Chapter fifty-one

Start from the beginning
                                    

"At last, yau ga ki ga ni"

Yayi maganar cikin kwanciyar hankali, da nishad'i, samira shashek'ar kuka ta fara,

"No no daina kuka, dan yau sweetheart dink'i abdulshakur baya nan balle ya rarrashe ki"

Yadda yayi maganar kasan abun nayi mishi mutuk'ar dad'i, samira kallan shi tayi da dalla mishi muguwar harara, k'azamin bakin shi ya daina kiran sunan shakur d'inta, ji tayi kamar ta tashi ta shak'e shi, wani tsnar shi take ji ta mamaye mata zuciya, k'arshen irin su ismail bazai tab'a yin kyau ba, shi da nabila sai Allah ya nuna musu tun kan subar duniya,

"Nasan kinsan yarda saurayin ki ya saka ni a gaba gaba d'aya ya b'ata mun kasuwanci na"

Wani irin kallo yake mata kuma a lokacin da yake mata maganar, kallan tsana, itama ta tabbata irin kallon take mishi,

"Ni da nake abokin shi shekara da shekaru ya zubar a shara saboda mace irin ki"

Ya nuna samira, ita kuwa ta kafa mishi ido wanda ke d'auke da tsan tsan tsana dan bata san mai zata ce mishi ba saboda gaba d'ayan ta a tsorace take,

"Da nabila ta gaya mun me zata miki naga shine babbar ramuwar da zan iya yi akan shi, a ganin ki, in har yaji labari anyi amfani dake kuma ba mutun d'aya ba ba biyu ba uku ba kafun a saka wuk'a a farke kayan cikin ki ya zaije"

Wani amai ne ya taho wa Samira, har ta fara yin shirin zubar da duk abunda ke cikinta a k'asan wurin, bayan zubar da hawayen da idanuwanta ke yi, tana ji ismail na sakin dariya, amma gaskiya ko a cikin marasa Imanin shi na k'arshe ne, bata tab'a had'uwa da mugun mutum irin shi ba a rayuwarta, gaba d'aya abokan abdulshakur nada mutunci da kamala shi kad'ai ne ya fita daban,

Ganin shi da tayi ya tashi ya fara yowa kanta ne ya saka ta fara motsi tana jan igiyar dake d'aure a bayan hanunta, so take kawai ta kwace, in har babu wanda zaizo cecanta Allah ya kawo mata mutuwar ta yanzu yanzun nan akan dai taga cin mutuncin da yake shirin yi mata, hawaye basu bar zuba a fuskar ta ba kuma bata daina jan igiyar ba, hannunta har ya fara yin jaa dukda bak'ar fatarta, ta jima kanta ciwo saboda igiyar akwai kwari, da taga ya doso dab da ita kawai ta kulle idanunta tana jiran taji k'azamin hannunshi a jikinta,

Amma sai jin jiniyar y'an sanda sukayi, sauri samira tayi ta bud'e idanunta, k'ara jin jiniyar tayi a kusa kusa kuma kamar da yawa, tana ganin ismail ya fara rikicewa yana waige waige, jin k'arar harbin bindiga sukayi, samira ta k'ara lumshe idanunta, ba kalar masifar da bata gani ba yau dai, tsabar bata cikin hayyacinta gaba ki d'aya bata yi tunani zuwa cecanta akai ba, ji tayi kamar ba kowa a wurin, tana bud'e idanunta ai kuwa ta nemi ismail ta rasa, yayi ta kanshi kenan,

Ji tayi an shigo wurin a guje, bata ga fuskar wane ba saboda akwai d'an duhu gashi kuma daga nesa, amma tunanin ta wani daga cikin y'an daban ne ya shigo, k'ara mak'alewa tayi jikin bango ta fara yin addu'a, tare  da sunkuyar da kanta da k'ara kulle idanunta, bata san taga ko wane bala'i dake shirin faruwa da ita, jin da tayi kamar an zube a k'asa kusa da ita ne ya saka ta fara bud'e idanunta a hankali,

Abdulshakur ta gani a gaban ta, abunda ya fara zuwa kanta shine ta fara gane gane ne, dan ko da wasa bata yi zatan shi bane, gaba d'aya ya canza ya koma kamar bashi ba, k'ara ji tayi an shigo wurin da sauri ta d'aga idanunta tayi shima bata ga fuskar shi ba sai da ya matso kusa, fuskar ya mu'azzam ce, sai a lokacin abun ya fara shigar mata kai, wani kuka ta saki da ta gane da gaske sune suka zo cecanta, kuka take yi sosai har mu'azzam yazo ya cire mata igiyar hannunta bata sani ba, yana cirewa ta tsinci kanta a cikin k'irjin abdulshakur, ya k'ank'ameta da mugun k'arfi yama manta da mu'azzam a wurin, tana ji bayan rigarta ya fara jek'ewa alamar kuka yake, wani irin dad'i ne ya kamata Allah yayi tana da sauran rai zata k'ara ganawa da masoyanta,

Godiya ta fara yima Allah da ya amshi addu'ar ta, kuka sosai ita da abudulshakur suke a wurin shi kuwa mu'azzam ya tsaya yana ta kallon su, amma kika k'ura mishi ido shima zaki ga hawaye na zuba a fuskar shi, sai da sukayi kuka mai isar su sannan suka saki juna, gaba d'aya abdulshakur ya fita daga hayyacin shi, har wani duhu yayi a yini d'aya, samira da take kallanshi taji sanshi ya k'ara shiga zuciyar ta tausayin shi ne ya sake kamata, Allah ne k'adai yasan halin da ya shiga da yaji an neme ta an rasa, kallon shi cikin kwayar idanun shi tayi da suka zama jaa, a hankali da bud'e bakinta ta furta abunda tafi komi san gaya mishi a yanzu,

"I'm sorry"

Tana gama fad'a taga kwallar hawaye ta zubo daga idanunshi, tausayin shi ne ya sake kamata, ta gode Allah da yasa ta sake ganin shi da idanunta, muryar da suka ji ce ta saka ta d'agowa daga kallan abdulshakur d'in da take, wanda shi kuwa a lokacin ya saka hannun ya share hawayen fuskarshi,

"Ina ji mun kama su gaba d'aya"

Kalan abdulshakur ahmad yayi, sannan yace mishi,

"Ya kamata kazo ka ga harda wa muka kama a cikin su"

Samira tasan sarai me haka yake nufi, ismail zaije ya gani, tasan in abdulshakur ya ganshi a wurin sai abun ya dake shi sosai, tana jin idanun shi a kanta, itama juyowa tayi ta kalle shi tare da yi mishi murmushi, dan tasan shine k'ad'ai abunda zai ta dashi daga wurin ta, a hankali ya mik'e ya bar wurin kana gani ba dan yaso ba, suna fita mu'azzam ya k'arasa ya kwance mata igiyar k'afar ta, tare da ruk'eta ya tayar da ita tsaye, kallan shi tayi shima tace mishi su mama fa, bai ce mata komi ba, bai bata amsa ba haka ya kamata har suka fita daga cikin kangon.


(Finally she is safe, and how do you like abudulshakur and samira's reunion 😂😍😍,

Please vote and share ❤️❤️

BA KYAU BA ✔️Where stories live. Discover now