MAKAUNIYAR RAYUWA

131 12 8
                                    

*MAKAUNIYAR RAYUWA*
________________________________

*AREWA WRITES ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________

~DIDECATED TO~
*ANTY FAUZIYA*
   *ƳAR AMANA*

https://www.facebook.com/104534761033461/posts/119016616251942/?app=fbl

         *PART THREE*
              *PAGE 10*

*BISMILLAHR RAHMANI RAHIM*

_____"Koda su Yaya Bala suka fita da Rukky sun jima tsaye agun basu samu mota ko Napep ba,har saida gari ya fara wayewa snn suka sami napep.
Har su shiga,gani su Muhammed da Muhasana tsaye suna faman kuka yasa Yaya Bala cewa"cewa muje..Cikin rawan baki Khadijat tace"harda asibitin ma sai anje dasu?,juyawa tai haɗi da daka masu tsawa da maza ku koma cikin gida... A'a Khadijat rabu dasu.sann ya juya garesu yace"kai kuzo muje".
Bayan Yaya Bala yaci gaba da cewa"gwama mutafi dasu,sabida idan ba tafiya mukai dasu ba,sunayi suna kallon mamasu hankalisu bazai kwanta ba.
"Uhmm kawai Khadijat tace, shiruuu tai bata sake magana ba har suka isa asibiti.
    Duk maganar da Yaya Bala keyi ta tafasa Khadijat bata cewa"gani bata tamka masa ba yasa Yaya Bala sake jefa mata tambaya dalilin da yasa ƙamaru ya kama Rukky da duka daga dawowarsa..cikin tsiwa tace"kajika da wani irin magana nida kwance a ɗaya ta yaya zanyi nasan abinda ya haɗasu..Abinne da mamaki Khadijat daga dawowarsa kawai sai yahau ƴar mutane da duke, jifa sabida Allah yanzu abin Allah ya kiyaye in wani abu ya faru ba,kina gani za'a kyalesa ne?" Tou nidai banida masaniya amma koma menene ruwa baya tsami banza..Hakane amma wanan abu akwai alamar tambaya a cikinta...kamar Yaya?""ban yarda haka kawai ƙamaru zai aikata haka ba tare da wani ya shiga tsakaninsu ba..Ban gane ba?"Duk yanda akai wanan abu ba banza ba,akwai sa hannu a ciki.."Toufa zargi kakomayi ko yaya?"Ni ba zargi nakeyi ba amma wlh nasan wanan irin aiki ba banza ba, Allah dai ya kiyayi ɓacin rana.
     Khadijat dake zaune ji tai gabanta yai wani irin bugawa dimmm,shiru tai bata sake magana ba har suka isa asibiti.
  Suna isa taimakon gaggawa Yaya Bala yanema,batare da an ɗauki lokaci mai tsayi ba likita ya dubata"
    Shiko ƙamaru tun bayan fitan su Yaya Bala waje ya samu ya zauna,kai ya haɗa da guiwa kuka yakeyi idanu bibiyu kamar wanda aka aikowa mutuwar uwarsa.
   Likita be taɓeta ba saida ya buƙaci a biyasa ƙuɗinsa,babu yanda Yaya Bala beyi dashi ba,bata mata kulawa zai biyasa,amma likitan yaji,domin yasa Yaya Bala yi masa transfer din kuɗin snn likita ya fara aikinsa.
     "Ya jima zaune yana kuka, zuburrr ya miƙe tsaye,kofin silver dake kusa dashi ya ɗauka yai hurgi dashi snn yaci gaba duk abinda ya rarumo kwan dashi yakeyi da ƙasa ko kuma ya buga dashi da bango hatta tv dake ɗakin be barsu ba duk saida ƙamaru ya ragargaza su"
     Yan shaw glass din Rukky wanda yake ɗauke da kayan turarukanta duk saida ƙamaru ya farfasa su.
     Jin ƙara yai yawa yasa iya fitowa haɗi da tambayar lafiya?,tun daga bakin ƙofa take hango kaya a warwatse har zuwa cikin ɗakin"
     "Da salati iya ta ƙarisa ɗaki,tana shiga taga ƙamaru cikin wanan hali,sake wani salatin tai haɗi da tambayarsa yaushe yazo?"
   Gani ya ƙinƙimi tv zai rotsashi da ƙasa yasa iya ƙarisa a guje ta riƙesa haɗi da tambayar kansa ɗaya kuwa.
  Bayan su sauke tv ƙamaru ya sake rusawa da  matsananci kuka haɗi da rungumar iya yana faɗi Rukky! Rukky!! Rukky!!! ta cuceni iya,iya na shiga uku na lalace wayyo Allana, wayyoooo Allahana iya...jin kalmar Rukky da ƙamaru yaita hurtawa yasa jikin iya yahau rawa,a razane take tambaya meya sami Rukky?,waima ina takene,eyye ƙamaru ina Rukky take?badai mutuwa tai ba,take itama ta fashe da kuka wanda ita kanta batasan lokacin ba kukan yazo mata ba.
    Shima kuka kawai yakeyi bebawa iya amsa ba,gani haka yasa iya zare ƙamaru daga jikinta da sauri ta nufi cikin ɗaki haɗi da kwadawa Rukky kira.koda ta shiga bata ganta ba sake fitowa tai taci gaba da tambayar ƙamaru inda Rukky take..duk irin tambayar da iya kewa ƙamaru be bata amsa ba..
  Bayan likita yai dube-duben da zaiyi ya gama jona mata drip yai hade da allurai snn yace dasu Yaya Bala da suke tsaye a kanta yace"ba wani matsala a zabar dukane amma idan tasamu wadattace bacci insha Allah komai zaiyi dai-dai.
   Yana gamawa yai ficewarsa daga ɗakin.
