♥♥♥ RIGAR K'AYA ♥♥♥

2.8K 62 5
                                    

[7/25, 10:21 PM] Momcy: ♥♥♥
°°°°°°°
♥♥♥♥

_RIGAR K'AYA_

_(ďan'uwa)_

*_🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION_*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*🌹NA:MMN USWAN🌹*

_*DAGA MARUBUYAR*_

*1:ILLAR GOYO*
*2:ĎAN'UWA RABIN JIKI*
*3:MATAR FARI*
*4:GARKUWATA*
*5:AURE IBADA NE*
*6:BATAN BASIRA*
*7:BAZATA*
*8:LABARIN RAYUWATA*
*9:IN DA RAI*
*10:TURURUWA*
*11:MUSSADIQ*
*12:NAMIJI K'ANIN AJALI*
*13:MAHBOOB*
*14:BE KAI ZUCI BA*
*15:ZYNAH*
*16:FITSARIN FAK'O*
*17:LOADING...📲R'IGAR K'AYA*
_____________________________

*_TAURARIN CIKIN LITTAFIN_*

*_ALHJ MANTARI_*
*_ALHJ KARIMU LATE_*
*_HJY JIDDAH_*
*_ABDUL-SHAKUR (USWAP)_*
*_ABDUL-MAJID (MUS'AP)_*
*_KHADIJAT_*
*_ZAHRA_*

______________________________

بسم اللة الرحمن الرحيم


_page1_

••••••••••••"Bayan hukucin da alkali ya yanke na sake meda uswap gidan kaso har zuwa lokacin da za'a kammala bincike.

"Bayan ficewar alkali ne sannan police da ganroba duk suka mika, tare da sauran al'ummar dake zaune cikin kotun.

"Nan aka ďauki uswap zuwa mota,mugirat dake biye dashi tana kuka ga jijiri a hannunta wanda baifi kwanaki da haihuwa ba, Alhj Aminu dake biye da'ita shine yasa hannu ya rikota haďi da kiran sunarta" Mugirat.

"Matsananci kuka da takeyi ya hanata amsa kiran da alhj Aminu yai mata, sai ma k'ok'arin k'wace kanta takeyi daga hannunsa.

"Har sukai bakin mota Uswap ya juyo ya sake kallon mugirat haďi da kwaďa tama kira" Mugirat!! Mugirat!!, jin kiran uswap yasa mugirat waigowa ita kanta batasan lokacin data kwaďa wani irin ihuu ba sannan tai hurrrgin da baby dake hannunta a guje ta nufi wajan motar haďi da kiran sunar uswap.

"Alhj Aminu dake tsaye shine yai saurin cafko baby, sbd kaďan yarage ya faďi k'asa, ba alhj Aminu ba hatta jama'ar dake bakin kotun saida ihu mugirat ya razanasu." Tana isa bakin motar faďawa tai jikin uswap haďi da fashewa da wani irin matsanancin kuka"
"Shima rungumarta yai a kirjinsa haďi da rintsa idonsa duka biyu, cikin zuciyarsa kuwa ji yake tamkar kamawa zatai da wuta sbd zafi da k'una.

"Alhj Aminu dake gefe rike da baby shima kansa saida ya tosayawa yar tasa, yana mai lisafe-lisafen al'amarin mugirat tun daga tashinta har izuwa wannan lokacin.

"Sunkai minti biyar a haka sannan ganroban suka dakatar dasu da ya'isa haka, nan suka tura uswap cikin mota ita kuma suka barta tsaye a gun.

"Suna shiga sukaja motar zuwa prison, Mugirat dake tsaye sulalewa tai a gun ta zube k'asa tana mai danko k'asar dake gun haďi da ihu da kiran sunar uswap!!!uswap!!!uswap!!,amma ina sun riga ta suyi nisa.

"Da sauri alhj Aminu ya k'ariso inda take hannu ďaya yasa yana k'ok'arin ďagota tsaye amma ya kasa sabida ďayar hannunsa akwai baby,"wasu mata biyu dake gefe tsaye gani abinda ke faruwa yasa suka kariso gun sune suka taimaka masa suka tayasa ďaga mugirat zuwa mota.

"Driver yajasu suka tafi,tun a mota alhj yakeyi wa mugirat nasifa da tayi imani da Allah da k'uma k'addara,duk cikanken musulmi babu yanda za'ayi yace zaiyi rayuwa ba tare da Allah ya jarabcesa ba, dan haka nakeso kiyi hakuri sannan kuma ki yarda Allah ne mai kowa mai komai mai ikon yida hanawa, inaso ki ďauki wannan a matsayin k'addara kada ki kawo kowa cikin wannan al'amari Allah shi kaďai ya barwa kansa sani kuma shine zai warware mana bi'iszinillah...

MAKAUNIYAR RAYUWAWhere stories live. Discover now