Chapter forty-two

1.4K 164 9
                                    

Yana fita ta zube a k'asan d'akin kuka mai karfi ya sub'uce mata, kuka take yi sosai harda shashek'a, tasan irin wulaqancin da tayi mishi yanzu ko ita y'ar gwal ce yace ace ya fita harkarta, wani sabun kukan ta sake saka, shikenan da rasa shakur d'inta, in batayi wasa ba baza ta k'ara ganin shi ba, haka ta zauna zaman dirshan a k'asa ta cigaba da zuba kukanta har nurse ta turo k'ofa ta shigo bata sani ba,

Ko da ta shigo sai da ta tsaya turus a gaban samira, ta fara zuba sallati da taga tana ta kuka tana tambayar ta in wani wuri ne ke mata ciwo, amma samira sam, ko d'agowa bata yi ba balle ta bata amsa ba, haka ta hak'ura da tambayarta da taga bata da shirin bata amsa, itama ta tsuguna a k'asa kusa da ita ta shiga rarrashin ta da yake nurse din mai tausayi ce, ai kuwa duk rarrashin nan samira tak'i yin shiru, haka ta kamata ta maida ta kan gadon ta, tare da mata dressing ciwon ta, da kuma b'ullo sabon wuri da saka drip d'in, tana gama aikinta ta fice abinta, aka k'ara barin samira ita k'ad'ai da ta kasa daina kuka,

Tunawa tayi yadda ta dunk'a jin bugawar zuciyar shi a bayanta lokacin da ya k'ankameta a jikinshi, itama zuciyarta harbawa ta dunk'ayi a wannan lokacin shi yasa ma ta kasa mostsi balle ta ture shi daga jikinta, tsoro ne ya baibaye ta da ta tuna yadda jikinshi yayi zafi kamar garwashin wuta, ba kokonto zazzabi ne me zafi ya kama shi, wani sabon kukan ta sake saki da ta tuna duk sanadiyar ta, anya kuwa Allah zai barta muguwar azabar da take bashi,

Gabanta ne ya yi wata mummunar fad'uwa da ta tuna shi kad'ai yazo kuma shine zaiyi ruk'i, d'auko wayarta tayi da take kan table d'in kusa da ita, hannunta wani mahaukacin rawa yake, harta jikinta gaba d'aya rawa suke, hankalinta a tashe, takai kan number d'in abdulshakur, bata damu ba kwata kwata a lokacin bata tuna da nabila ba, shakur d'inta ne kawai a ranta so take taji lafiyar shi, ya isa gida lafiya, haka tayi unblocking number d'inshi tayi dialing, zuciyarta k'ara harbawa tayi kamar kirjinta zai tsage da taga ba a d'auka ba, haka ta k'ara dialing shima shiru, wani kukan ne ya sake zuwa mata, me yasa bata rik'e shi ba lokacin da zai tafi bayan tasan gaba d'aya baya cikin hankalin shi, ji take kamar wani abu zai same shi a hanya,
sauri tayi ta k'ara kiran layin shima ba'a dauka ba,

D'ora kanta tayi akan cinyoyinta ta ci gaba da kukanta me mugun abun tausayi, ba abunda take a ranta in ba addu'a ba, Allah ya kaishi gida lafiya ya kuma kare shi, tunda take a rayuwarta bata tab'a jin tsoro irin na yau ba, gaba d'ayanta ta kasa samun nutsuwa, tana ji zazzabinta ya dawo sabo gal bayan sarawar da kanta ke yi, amma bata damu ba dan gaba d'aya zuciyarta na wurin shi,

"Ni wallahi banga amfanin mai dani gida da ya mu'azzam yayi ba kuma ya k'ara dawo dani, wahala ce inaji bata ishe shi ba ko dan yaga nan kusa-, me kuma aka miki kike kuka?"

Safiya tayi tambayar wacce a lokacin ta shigo d'akin ko sallama batayi ba tsabar tana jin haushin abunda yayanta yayi mata na maida ta gida haka kawai bayan anan zata kwana da mara lafiyar kuma ya k'ara dawo da ita, matsowa tayi da sauri ta samu wuri ta zauna a kusa da yayartata, dukda kullum suna cikin fad'a kowa yasan suna mutuk'ar san junan su,

Ci gaba tayi da tambayar ta me ya faru da taga kukan da samiran take yi ba d'an k'aramin kuka bane, har tasa hankalinta ya fara tashi saboda tunda take a rayuwarta bata tab'a ganin yayartata a cikin wannan yanayin ba, samira da bata fad'a balle har wani ya b'ata mata rai ya saka ta a cikin k'unci, gaskiya duk abunda ya saka ta kuka ba d'an k'aramin abu bane, safiya tayi k'asa da muryarta ta k'ara tambayarta lafiya,