     Bini-bini sai nurse's su shigo su dubata,gani har gari ya fara wayewa bata falka ba yasa Yaya Bala cewa"bari yaje gida ya duba yara snn ya dawo.
   A dawo lafiya Khadijat tace dashi.
     Yana fita kujeran rover dake gefe ta jawo ta zauna kusa da Rukky,duk juyin da Rukky zatai idanu Khadijat na kanta.
    Can kuma maganar Yaya Bala ya faɗo mata arai,nan tashiga kokwanto haɗi da tambayar kanta kalmar da Yaya Bala ya faɗi na Allah ya kiyayi ɓacin rana,tou idan asiri ya tuno me zaiyi??koma menene ya daɗe beyi ba,can kuma tace bare ma nasan babu yanda za'ayi asirina ya tuno dalili kuwa shine koda na tura saƙon saida nabi na goge,ban barsa akan waya ba,snn kuma ai bada wayarta na tura saƙon ba bare aga numbar ba,dan haka banga abin tada hankali ba.
   Dan haka asirin ya daɗe be tuno ba.
       Yaya Bala na isa bakin gate din asibiti ya sami napep yahau zuwa gida,zaune kawai yake amma gaba ɗaya jikinsa babu gwari,suna isa ina zuwa yace dame napep ɗin, da sauri ya ƙarisa daga ciki,yana shiga sautin kukan iya yaji a ɗakin ƙamaru,da sauri ya nufi ɗakin yana shiga ya tarar da halin da ake ciki.
   Subhanallilahi yace"haɗi da ƙarisawa kusa da ƙamaru hannu yasa ya riƙesa da ƙarfi snn yaci gaba da yi masa faɗa haɗi da cewa"kodai ya fara shaye-shayene,yanzu abinda yai ya kyauta kenan?yanzu inda wani abu yasami Rukky yana gani ɗangin zasu zuba idone suna kallonsa...Cikin zafin rai ƙamaru yace"ina runa da wata Rukky, Rukky banza Rukky wofi, Allah ya isa tsakanina da ita,kuma daga yau bani babu ita na saketa saki ukuuuu...kafin ya ƙarisa ji kawai kakeyi fassfassfass wani irin wawayen maruka yaya Bala yai masa haɗi da shaƙesa,yana faɗi da alama shaye-shayen da kakeyi ne ya taɓa maka kwakwalwa..
    Iya dake tsaya innallilahi wa'innailailin raju'un kawai take ambata,jikinta har karma yakeyi.
    Hannu ƙamaru yasa ya bigewa Yaya Bala nasa hannu haɗi da cewa"nace bana auren ko dole ne?nace na saketa bana sonta bana ƙaunarta, daga ƙarshe kuma ya ƙarisa maganar da kuka yana faɗi Yaya kayafemi sake ƙanƙame Yaya Bala yai yana me faɗi kayafemi yaya, bazan iya ci gaba da zama da Rukky ba, Rukky ta cuceni tana amanata.wayyooo yayana,yayana na shiga uku.
   Cikin matsananci kuka ƙamaru ke magana. Gani haka yasa Yaya Bala rungumarsa haɗi da bubuga masa baya alamar rarrashi.
       Cikin kuka murya na karkarwa iya ke faɗi ni RABI me nake shirin gani haka?,wanan wacce irin masifa ce ta sauko min haka?,anya ƙamaru ba wani abu kasha ba?..
    Kai kawai ƙamaru ke jijigawa alamar a'a,kukane yaci ƙarfin sa yasa shi kasa magana.
   Gani tashin hankalin da mahaifiyarsu tashiga yasa Yaya Bala kama zauna ya zauna snn yasa hannu ya kamo iya zuwa ɗakinta,Iya na tafe tana faɗin me zangani ɗan gidan yaya wanan wacce irin masifa ce ta sauko min, innallilahi wa'inna'ilaihin raju'un subhanallilahi walhamdulillahi wala'ila'illahu'allahu akbar,gani ta shiga matsananci ruɗani yana Yaya Bala cewa baby komai iya,ki kwantar da hankalinki.
   Ina Rukky? Rukky fa ɗan gidan Yaya,idan mutuwa tai ka faɗimi kawai..A'a Rukky ba mutuwa tai ba..Tou Ina take?.
     Suna shiga ɗaki zaunar da ita yai yajima yana yimata masiha haɗi da batanan ƙarya, domin shima kansa besan abinda hakan ba,saida yaga iya ta numfasa snn yakoma ga ƙamaru,
Su sujima suna magana da Ƙamaru,duk yanda ƙamaru yaso yiwa Yaya Bala bayani amma yaƙi fahimta domin har yanzu be yarda Rukky ce zata aikata irin abinda ƙamaru ya faɗi masa ba.
    Sai dai tashin hankalinsa ɗaya daya riga ya furta kalmar saki,gashi ba ɗaya ba har uku.
   Dafe kansa yai yana innallilahi wa'inna'ilaihin raju'un,miƙewa yai zuwa ɗakinsa,koda ya shiga be waje kawai yasamu ya zauna,domin gaba ɗaya jikinsa yai sanyi.yana cikin wanan juyayin kenan saiga yaro yai sallama wai me napep yace a basa kuɗinsa.
    A lokacin ne ya tuna da cewa yabar me napep a waje, subhanallilahi yace"haɗi da miƙewa ciki yaje ya ɗauko kuɗi ya bawa yaron snn yace bayawa me napep ɗin hakuri.
  Tunda Rukky tasami bacci bata tashi ba sai bayan azahar,tana buɗe ido gani su Muhasana da Muhammad tai tsantsaye a gefen gadon da take kwance,gani ta buɗe ido ne yasa su ƙara matsawa kusa da ita haɗi da kiran sunanta, ummanmu! ummanmu snnu umma!!.Jin kiranta dasu Muhammed sukai ne yasa Khadijat juyowa suna haɗi ido tace da ita Yaya jiki?. Kai Rukky ta ɗaga alamar da sauki".


