MAKAUNIYAR RAYUWA

396 6 1
                                    

[9/24, 9:28 PM] Momcy: _*MAKAUNIYAR*_
                      _*RAYUWA*_
        
     

_NA:MMN USWAN_
_WATTPAD@HAUWASZARIA_

*_🌈KAINUWA WRITERS✍🏻 ASSOCIATION_*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*DAGA MARUBUCIYAR*

*ILLAR GOYO*
*ĎAN'UWA RABI JIKI*
*MATAR FARI*
*GARKUWATA*
*BAZATA*
*BATAN BASIRA*
*AURE IBADA NE*
*LABARIN RAYUWATA*
*TURURUWA*
*IN DA RAI*
*ZYNAH*
*MAHBOOB*
*BE KAI ZUCI BA*
*FITSARIN FAK'O*
*RIGAR K'AYA*
*MUSSADIQ*
*NAMIJI QANIN AJALI*
*LOADING....MAKAUNIYAR RAYUWA*

      _*BISMILLAHI~RAHMANI~RAHIM*_

*_________1* Tafiya take cikin sauri ga hadari yataso sai faman cida yakeyi, gani haka yasa Rukayya dake rike da bak'in leda a hannu cewa na shiga uku.

       Gani iska yataso gaďan-gadan yasa Rukayya fara sauri haďi da gudu, kamar wacce zata tashi sama, kafin takai gida ruwan sama ya6anlo.

       Gani haka yasata samu gefe ďaya tara6a tana jiran ďaukewar ruwa, ko kafin tak'atosa inda zata ra6e tuni kayan dake jikinta yajike sharaf,da haka tak'arisa gun tatsaya.
               Bata jima da tsayuwa ba wasu gun yacika da jama'a domin fakewar ruwa,anjima ana ruwan babu k'afk'aftawa.

     Rukayya dake tsaye jitakeyi kamar dada hali tatsaida ruwan sabida tasamu ta k'arisa gida gudan abinda zata taris a chan gidan.
 
      A 6angaren inna shatu kuwa tana kwance bisa gado ita da yar'lelenta wato Meenal kenan, himm kawai inna shatu tace"meenal dake kwance kusa da innarta tace"inna yayane?.

      Babu komai illa al'amarin yarinyar nan mana,"wa kenan inna?.
         Yawuci Rukayya!!.
            Rukayya kuma?!!.
                  Eh mana,"ni dama tun farko bansan abinda yasa kika ďaukota ba, ki dubafa sabida Allah duk irin ďawainiya da wahalan da kikeyi akanta ba'a gani, anan gidan daddy yayi maki waje suma suyi maki kuma duk akan Rukayya...

      Amina kenan, nima kaina babu yanda zanyine idan ban dauki Rukayya ba duniya zata zageni,sannan kuma idan nayi duba da zamucin dake tsakanina da yaya dan na ďauki Rukayya riko ba wani abu bane.

      Inna kenan, idan akai magana saikice yaya-yaya to yanzu ina yayan naki yake,keda kike wannan maganar wlhy inna nayi imani inda kece kika mutu ko kallonmu yayan naki bazaiyi ba bare ya ďaukemu..

       Amina kenan,to ai baka daka tamutum, nidai duk abinda zanyi zanyishine sabida Allah..

       Rukayya dake cha gani ruwan ya tsagaita yasa takamo hanyar zuwa gida,tana tafe tana rawar sanyi sabida kayan dake jikinta su jik'e sharrrkaf da ruwa.

     Jiki a sanyaye ta k'arisa  gida, da sallama tashiga. rukayya tai sallama har baki uku amma babu wanda ya'amsa daga inna har meenal ďin dake kwance.

     Shiruuu da Rukayya taji yasata k'arisawa daga cikin ďakin da suke kwanca, a bakin kofa tatsaya haďi da cewa nadawo inna..

    Kamar abin arziki inna tace"har kindawo?.
   Eh nadawo inna.
Inna tai maganar ne kamar abinda arziki."Rukayya dake tsaye batare data ankara ba kawai taji anhaďata da bango.
    Kafin tai wani yuk'uri tuni inna ta risketa agun ta hauta da duka kamar Allah ya aikota gareta.

     Tunda inna tafara dukan Rukayya bata bariba, kuka agun Rukayya kuwa tayishi har taji babu daďi."meenal na kwance sai faman juyi takeyi agado.

MAKAUNIYAR RAYUWAWhere stories live. Discover now