Samira bata d'ago kanta ba, ita kuwa safiya tunani ta fara, haka d'azu da abudulshakur yazo ta tsince tana kuka da share hawaye, kuma tasan yanzun nan ita dashi k'ad'ai aka k'ara bari a d'aki, gashi ta sake dawowa ta tarar tana kuka, zumbur tayi ta kalli yayartata da wani abu ya fad'o mata,

"Na shiga uku Ya Samira wani abu abdulshakur ashaka yayi miki, naga ku biyu aka bari a d'akin" tayi tambayar a rikice,

Samira kuwa da taji an ambaci sunan shi ba sai ta k'ara sakin wani sabon kukan ba, safiya abun bata tsoro yayi, ba abunda bata kawo cikin ranta ba, anya baza ta tashi taje ta tambayi nurse d'in ba in wani abu yayyarta ke b'oye mata, a ganinta zata san wani abu tunda tana isowa sukayi karo a kofa tana shirin fita daga d'akin, haka kuwa akai dan mik'ewa tayi tare da fad'in,

"Ni bari naje na tambayi nurse d'in in ma wani abu kike b'oye mun yanzun nan in kira mama in sanarda ita"

Yayartata sauri tayi ta d'ago tare da kamo hannunta, had'e da girgiza mata kai, safiya da taga kamar tana da shirin fara magana ta koma wurinta ta zauna, ta k'ara kafa mata ido alamun jiranta take, a lokacin samira taji tana so ta gaya ma wani damuwarta, tana so ta fad'a ko zata samu zuciyarta ta rage rad'ad'in da take mata, ko ta samu sukuni a cikin ranta, amma kuma da wani yasan tana san saurayin babbar k'awarta, wacce kowa ya San su tare gwamma ta had'iye komai ta bar komai a cikin ranta koda mutuwa zatai,

Haka ta share hawayen ta dan taga safiya da rigima ta dawo, in har aka samu matsala to da gaske sai ta kira mama ta gaya mata, koma ta tsani wannan jerin tambayoyin da zasu saka ta a gaba ita da gwaggo suyi mata, itama tayi kuskure da tabar safiya taga tana kuka,

"Zazzabina ya dawo mik'o mun magani nasha" muryarta na rawa tayi magana bayan k'ankame wayar ta da tayi a hannunta kamar abdulshakur d'in ne,

Safiya tashi tayi tai wurin da aka ajiye maganin, tasan yayartata baza ta tab'a gaya mata abunda ke damunta ba, addu'a ta shiga yi mata na Allah ya rage mata wannan zurfin cikin, kicibis tayi da abinci da fasashen plate a k'asa, da yake ta d'aya side d'in gadon ne shi ya sa bata lura ba ga tun da ta shigo hankalinta yayi wurin kukan da yayartata take, samira wacce tunda da safiyar ta tashi take kallonta tayi saurin cewa,

"Nice na zuba abinci ya kife daga hannun na, d'auko tsintsiya ki share" tana maganar ta kwanta, yanzu jikinta yayi mugun zafi,

Custard d'in fa?" Safiya ta tambaya tare da nuna custard d'in dake zaune akan table,

"Zubar dashi bazan sha ba" ta k'ara juya ma safiya baya.

Bayan ta had'iyi maganin da k'anwarta ta mik'o mata, ta k'ara kiran number d'in abdulshakur shiru ba'a d'auka ba, lumshe idanunta tayi hawaye masu zafi suka sake zubowa, in har wani abu ya same shi bata jin zata iya rayuwa, zata rasa farin cikin, zata zama fanko, ma'ana tana da rai amma bata da amfani,

Ji tayi anyi knocking k'ofa, tana ji safiya ta tashi ta bud'e,

"Wanda ya fita ne yace mu kawo kaya, ya d'an dad'e da yace mu kawo amma mun d'an tsaya yin wani abu ne sai yanzu muka samu dama"

Suna gama maganar son shi taji ya k'ara nin nin kuwa acikin zuciyarta, da tausayin shi wanda duk ya mamaye gab'obin jikinta, shakur d'inta mutumin kirki ne, bai cancanci irin wulaqancin da take mishi ba, ko kusa ma, hawaye ne suka sake jik'a fuskarta,

Tana ji safiya ta zauna zaman bud'ewa kayan bayan sun fita, tana bud'ewa tana sallati da santi, daman anan aka fi kwawri, samira banza tayi da ita ta k'ara kiran wayar shi ta saka a kunnan ta, ji tayi an d'auka, da wani mugun sauri ta mik'e daga kwanciyar da take, har sai da taji jiri, ta lumshe idanunta tana jiran a fara magana daga d'ayan b'angaran, muryar da taji ba muryar shi bace, ji tayi ta jik'e sharkaf da gumi bayan mahaukacin bugawar da zuciyarta keyi a k'irjinta har tana jiyo sautin ta, addu'a kawai tak'e yi a k'asan ranta tana jira taji mugun labari.

(Me kuwa ya samu abdulshakur ne??

Vote and share ❤️❤️)

BA KYAU BA ✔️Where stories live. Discover now