Yau dai hakuri zakuyi dani domin Short typing nayi,jima nayi log banga comment ɗinku ba sai ƙorafi da nayi tacin karo dashi,duk da haka banyi fushi ba snn kuma nagode sosai da ƙorafinku domin ta hakane zaisa inda nayi ba dai-dai ba na gyara.Snn ina ƙara baku hakuri akan abinda ke faruwa da Rukky insha Allahu komai zai dai-daita, snn kuma inaso kusan cewa babu yanda za'ayi kayi rayuwa ba tare Allah ya jarabce keba, musanman ma idan kakasance me kyankyawan hali dole sai kaci karo da jarabawa iri-iri a rayuwa amma idan kai hakuri sai kaga komai ya wuce, al'amarin Khadijat da Rukky kuma wanan kowa yasan yanda kishin sauri yake,inji hausawa suce harma tafi kishiyar da kuke zaman miji ɗaya kishi dakai,dan haka ku ɗauki al'amarin Khadijat a matsayin mynus domin domin aikine a gabanta tukuru wanda bezoba kuma be wuce ba, kunga kenan na Rukky duk me saukine.dan haka inda zamu gano ta kowa ta fisheshi...bari na barku haka sai gobe idan Allah yasa mukai rai da lafiya...😀😀###

MAKAUNIYAR RAYUWAWhere stories live. Discover now