum sai bayan takwas suke fita bare kuma yanzu"
   School har su gaji da koransu sukai su haƙura suka kyalesu"
  Yan class kuwa har suna suka sanya masu da latecomer".
Gani abin yana nima ya shafi karatun yaransa yasa Yaya Bala daina jiranta,da zaran ya tashi sallar asuba kafin ya fita masallaci yake ɗora ruwan wanka kafin ya dawo daga masallaci yai zafi juyewa yakeyi yaiwa yaransa wanka ya shiryasu idan su fita kafin su ƙarisa school ɗin takeaway yake siye masu ya juye a lunch boxes ɗin snn ya ƙarisa dasu school"
Yau da gobe sai Allah,gani shike shirya yara zuwa school ya kaisu snn ya dawo yai nasa shirin zuwa kasuwa,yanda yafita yabar gida haka zai dawo ya samesa kace-kace babu shara bare wanke-wanke lunch boxes uniform kowane zaune yake da gindinsa yanda inda su Khairat suka ije nan baban ke dawowa ya samesu"
  Kamar kullum yana dawowa daga kasuwa jefa ƙafar da zaiyi falo sai cikin kwanu abinci,santsine ya kwasheshi da badan ya riƙe kushi ba babu abinda zai hanasa faɗuwa, innallilahi yace"Khairat da Na'eem dake zaune a falo da sauri suka jiyo suna faɗin sorry Abba duk abinda akeyi Khadijat na ciki tana jinsu amma bata fito taga abinda ke faruwa ba"
   Bayam ya miƙe ne yace"dashi ina mamanku take?"
  Tana ciki"
Tsaki yai snn ya ƙarisa daga ciki,koda ya shiga ganita yai kwance akan gado"
Faɗita da faɗi yai yana cewa"haba Khadijat wanan wani irin rayuwace haka?,yanzu abin naki har yakai ga haka?,ace kwanu da aka gama cin abincin ma bazaki iya kaudawa ba,inda badan Allah ya tsare ba nayi imani kaɗan ne zai rage ban faɗi ba"
  Duk magana da Yaya Bala keyi ko motsi Khadijat batai ba bare da nuna tasan da ita yakeyi"Baci ciki da takaici da suka kamasa besan lokacin daya ficcikota yai hurgi da ita ba"
Ihu Khadijat tasa tana kiran wayyo kanta,miƙewa da zatayi takai masa shako haɗi da cewa"wlh saika kasheni snn zan sakeka"Jin haka yasa shi niman kwacewa daga hannu domin ya fice yabar mata ɗakin"da yake tariga tasan bame son tashin hankali neba yasa taki sakinsa,duk inda yabi tana biye dashi haɗi da ɗura masa zagi"
  Shege matsiyaci talakan banza talakan wofi kawai idan banda soyayya mezan dakai?,wlh yau ko ka kasheni ko kuma ka sakeni idan ba haka ba nabar sakinka".
  Jin hataniya yai yawa yasa Khairat zuwa ta leƙa,gani irin abinda iyayenta sukeyi yasa Khairat rusawa da kuka a guje taje kiran iya"
  Gani yaki sakinta yasa Khadijat ce masa ɗan shege da shegiya ɗan matsiyata wanda basu gaji arziki ba,babu mamaki talaucinku na gadone a cikin jininku yake...Kafin ta ƙarisa saukar duka taji inda yake shiga banan yake fita ba,duk inda yasamu dukanta kawai yakeyi haɗi da tokari"Suna cikin haka kenan saiga iya su shigo a guje gani abinda ke faruwa yasa iya shiga tsakiyar haɗi da cewa sai dai ni kadakeni amma wlh inaji ina gani bazan bari ka dakar masu ƴar mutane ba"""Yunkurawan da Khadijat zatayi ta hankaɗe Iya dake tsakiyarsu haɗi da cewa"dallah ja kiban waje,tsohuwar banza tsohuwar wufi kawai,baƙar alguguma... Faɗiwa akan gadonsu iya tai haɗi  da cewa"Na shiga uku"
     Wani irin wawan tokari Yaya Bala ya kaiwa Khadijat wanta kaɗan yarage da taci da baki snn yaci gaba da dukanta haɗi da cewa"uwata tafi ƙarfin wulaƙanci wlh baki isa ki wula kantami uwa na tsaya ina kallonki ba"
Duk yana maganar ne haɗi da duka"duk irin dukan da yakeyi mata besa bakinta ya mutu ba"
Idan yace"uwata tafi ƙarfin wulaƙanci a wajanki""Tace"uwarka ɗin banza uwarka ɗin wufi"Gani yanda sukata zage-zage yasa iya cewa"yazo ya fita yabar mata gidan"Jin iya tace ya fita yasa Khadijat shaƙesa haɗi da cewa"idan har kaga na saketa wlh sakina kai"Duk irin hakurin da iya taita bata amma besa Khadijat ta hakura ba, har da yara tai mata nuni da tai hakuri ta zauna ta tallafi 'ya'yanta amma Khadijat tai kunni uwar shegu"
   Buɗe bakin Yaya Bala yace"jeki na sakeki saki ɗaya""""innallilahi wa'innailailin raju'un iya tace"Shima kanta dayai sakin sai da yaji babu daɗi"
   Iyyirirrin Khadijat tace"haɗi da shewa tana faɗi alhamdullhi yau burina ya shika Allah ya rabani da ala ƙaƙai,insha Allahu na barka kenan domin bazan iya rayuwar talauci ba"
   Har iya ta buɗe baki zatai magana karaf Khadijat ta hantareta da cewa"dallah ja ki rufemi baki banza kawai"mayafin dake sagale a ƙofa ta ɗauka,daga shi bata ƙara komai ba haka tafice daga gida"Duk irin kukan dasu Khairat da Na'eem keyi besa Khadijat ta juya ba"Cikin kuka suke faɗin Dan Allah mama ki dawo Dan Allah kada ki tafi ki barmu mama"
har ta kusa bakin gate a guje suka ruga sunabin Khadijat suna gudu suna kiran kiranta da tadawo"
  Bakin gado Yaya Bala zauna,kwashe hannayesa yai ya zuwa kai,gaba ɗaya jin yai babu abinda ke masa daɗi a duniya,mema yasa ya biye mata da har hakan ya faru".
   A guje iya tabisu tana gudu tana kuka haɗi da cewa"ku dawo insha Allahu zata dawo kunji"""Wahhhh!!! Allah yai min tsari,na dawofa kikace? ai na tafi kenan,kuma tsohuwar banza tsohuwar wufi ga 'ya'yanan mu tafi mu barki dasu ki dafa kisha matsiyaci talakar banza talakar wufi kawai"
  Cikin kuka iya ke cewa"nice tsohuwar banza HADIZA?"
  tsaki Khadijat tai haɗi da ficewa daga gida""""!!!!...

MAKAUNIYAR RAYUWAWhere stories live. Discover now